Wakar Kudi Ta Nasiru G. Ahmad

    1. Rabbi ban iko na tsara,

        Baituka kar nai gazawa.


    2. Yau batu zan kan "NuÆ™udu" 

        Ko ko "Money" ba sakewa.


     3.Mallakar su tana da daÉ—i,

        Duniya ba mai musawa.


    4. Laƙani na farin jini ne,

        Ba Æ™iyayya sai biyewa.


      5.Maganin huce takaici,

         Duniyar ga kana sakewa.


    6. Duk batunka abin yabo ne,

        Aibukanka suna É“acewa.


    7. Kai da Sarki har su Gwamna,

        Sai abota ba rabewa.


    8. Dukka faÉ—in duniyar nan,

        Za ka je lale anai wa.


    9. Dukka yare za ka ji shI,

        Don ko Naira ta iyawa.


    10. A gida ba babba sai kai,

          Duk batunka ba a Æ™iyawa.


    11. 'Yan uwa su taho gare ka,

           Lamarinka suna yabawa.


    12. Fa'idojin ba su ƙirgo,

          In da "Money" ka hayewa!


    13. Aibuka zan bayyana su,

           Don dukanmu mu zam kulawa.


    14. Kar ka manta akwai hisabi,

           Kan abin da ka mallakawa.


    15. Shin ta yaya kab biÉ—e su?

          Haka yadda ka zan kashewa.


    16. In ka tara sai ka koma,

           Fargabar su zamo É“acewa,


    17. Ga É“arayi na fakon ka,

           Ko ina ka yi ba sakewa.


      18. Hankalinka yana gare su,

            Ko da yaushe kana tunawa.


    19. "Ga kuÉ—ina can ga wane,

           Gobe haja za ta zowa."


    20. To ina nutsuwar ibada,

           Gun Tabaraka mai iyawa?


    21. Ƙoƙarin tsare dukiya na,

          Sa ralala ai biyewa.


    22. Sai ka ga an kai ga tsafi,

          Sihiri an rungumewa.


    23. Har a kai shirka da Allah,

          Dukiya don ai tsarewa.


    24. Son da kowa ke gare ka,

           Ka sani Æ™arya sukewa.


    25. Don a samu abin riƙa ne,

          In fa babu suna bajewa.


    26. In ka so ka farar dabara,

           Hidimar dini ka yowa.


    27. In halal ce dukiyarka,

          Rabbi zai karÉ“a yabawa.


    28. Ba a ba Allah haramun,

          "ÆŠayyibun" yake bai riÆ™awa. 


    29. Don haka mu biÉ—i halali,

          Don haram ba ta daÉ—ewa.


    30. Dukiya ta halali za ai

          Wa hisabi ran tsayawa.


     31. In haram ce sai uÆ™uba,

           Ga Jahannama ke direwa.


     32. ÆŠan uwa gode wa Allah,

           Lafiya da yake ta baiwa.


     33. Sana’arka riÆ™e da kyawu,

           Æ˜wadagonka zamo kulawa.


     34. Kar ka raina abin riÆ™awa,

           Na halal shi ke daÉ—ewa.


    35. Zam ƙana'a kar ka damu,

           In asiri yai rufewa.


    36. Nemi albarkar Ilahu,

          Godiya ka yi zai daÉ—awa.


    37. Ko da yaushe mu roƙi Allah,

           Mu yi kyan Æ™arshe gamawa.


    38. ‘Yan uwa da ka jarrabe su,

          Dukiyarsu ta yi yalwa.


    39. Rabbi sa su bisa tafarki,

          MustaÆ™im ba kangarewa.


    40. Ba su ikon taimakawa,

          Da halal mai tsarkakewa.


    41. Mu talakkawa ka ba mu,

          Hakuri da kaÉ—an mu yowa.


    42. Zan tsaya haka ‘yan uwana,

          Baitukan nai kammalawa.


    43. Nasiru G. Ahmadu ne,

          Ya yi waÆ™ar don tunarwa.


     Alhamdu lillahi.

          28 / 4 / 2014

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.