Ticker

6/recent/ticker-posts

Abubuwan Da Suke Warware Musulinci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam Wadanne Abubuwa ne Suke Fitar da mutum Daga Musulinci Idan ya aikata su?

𝐀𝐌SA❗️

الحمد لله الذي رضيت لنا الإسلام دينا، ولا يقبل دينا سواه يوم القيامة.

Abubuwanda suke fitarwa daka musulunci sunada yawa zamu kawo kaɗan daka cikinsu

Sheikh Abdul'aziz  bin Bazz Allah ya yi masa rahama ya ce:" Ka sani ya kai Muslim, lallai Allah ya wajabtawa baki ɗayab bayi  shiga  musulunci  da riko da shi da tsawatarwa  daga  abin da yake saɓa masa, Allah ya aiko Annabinsa Muhammad Sallallahu Alaihi wasallam domin ya yi kira (Da'awa) akan hakan, Allah madaukakin sarki ya bada labari cewa Wanda duk ya bishi (ya tsira yashiryu) wanda kuma ya juya masa baya daga barinsa hakika ya ɓata.

 Allah ya tsawatar a cikin ayoyi  da dama game da dalilanda sukesa Ridda ( barin addini), da sauran nau'o'i  shirka da kafirci malamai Allah ya yi masu rahama sun ambata acikin babin hukuncin Wanda ya yi Ridda cewa: lallai musulmi yana iya barin addininsa  ta hanyoyi da dama daga cikin abubuwan da ke war-ware  musulunci  wadanda kuma suke halatta jininsa da dukiyarsa, ya zamto ya fita daga musulunci  da su, Yana daga cikin  mafi hadarinsu kuma mafi yawansu  Musulmi ya fada cikin nau'o'in abubuwa  goma  dake war-ware musulunci Wanda sheikh Muhammad bin Abdulwahab da wasunsa daga ma'abota ilimi Allah ya yi masu rahama baki-daya suka fada, zamu kawo  maka su ataƙaice, domin kagujesu katsawatar da waninka su,  domin kwadayin kubuta da zaman lafiya  tare da bayanan da zamu ambata  abayansu.     

1. SHIRKA (hada Allah da wani cikin bauta) cikin bautar  Allah maɗaukakin sarki, Allah madaukakin sarki ya ce:

إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ ۚ وَمَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا

Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ɓace, ɓata mai nĩsa. (Suratul Nisa'i 116)

 Allah maɗaukakin sarki ya ce:

... ۖ إِنَّهُ مَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ ۖ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنْصَارٍ

Lallai wanda duk ya yi shirka  da Allah hakika Allah ya haramta masa aljanna kuma wuta ce makomarsa, Azzalumai (mushirikai) ba su da mai taimakonsu. (Suratul Má'idah 72).

Yana daga cikin shirka rokon matattu ,da neman agaji awajansu da yin alwashi da yanka dansu. Kamar wanda zai yi yanka don wani aljani ko kabari.

2. Wanda ya sanya wani shamaki tsakaninsa da Allah kuma yake rokonsu kuma yake neman ceto wurinsu, kuma ya ke dogaro da su hakika ya Kafirta.

3. Wanda ya ki kafirta mushirikai, ko ya yi ko-kwanton kafircinsu, ko ya inganta mazahabarsu.

4. Wanda ya ƙudurta cewa shiriyar da ba ta manzon Allah (Sallalahu Alaihi wasallam) ba, ita ce mafificiyar shiriya, ko hukuncin waninsa  shi ne mafi kyawu, kamar wanda zai fifita hukuncin Dagutu (wanin Allah) akan hukuncin Allah. Shima kafiri ne.

5. Wanda ya yi fushi da wani abu da manzon Allah (Sallahu Alaihi Wasallam) yazo dashi ko da ya aikata shi, saboda faɗin Allah madaukakin sarki :

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَرِهُوا مَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأَحْبَطَ أَعْمَالَهُمْ

Saboda sun kyamaci abinda Allah ya saukar, sai ayyukansu suka ɓaci. (Suratul Muhammad 9)

6. Wanda yayi izgilanci da wani abu daga cikin addinin manzon Allah (Sallahu Alaihi Wasallam) ko ladarsa ko ukubarsa, ya kafirta, Dalili fadin Allah madaukakin sarki:

... ۚ قُلْ أَبِاللَّهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنْتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ

kace ayoyin Allah da manzonsa Kuke yiwa izgilanci karKu kawo wani uzuri, hakika kun kafirta bayan imaninku. (Suratu-Taubah Taubah 65)

لَا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُمْ بَعْدَ إِيمَانِكُمْ ۚ ...

"Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyan ĩmãninku. (Suratu-Taubah Taubah 66)

7. SIHIRI (tsafi, bokanci, rufa ido) yana daga cikin sihiri duba da dabo, wanda ya aikatashi ko ya yarda dashi ya kafirta, dalili shi ne  fadin Allah madaukakin sarki:

... ۚ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنْ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَا إِنَّمَا نَحْنُ فِتْنَةٌ فَلَا تَكْفُرْ ۖ ...

ba sa koyarda wani har sai sun faɗa masa cewa lallai mu fitinane karka kafirta. (Suratul Bakara 102)

8. Zama ko jibintar mushirikai da taimakonsu akan musulmai. Dalili shi ne fadarSa madaukakin sarki:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْيَهُودَ وَالنَّصَارَىٰ أَوْلِيَاءَ ۘ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۚ وَمَنْ يَتَوَلَّهُمْ مِنْكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi Yahudu da Nasãra majiɓinta. Sãshensu majiɓinci ne ga sãshe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ, yanã daga gare su. Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. (Suratul Má'idah 51).

9. Wanda ya kudurce cewa wani bangaren mutane ya Isar masa ya fita daga shari'ar Annabi Muhammad (Sallalaahu Alaihi Wasallam) kamar yadda ya isarwa  Khadar fita daga shari'ar Musa (Alaihissalamu) to kafirine, saboda fadar Allah maɗaukakin sarki:

وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ

Kuma wanda ya nemi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra. ( Suratul Al-imran 85)

10. Juya baya daga barin addinin Allah, baka koyansa baka aiki dashi, dalili shi ne fadar Allah maɗaukakin sarki:

وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنْ ذُكِّرَ بِآيَاتِ رَبِّهِ ثُمَّ أَعْرَضَ عَنْهَا ۚ إِنَّا مِنَ الْمُجْرِمِينَ مُنْتَقِمُونَ

Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda aka tunãtar da ãyõyin Ubangijinsa, sa'annan ya bijire daga barinsu? Lalle Mũ, Mãsu yin azãbar rãmuwa ne ga mãsu laifi. (Suratul Sajdah 22).

Babu bambanci cikin baki-dayan waɗannan abubuwa da ke war-ware musulunci tsakanin gan-ganci da hakikancewa dajin tsoro, saifa halin Tilasci kaɗai, kuma baki-dayan waɗannan suna daga cikin girman abinda ke zama haɗari kuma abin da aka fi Faɗawa cikinsu.

Ya kamata musulmi ya gujesu, ya tsoratar kansa su,muna neman tsarin Allah daga ababen dake wajabta fushinsa, da radaɗin azabarsa. Allah ya yi dadin tsira da Aminci ga mafi alkhairin halittunsa, Muhammad sallallahu alaihi wasallam.

zancensa ya kare Allah ya yi masa rahama.

Zai iya shiga cikin kaso na huɗu da muka ambata a sama cewa Wanda ya kudurce cewa lallai Tsare-tsare  da ka'idoji  waɗanda wasu suka ƙir-ƙira suja sunnantasu, cewa sune mafifita fiye da tsarin da musulunci ya zo da shi, ko dai-dai suke dasu, ko yahalatta a hukunci dasu, ko da Kuwa ya kudurce cewa lallai hukuncin shari'a shi ne mafifici, ko tsarin musulunci baya yiwuwa a gudanar da shi a cikin wannan karni na ashirin, koshi ne sababin saɓanin musulmai, ko kawai yana gudana ne tsakanin alakar bawa da mahaliccinsa ba tare da wasu ababen da suka shafi wata rayuwar ba daban.

Hakanan zai iya shiga cikin kashi na huɗun dai, cewa wanda ya ke ganin zartar da hukuncin Allah wajen datse hannun ɓarawo ko jefe mazinaci kamamme bai dace da wannan zamaninda muke ciki ba.

Haka kuma dai zai shiga cikin wannan kason, cewa duk wanda ya kudurce cewa hukunci da wanin shari'ar Allah ya halatta a cikin mu'amala ko haddodi  ko waninsu koda bai kudurce cewa su ne mafifita akan hukuncin Shari'a ba, domin da wannan sai ya zamto ya halatta abin da Allah ya haramtar fahimtar baki dayan  malamai, wanda duk ya halatta abin da ya haramta cikin abinda yake sananne ne a addini, kamar zina, giya da riba, da hukunci da shari'ar da ba ta Allah ba, to shima kafiri ne a bisa haɗuwar maganar malamai na musulunci.

Muna rokon Allah ya datar damu akan dukkan abunda yakeso yarda dashi, ya shiryar damu dasauran musulmai hanya madai-daiciya lallai shi mai jine makusancine gamai kiransa, tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad da iyalansa da sahabbansa baki-daya.

WALLAHU A'ALAMU.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments