Ticker

6/recent/ticker-posts

Hada Kalmomi

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Haɗa Kalmomi

36. Ba ita ke baba, birni, buzaye,

 Bar bakalin biri yana bin ganyaye,

 Bobo ba ruwansa sabgar bokaye,

 Ba, bi, bo da bu, da be  kwai bebaye,

  Borin beguwa ƙaya taka harbowa.

37. Ɗauko ‘ca’ mu yo misalai kyawawa,

 Ca ita ke da caca, ciwo, cutarwa,

 Ce kaca, carafke, cacuma ga gocewa,

 Cinnaka, cida, kucaki, ciza da ƙucewa,

  Mai cin Cera ba ya burge Hausawa.

 

38. Dawa, dankali, akai dogo, dubbai,

 Dakali ya daɓe a dandali can Dabai,

 Dogon dogari ya sanya wando baibai,

 Dakaru dubu dukansu du ba kibbai,

  Ita ko, Dediya hatsi taka katsewa.

 

39. Fara mara fuka-fukin ba ta firka ba,

 Duba daɗin misalai idan ba ka gane ba,

 Fafe duma farat guda ba aiki ba,

 Fati fito ki kai fura zauren baba,

  Ka da ki bari a feƙe ƙwaryar damawa.

 

40. Gangara gangaren Bala geben Suru,

 Gagare ga shi yanzu ya gagari taru,

 Gabada, gada, gida, goro da guru,

 Ga gara, gira, gumi, ga kuma goru,

  Mai gemu ya zanka aiki na yabawa.

 

41. A misalai ‘h’ idan zan zanowa,

 Hauka, hankali ka magance taɓewa,

 Yanzu mu lura ga su jumla ka biyowa,

 Na ga Habu ga hira shi ke holewa,

  Hura wuta cikin dawa sai herewa.

 

42. Yanzu mu ɗauki ‘j’ mu jera misalinshi,

 Jaji Hajjo juyi, jeji duka sa shi,

 Ga wata jumla a zan kula zan gane shi,

 Jakin Jika jori na son huda shi,

  Juraha ɗan Baduku manyan jemewa.

43. “K(a)” na nan ga sautuka bari in jero,

 Kaki, koko, kuka, rakke sa koro,

 Ga jimla ƙasa misalan zan ƙaro,

 Kakaki kira yakai Allah koro,

  Kukuma amonta shi ke godewa.

 

44. “L(a)” sautin amonta tamkar dai lalo,

Lale marhaba da ‘yan wasan ƙwallo,

 Ga wata jimla cikinta “l(a) ta sha lilo,

 Liman Bawa shi ka limancin Lolo,

  Lura da lokaci ake iya lelawa.

 

45. Matar Manu na ga ta aiki su Kande-

 Mamman, Mode har da Mani sa Mande,

 Mai damun fura a nemo mata ludde,

 Matan Minjibir suna neman Mode,

Mai musu munduwa da buzun jemewa.

 

46.  A kalmomi ‘n’ takan fito in kun yarda,

 Nana, niƙa da naniya ga kuma hoda,

 Idan mun sa a jimla ‘n’ kan bayar da:

 Nana ka son ni’imta nono ya yi tsada,

Kwara ruwa gare shi nan muka ganewa.

 

47. Raggo bai da rangwame dutsen Dala,

 Rigar ragguwa da dauɗa ɗan kalla,

 Ra ke raraka a kalmomi kalla,

 Ragon Rigu ya yi rero madalla!

  Dussa ga ruwa ya sha ba renawa.

 

48. ‘S’ ma na zuwa a kalmomi jere,

 Sara, samfuri, sukar sa sassare,

 Sura, safiya, sigari ga sure,

 Sambo, Sirajo sun ka sha romon sure,

  Sososo ka shan miya bai suɗewa.

 

49.  Tattara kalma da ke da “t” malam jero,

 Teku tana da tambuwa ga kuma toro,

 Telan Tumba tambaɗaɗɗe mai tsoro,

 Tasar Titi an ka sa toshin Mairo,

  Ta turo akwati tebur na azawa.

 

50. Ga misalin w cikin kalamai an kawo,

 Waƙa, wuƙa, wuya, kuwwa, dawo,

 Wayon waiwaya yana can bisa gawo,

 Wawa mun ganai da wiwi bisa gawo,

  Ya wuce ƙa’ida a nan sai ɗaurewa.

 

51.  Yaro bai yini a ɗaki mai yoyo,

 In ko ka ganai ka san ba shi da wayo,

 Bai zarce a ɗau zani ai mai goyo,

 Wayo na ga yara manya wuce goyo

Gayu, wa ka bar su baya ga wayewa?

 

52. Zakari da Zoro yau wurin zikiri za su,

 Zazzage-zazzagen gaba babu irinsu,

 Zabure-zaburensu ya wuce sa’arsu,

 Zanka zumuɗi zuwa ga tasu ibadarsu,

  Zuci ka ambaton Ilahi da dacewa.

Post a Comment

0 Comments