𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malam Wai yaron da aka same shi
ba ta hanyar auren Sunnah ba zai iya gadon iyayensa ko ba zai iya ba a
musulunce?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Al-Imaam At-Tirmiziy da Al-Imaam Ibn Maajah sun
riwaito daga hadisin Amr Bn Shu’aib, daga babansa, daga kakansa cewa: Manzon
Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« أَيُّمَا رَجُلٍ عَاهَرَ بِحُرَّةٍ أَوْ أَمَةٍ فَالْوَلَدُ وَلَدُ زِنَا لاَ يَرِثُ وَلاَ يُورَثُ »
Duk mutumin da ya yi zina da wata ’ya ko baiwa, to
ɗan ɗan zina ne: Ba ya gado kuma ba a gadon sa.
(Sahih Ibn Maajah: 2217)
Al-Imaam At-Tirmiziy ya ce:
وَالْعَمَلُ عَلَى هَذَا عِنْدَ أَهْلِ الْعِلْمِ أَنَّ وَلَدَ الزِّنَا لاَ يَرِثُ مِنْ أَبِيهِ.
Kuma malamai a kan wannan hadisin ne suke aiki
cewa: Ɗan zina ba ya yin gado daga mahaifinsa.
Sannan kuma malamai sun yi ijma’i a kan cewa: Ɗan da
iyayensa suka yi li’aani a
kansa ko suka same shi ta hanyar zina ba ya gadon wanda ya yi cikinsa, haka ma
danginsa. Shi ma kuma ba zai gaje su ba. Mahaifiyarsa ce kawai ta ke gadon irin
wannan ɗan na
zina ko na li’aani, haka ma danginta. Shi ma kuma yana dagon su. (At-Ta’aleeƙaatur Radiyyah: 3/420).
Amma idan wanda ya yi cikin ya yarda cewa zai riƙe shi
a matsayin ɗansa
da ya samu ta hanyar zina, a nan wasu malamai suna ganin wannan ya mayar da shi
kamar ɗansa
na halal, kuma zai iya gadonsa! Musamman dayake ba shi ɗan ne ya zama sanadin zuwansa duniya ta
wannan mummunar hanyar ba. Laifin iyayensa ne.
Sai dai kuma yarda da wannan maganar tana ɗauke da waɗansu matsalolin da suke buƙatar a
warware su, kamar haka:
1. Shin ɗaukar wannan matsayin bai ci karo da wannan
hadisin sahihi ba, da kuma maganganun malamai kamar yadda ya gabata a sama ba?
2. Da menene za a iya bambanta wannan ɗan na zina da wanda iyayensa suka same shi
ta hanyar sahihin auren Sunnah kenan?
3. Kuma wannan bai zama kamar taimakawa ne a
fakaice ga cigaba da samar da ’ya’ya ta wannan hanyar da ta saɓa wa Shari’a ba?
4. In kuwa ya zama haka, to da menene za a iya
bambanta wannan da hanyar samun ’ya’ya ta auren mutu’a da ’yan shi’a suke yi?
5. Idan kuma mutane suka yarda da samun haihuwa ta
wannan hanyar abin ba zai kai ga lalacewar gidajen aure ba kenan, kamar yadda
abin yake faruwa a ƙasashen Turai da Amirka?
6. Sannan ko mutane za ta iya jure wa masifu da
bala’o’in da hakan zai iya janyowa musamman a cikin wannan halin na ƙuncin
rayuwa da ake ciki a yau?
7. Amincewa da wannan ɗan a cikin gida da ɗaukarsa daidai da sauran ’ya’yan Sunnah,
wannan ba zai kai ga cutar da haƙƙoƙin sauran ’ya’yan
ba, kamar a wurin rabon gado?
Don haka abin da ya fi daidai daga waɗannan bayanan, gara a nisanci bai wa irin
wannan ɗan na
zina matsayi irin na ɗan
Sunnah, har a lokacin da wanda ya yi cikinsa ya amince da shi a matsayin ɗansa. Allaah ya kyauta.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.