Shin Wankan Tsarki Ta Wajaba Akan Yarinyar Da Akayi Zina Da Ita Bata Balaga Ba?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum. Lokacin da yarinya take ƙarama maza suka dinga biyan buƙatunsu da ita, to sai yanzu da ta girma shi ne ta gane abin da suka yi da ita haramun ne. To yanzu malam, wanka ya wajaba a kanta. Amma yau ya kai 4 years (shekaru huɗu) da tubanta, shi ne take tambaya: Ya dace ta yi wankan janaba, ko a’a?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

    Wankan janaba kamar sauran ayyukan ibada, yana zama wajibi ne a kan wanda ya balaga kaɗai. Amma ƙaramar yarinyar da aka yi amfani da ita, alhali ba ta kai lokacin balaga ba, ba dole ne sai ta yi wanka ba.

    Ko dayake wasu malaman sun nemi cewa ta yi wankan, kamar ƙaramin yaro shi ma idan aka yi amfani da shi. Amma dai a matsayin mustahabbi ne, ba a matsayin wajibi ba.

    Idan kuma a lokacin da aka yi amfani da ita yarinyar ta balaga, amma dai ba ta san hukuncin yin wankan ba ne sai yanzu, a nan wasu malaman sun ce dole yanzu sai ta tashi ta yi wankan janaba, sannan kuma ta ramo dukkan sallolin da ta yi tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu. Idan kuma ba ta iya gano adadin sallolin ba, sai ta yi ta ramawa har sai ta fahimci cewa ta gama biya!

    Wasu malaman kuma suna ganin wankan kawai za ta yi, amma ba sai ta ramo waɗannan sallolin ba, matuƙar dai a cikin rashin sani ne ta ƙi yin wankan, ba da gangar ba ne.

    Allaah Ta'aala ya ambaci addu'ar muminai cewa:

    رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَآ إِنْ نَسِينَآ أَوْ أَخْطَأْنَا

     Ya Ubangijinmu! Kar ka kama mu idan muka manta, ko idan muka yi kuskure.

    Sannan ya tabbata a cikin Sahih Muslim game da wannan addu'ar ta muminai cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Ubangiji Ta'aala ya ce:

    قَدْ فَعَلْتُ

    Na yarda.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.