𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum, Dan Allah tambya nake, Ina son
yin ramuwar azumin ramadan to ban daura niyya ba se bayan alfijr, Yaya matsayin
azumina, Kamar dai ance ba Azumi koh, Toh ina tantama ne idan kuma babu shin
zan iya maida shi azumin bakance da nayi Alkawari ?Allah y saka da alheri.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Yin niyya cikin dare game da azumi na farilla, a
bisa mahangar malamai mafi inganci, game da azumin ko kuma na ramuwa ne wannan shi
ne ra'ayin mafi yawan malamai....
Ibn Ƙudamah
mai littafin al-Mughni ya ce: Idan ya kasance azumin farilla ne, kamar azumin
Ramadan akan lokaci ko kuma na ramuwa ne wanda mutum zai rama shi daga baya, ko
azumin cika bakance, ko azumin kaffara, to an shardanta ma mutum ya yi niyya
tun daga daren da ya gabata, kamar yadda limaminmu, da Malik da ash-Shafi'i
suka fada.
Imam Abu Hanifah ya ce: An yarda gameda mai yin
azumin ramadana da duk wani azumi wanda wani dalili ne ya ke samar dashi na
musamman ya samar da niyya tun daga ranar.
(littafin
Al-mugni 3/109)
Dalilin da yasa suka ce wajibi ne mutum ya yi
niyya tun daga daren da ya gabata, shi ne hadisin da ya tabbata daga Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Duk wanda bai yi niyyar yin azumin gabanin
alfijir ba, to azuminsa ba ya cikin lissafi (bashi da wannan azumin).” Tirmiziy
(730) ya ruwaito kuma Albaani ya sanya shi a matsayin hadisi sahih a cikin
Sahih at-Tirmidhi.
Imamut Tirmizi ya ce, bayan ya kawo wannan hadisi:
Abin da ake nufi da hakan, a wajen malamai, shi ne, babu azumi ga wanda bai yi
niyyar yin azumi ba kafin fitowar alfijir, ko a cikin Ramadan ne ko kuma
lokacin da ya zo rama azumin ramadana ko lokacin da zai rama azumin bakance.
Idan bai yi niyya daga daren da ya gabata ba, to bashi da azumi.
Amma azumin nafila, ya halatta a gare shi ya yi
niyya bayan ya tashi (da safe). Wannan shi
ne ra'ayin ash-Shafi’i, Ahmad da Is-haaƙ.
Allah ne mafi sani.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.