Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sanya Jigida (Waist Beads)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

 Assalamu Alaikum, mallam tambayata shi ne Ya halasta mace ta sanya jigida?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

 Waalaikumus Salm Wa Rahmatullahi Wabarakatuh.

Ya halasta mace tayi Ado da jigida, don kuwa baya cikin IBADAT, kenan yana cikin Dangin MUBAHAT, sai dai idan sanya Jigidar ya zamo Al'ada ce ta wasu Ɓata-Gari kamar CUITIS, anan baya Halasta, don karta jawowa kanta Mumunan Zargi da Shaida.

Asali Gameda Jigida Sanyashi Halal ne  amma Tunda yana Cikin Kayan Kwalliya toh Haramun ne Mace Ta Bayyanashi ga Wanda Ba Muharraminta ba. Sannan Kuma Idan Yazamana Mutanen Banza ne sukayi fice wajan Sanya Jigidar toh anan Lallai yakamata Mutanen Kirki su nisanceta koda kuwa a Tsakanin sune su Mata be kamata suna ganinta da wani abunda yariga yazama Alamar Mutanen Banza ba. Amma Kuma akwai Wasu Nau'ukan Jigida na tsafi kamar Wacce za'ace Jigida ce amma kuma tana Maganin Farin Jini ko kuma tana sawa Miji ya ƙara Son Mace ko wani abu dai wanda ya Danganci Magani toh duk waɗannan Iri Irinsu Haramun ne kuma suna iya kai Mutum zuwaga Kafirci da Shirka, dan haka Haramun ne yin Amfani dashi koda kuwa da Kyakkyawar Manufa ce zakiyi, Toh Haramun ne a Nisanci irin Wannan domin tana cikin irin Abunda ake cema Attiwalah wanda Annabi yace Ruƙa da Laya da Tiwala Shirka ne. Dan Haka wannan irin Jigidar wacce kuke cewa Me Magani wannan Babu Shakka Haramun ne kuma Zasu iya Taɓa Tauhidin Mutum.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments