Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Huda Hanci Da Saka Zobe Ko Sarka A Kafa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Warahmatallahi Malam don Allah yaya kwalliya da hudan hanci, gyaran gira, zoben kafa da sarkan kafa suke amusulunci? Nagode. Allah saka da alkhairi

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Malamai sunce hujin hanci da hujin kunne duk ya halatta ga Matayen musulmai. Domin kuwa matan Sahabban Manzon Allah sun kasance sunayi kuma Annabi bai hanasu ba.

Acikin FATHUL-BAREE juzu'i na 10 shafi na 407-408, Al-Imam Ibnu Hajrin ya kawo wani hadisi wanda Tabarany ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) Ya lissafta abubuwa bakwai sunnah ne ga duk wata 'ya-mace. Daga ciki akwai hudar hanci da hudar kunne.

Amma malamai sunce wajibi ne kowacce mace ta tabbatar da cewa ruwa yana ratsawa cikin wannan hujin yayin da tazo yin wankan haila ko janabah.

Dangane da sarkar Ƙafa da zoɓen Ƙafa kuwa, rashin sanyasu shi ne mafi alkhairi. Domin kuwa idan tana tafiya za'a iyajin Ƙararsu. Sannan kuma indai bata sanya safar Ƙafa ba, wasu mazajen da ba muharramanta ba zasu iya ganin wannan adon. Yin hakan kuwa haramun ne a Musulunci.

Allah ya umurci matan muminai cewar su ɓoye adonsu kuma kada surika buga kafafunsu yayin da suke tafiya.

(Suratun nuur).

وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا ۖ وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّ ۖ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آبَائِهِنَّ أَوْ آبَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ أَوْ أَبْنَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ أَوْ نِسَائِهِنَّ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ أَوِ التَّابِعِينَ غَيْرِ أُولِي الْإِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ أَوِ الطِّفْلِ الَّذِينَ لَمْ يَظْهَرُوا عَلَىٰ عَوْرَاتِ النِّسَاءِ ۖ وَلَا يَضْرِبْنَ بِأَرْجُلِهِنَّ لِيُعْلَمَ مَا يُخْفِينَ مِنْ زِينَتِهِنَّ ۚ وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ

Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko ´yan'uwansu, ko ɗiyan ´yan'uwansu mãtã, kõ mãtan ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyewa daga ƙawarsu. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo. (Suratun-Nur aya ta 31)

Shi kuwa gyaran gira ta hanyar ragewa gashin ko askewa, Wannan haram ne. Manzon Allah ya tsine ma duk matar da take tsigewa gashin girarta da kuma wacce take tsige mata ɗin. (aduba Sahihul Bukhary hadisi mai lamba 4886 da sahihu muslim hadisimai lamba 2125)

DON KARIN BAYANI:

@ aduba FATAWA AL-LAJNATUD DA'IMAH (juzu'i na 5 shafi na 195-197)

@ Da kuma FATAAWA ULAMA'I BALADIL HARAM shafi na 577.

@ ALFATAWAL HINDIYYA juzu'i na 5 shafi na 357.

@ RADDUL-MUHTAR juzu'i na 6 shafi na 420.

@ MARAƘEEL FALAHI shafi na 102.

@ BAHRUR-RAA'IƘ juzu'i na 1 shafi na 47

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments