Menene Hukuncin Wanda Baya Wankan Janaba?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    An ruwaito narkon azaba mai girma ga wanda baya wankan janaba kamar yadda Allah ya nemi musulmi suyi aduk lokacin da janaba ta same su, yazo acikin mu'ujamul dabarani al'ausad, daka Anas Yardar Allah taƙara tabbata a gareshi ya ce: Manzan Allah salallahu Alaihi wasallam ya ce: (Abubuwa uku duk wanda ya kiyayesu toshi waliyyin Allah ne ma'ana masoyin Allah ne, duk wanda ya tozartasu toshi makiyin Allah ne nagaske, Sallah, da azumi, dakuma janaba).

    Azzarƙani acikin sharhin muwadda ya ce:[ Abunda ake nufi da kasancewar wanda ya tauyesu makiyin Allah ne, shi ne Allah zai masa sakamako akai, zai tabar dashi ya wulakan tashi, ya kaskantashi, idan afuwar Allah bata riske shiba yatuba, idan ya tozarta tasu yana mai kore wajab cinsu, to shi kafirine, sai kiyayyar takasance ababinta.

    Wanda baya wankan janaba tahanyar mafarki ko zina ko jima'i da matarsa, idan yana hakanne yana mai inkarin wajabcin wankan to ya kafirta, shaikul islam ibnu taimiyya yace acikin lttafinsa jawabi ingantacce ga wanda yacanza addinin Annabi isah.

    Lallai munsani acikin musulunci salloli biyar wajibine akan kowanne musulmi, haka tsarki daka hadasi da kuma janaba shima wajibine, mutum ba zaiyi sallah ba sai dasu tare da iko, ba zaiyi taimama ba idan yana da iko, duk wanda yayi inkarin wannan kafirine a ittifaƙin musulmi.

    Malam shankiki ya ce: acikin littafinsa AZWA'UL BAYAN Malamai sun haɗu akan cewa wanda yabar sallah yana mai kore wajabcinta kafirine, kuma za'a kasheshi amatsayin kafiri matukar bai tuba ba, abune afili barin bunda sallah bata yiwuwa saida shi kamar barin sallar ne, haka kore wajabcinsa kamar kore tane, Amma idan yabar wankan janaba bai kore wajabcinsa ba, kuma bai jahilci hakan ba, toshi mai Saɓo ne kuma ya cancanci ukuba, malamai sunyi saɓani akan kafircinsa, antambayi shaikul islam ibnu taimiyyah Rahimahullah kamar yanda yazo amajmu'ul fatawa, shin wankan janaba wajibine ko bawajibi bane? shin kuma yahalatta sallah da janaba batare da ansake ba,?

    Sai ya amsa dacewa: ( wankan janaba wajibine bai halatta ga wani yayi sallah yana da janaba ko hadasi ba har sai yayi tsarki, duk wanda yai sallah batare da tsarki ba ashari'a yana mai halatta hakan to ya zama kafiri, wanda kuma bai halatta hakan ba anyi saɓani akan kafircinsa, zai fuskanci hukunci mai tsanani, saidai in zai iya wanka da ruwa zaiyi wankan, inkuma bazai iya amfani da ruwa ba yana tsoran cutuwa inyai amfani daruwan saboda wata cuta dayake da ita ko tsoran sanyi sai yayi taimama yayi sallah ba ramuwa akansa, amafi bayyanar zantukan malamai.

    Wallahu ta'ala a'ala wa'alam

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.