Mijina Baya Kyautatawa Mahaifiyarsa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As salamu Alaikum Malam, tambayata ita ce: Mijina ne yana da kuɗi daidai gwargwado kuma yana yi min hidima ni da ’ya’yana sosai. Kuma shi ke ɗaukan hidimar gidansu, ciyarwa da sutura komai da komai. A inda matsalar ta ke shi ne mahaifiyarsa, in ta tambaye shi wani abu ba ya yi mata. Kuma a gaskiya ba ta jin daɗi da shi sosai yadda ya kamata. Ita mace ce mai son ɗanta ya yi mata hidima, tana son in za ta unguwa ya ɗauki kuɗin mota ya ba ta, tun da yana da hali. To, malam don Allah ina son a taimaka min da nasihar da zan yi ma sa, domin abin yana damuna. Kuma yana min hidima fiye da ƙima, amma ga mahaifiyarsa tana kuka da shi.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

    Hanyoyi biyu ake bi don warware irin wannan mas'alar, in Shã Allãh:

    1. RAZANARWA: Watau a janyo ayoyi da hadisai sahihai waɗanda a cikinsu, akwai gargaɗi da jan-kunne ga mai aikata irin wannan aikin:

    2. KWAƊAITARWA; watau a janyo ayoyi da hadisai sahihai masu kwaɗaitarwa ko zaburarwa ga aikata irin abin da ba ya yi. Kamar ayar Suratul Isra'i: 23-24

    وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِنْدَكَ الْكِبَرَ أَحَدُهُمَا أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُلْ لَهُمَا أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُلْ لَهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا (23) وَاخْفِضْ لَهُمَا جَنَاحَ الذُّلِّ مِنَ الرَّحْمَةِ وَقُلْ رَبِّ ارْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرًا (24)

    'Kuma Ubangijinka ya hukunta cewa kar ku yi bauta sai dai gare shi kaɗai, kuma iyaye guda biyu ku kyautata musu matuƙar kyatatawa. Idan kuma har ɗayansu ko dukkansu ya tsufa a tare da kai, kar ka ce masa uf! Kuma kar ka raina su, amma dai ka faɗa musu magana ta mutuntawa da girmamawa.

    Kuma ka saukar musu da fika-fikan ƙasƙanci na rahama, kuma ka ce: Ya Ubangijina! Ka yi musu Rahama, kamar yadda suka rene ni tun ina ƙarami.

    Wannan ayar ta nuna:

    1. Haƙƙin iyaye yana da girma, domin daga haƙƙin Allaah sai shi.

    2. Yana daga cikin haƙƙin iyaye a kai matuƙa wurin kyautata musu.

    3. Yana daga cikin kyautatawa gare su a yi musu duk abin da suke so, matuƙar dai bai kauce wa dokokin Allaah Ta'aala ba.

    4. Ayar ta nuna yana daga cikin haƙƙin iyaye a kula da irin kalmomin da za a faɗa musu:

    5. Kalmar 'uf' ta nuna kar a gaya musu duk wata maganar da take iya nuna raini, ko an ƙosa, ko an gaji da su, kamar a ce: Kash! Ko tir! Ko: A'a! Ko: Haba! da sauransu.

    6. Haka kuma kar a raina su ko a wulaƙanta su, ko a daka musu tsawa a razana su! Amma dai a faɗa musu magana ta mutuntawa da girmamawa.

    7. Duk yadda al'amura suka kai da tsanani, kar a yarda su shiga cikin ƙunci da damuwa, amma a riƙa nuna musu tausayi da rahama.

    Ko shakka babu, duk mahaifiyar da ta san ana fifita matar auren ɗanta a kanta ba za ta ji daɗi ba, kuma a ƙarƙashin haka, ba a kyautata mata yadda ya kamata ba.

    Haka dai za a bi ayoyi da hadisai masu yawa ana fitar da irin waɗannan darussa da fa'idoji, sannan a yi masa bayaninsu cikin hikima da wa'azi kyakkyawa, tare da addu'ar nema masa shiriyar Allaah Ta'aala da kuma samun tsira daga kamun shaiɗan.

    Allaah ya shiryar da mu gaba-ɗaya

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

     Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.