Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yiwa Kirista Kitso

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam don Allah ina da tambayoyi, Allah ya ba da ikon a amsa min, amin. Ina sana'ar kitso, kuma har kiristoci ina yi musu. Sukan zauna ni kuma ina tsaye. Shin akwai laifi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Sana'ar Kitso ɗaya ce daga cikin sanannun sana'o'in hannu na mata, tun tuni. Kuma ba mu san wani dalili a Shari'ar Musulunci da ya hana musulma ƙulla irin wannan sana'ar da mace kirista ba, matuƙar dai an kiyaye waɗansu ƙa'idoji, kamar haka:

1. Kiristar ta zama ba ta daga cikin maƙiya kuma mayaƙa ga Musulmi, saboda Allaah Ta'aala ya ce:

 لَا يَنْهَاكُمُ اللَّهُ عَنِ الَّذِينَ لَمْ يُقَاتِلُوكُمْ فِي الدِّينِ وَلَمْ يُخْرِجُوكُمْ مِنْ دِيَارِكُمْ أَنْ تَبَرُّوهُمْ وَتُقْسِطُوا إِلَيْهِمْ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُقْسِطِينَ

 Allaah ba ya hana ku daga waɗannan (kafiran) da ba su yaƙe ku a cikin addini ba, kuma ba su fitar da ku daga garuruwanku ba, ga ku yi musu alheri kuma ku yi adalci gare su. Haƙiƙa Allaah yana son masu adalci.

Sai kuma ya ce:

 إِنَّمَا يَنْهَاكُمُ اللَّهُ عَنِ الَّذِينَ قَاتَلُوكُمْ فِي الدِّينِ وَأَخْرَجُوكُمْ مِنْ دِيَارِكُمْ وَظَاهَرُوا عَلَى إِخْرَاجِكُمْ أَنْ تَوَلَّوْهُمْ وَمَنْ يَتَوَلَّهُمْ فَأُولَئِكَ هُمُ الظَّالِمُون

 Allaah yana hana ku ne kawai daga waɗannan (kafiran) da suka yaƙe ku a cikin addini, kuma suka fitar da ku daga garuruwanku, ko kuma suka taimaka a kan fitar da ku, ga ku jiɓince su. Kuma duk wanda ya jiɓince su to waɗannan su ne cikakun azzalumai.

Watau nau'ukan kafirai na farko ne kawai Allaah ya yarda, kuma bai hana mu yin duk wata mu'amala ta taimakon juna da sadar da alheri a tsakanin mu da su ba.

2. Lallai kitson da za a yi mata ya zama bai saɓa da koyarwa ko karantarwar addinin musulunci ba. Kamar abin da ya shafi ƙarin gashi (attachment) da sauransu. Tun da ya tabbata a cikin hadisin Ibn Mas'ud (Radiyal Laahu Anhu) wanda Al-Bukhaariy da Muslim suka fitar da shi cewa:

 لَعَنَ رَسُولَ اللهِ الْوَاصِلَاتِ وَالْمُسْتَوْصِلَاتِ

 Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya la'anci mata masu aikin yin ‘attachment’, da waɗanda suke kai kansu domin a yi musu.

 

3. Kuma lallai ya zama a inda musulmar take yin kitson ba a ɗauki wannan sana'ar a matsayin ta wulaƙanci ba. Domin bai halatta Musulmi ya wulaƙanta kansa a gaban wanda ba Musulmi ba.

Wannan shi ne fahimtarmu ga wannan tambayar.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐓��𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments