Ticker

6/recent/ticker-posts

Saurayina Wai Ba Zai Aureni Ba Sai Yayi Zina Dani, Ya Tabbatar Ni Virgin Ce.

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamu alaikum Don Allah ataimakamin da Amsan Tambayan nan Kawatace Tana turkey takeson Amsan Wai wanda xata aura ne Angama maganan aure Wai shi sai Yayi kwanciyar aure da ita Sannan Xai aure ta malam menene hukuncin wannan auren Nasu kuma ta Yaya xata iya gamsar dashi ciwa Allah Ya Hana tacikin sauki daxai fahimce ta Wai shi Baxai iya auren Macen Da ba virgin bace Don Allah Malam abata Amsan tambayan.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

wa'alaikum salam. To ai Allah ne ya hana yin zina, danhaka Allah ne yafi kamata tayi ma biyayya fiye da mijin da zata Aura, in tana tunanin Mijin yanada abinda ze iya bata in ta Aureshi to shikuma Allah yanada abinda yafi na Mijin in tayimishi biyayya ze bata, danhaka yazama dole ta ƙi yarda da saɓon da wannan Mijin yakeso ya sakata aciki dan tayi ma Allah biyayya.

Zina tana daga cikin manyan laifuka da Allah() ya haramta akan dukkan musulmi namiji ko mace, Kamar yadda Allah() yake cewa a Suratul isra'i Aya 32

وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا

FASSARA:

Allah() ya ce: kada ku kusanci zina, domin ita alfahashace dakuma mummunar hanya

Saboda Mugun laifin dake cikin zina, shi yasa Allah ya tanadar da hukuncin Jefewa ga Mazinaci ko Mazinaciya in dai sun taɓa yin aure. Idan kuma Samari ne ko 'yan mata ana yi musu bulala ɗari-ɗari ne mutukar dai laifin ya tabbata akansu.

Danhaka in yace baze Auri Mace wacce ba virgin bace to yabari in an Ɗaura Auran sannan yaji ba virgin bace se ya sa awarware Auran abashi kuɗinshi wannan haka yake ashari'an Muslinci.

Amma yanzu inyace ze yi Zina da ita kuma ita tayarda to ya sakata acinkin Manyan Halaka guda 5:

1. Yayi disvirgin ɗinta, in yazo ya fasa yin Auren kuma ya riga ya hanata Auran wani wanda yakeso ya Auri virgin kenan.

2. In tabari yayi amfani da ita tariga tashiga fushin Allah, domin ta nuna tafi jin tsoranshi akan tsoron Allah danhaka se Allah ya ƙyaleta dashi yaƙi temakonta akanshi.

3. Shikanshi baze dinga ƙosawa ya Aureta ba tunda yariga ya ɗanɗani zaƙinta.

4. Shi kanshi baze dinga yarda da itaba ko bayan Auren tunda yasan zata iya yin zina da namiji dan ta samu wani abu wanda takeso na Rayuwa.

5. Za'a iya zuwa asamu yaro sakamakon wannan Zinan.

Danhaka taja hankalinshi ta hanya me sauƙi ya fahimta, Musamman gurin nunamishi wannan saɓon Allah ne kuma ko wace irin Musifa tana iya faruwa in an Saɓama Allah kaman yanda yake ganin in an Saɓa mishi zeyi wani abu na sharri. Kuma sannan ba wani abu bane yana iya kai ƙara abashi kuɗinshi Araba Auren akotu in yaji ke ba virgin ba ce.

Kuma in yaƙi yarda kisancewa ko ya rabu dake to sa'a kikaci domin ya nuna shi ba me tsoron Allah bane se ki gode ma Allah da yarabaki da mara tsoron Allah domin ko ya Aureki baze tsaremiki Haƙƙinki yanda ya kamataba.

Allah ta'ala ya tsare mana imaninmu

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments