Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Hadasi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, na kasance idan wasanni sun auku a tsakanina da mijiina ko kuma idan tunani ya kama ni, sai wani ruwa mai yauƙi ya riƙa fito mini, to wai sai na yi wankan tsarki idan hakan ya faru?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Abin da kike gani ɗaya ne daga cikin abubuwan da suke janyo hadasi ga mutane idan sun fito musu:

[1] Akwai masu fitowa daga kowane irin mutum namiji ko mace, kuma babba ko ƙaramin yaro, su ne: Tusa da kashi da suke fitowa ta dubura. Fitsari wanda ke fitowa ta gaba. Hukuncinsu: Kowannensu najasa ne. Dole ne a wanke inda suka fito kawai, a sake alwala. Wurin da suka shafa kuma dole sai an wanke shi da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa. Sai dai fitsarin jariri a kan tufa, shi ba sai an wanke ba. Idan aka jiƙa tufar da ruwa kawai ya wadatar.

[2] Sai kuma waɗanda suke fitowa daga manyan mutanen da suka balaga, su ne: Wadiyyi da maziyyi da maniyyi.

WADIYYI: Ruwa ne fari mai kauri da yake fitowa yawanci a ƙarshen fitsari. Kuma yana fitowa yawanci daga tsofaffi ne. Hukuncinsa iri ɗaya da na fitsari ne: A wanke inda ya fito da inda ya taɓa kawai, a sake alwala.

MAZIYYI: Ruwa ne tsararo mai yauƙi, yana fitowa a lokacin ƙaramar shaawa, kamar a lokacin tunani a kan shaanin jimai, ko kallon shaawa ga alaurori, ko wasannin shaawa a tsakanin miji da mata. Ba ya tunkuɗar juna wurin fitowarsa, yawanci ba a ma ji ko sanin fitowarsa sai dai a ga jiƙewa kawai. Hukuncinsa shi ne: Shi najasa ne, don haka sai a wanke duk inda ya shafa da dukkan al’aurar da ya fito daga cikinta, sannan kuma a sake alwala. Idan ya shafi tufafin matasa an yi sassauci cewa a jiƙa wurin da ruwa kawai maimakon wankewa.

MANIYYI: Ruwa ne fari mai kauri (a wurin namiji), yana tunkuɗar juna a lokacin fitowarsa, kuma yana janyo sakewar jiki bayan fitowarsa. Yana fitowa ne a lokacin babbar sha’awa, kamar a lokacin saduwar jima’i, ko wasa da gaba (istimna’i). Yakan fito a cikin barci kamar yadda yake fitowa a farke. Hukuncinsa: Ba najasa ba ne a maganar da ta fi ƙarfi a wurin malamai. Amma kuma yana wajabta yin wankan da ake kira wankan janaba a bayan fitowarsa.

[3] Akwai kuma waɗanda suke fitowa ta gaban manyan mata kaɗai su ne: Haila da nafasi da kuma istihala.

HAILA: Jini ne da yakan fita daga gaban mace a lokacin da ta balaga, ba don wani dalili na rashin lafiya ko wata larura ba. Jini ne na al’ada, wanda ba shi da wani iyakantaccen adadi ta fuska yawa ko kwanaki. Yana maimaita fitowa yawanci a kowane wata guda ne. Hukuncinsa: Mai haila ba za ta yi sallah ba, ba za ta yi azumi ba, ba za ta yi ɗawafi ba, ba za a sadu da ita ba, kuma ba za a sake ta ba. Bayan ɗaukewarsa wajibi ne ta yi wankan da ake kira wankan haila. Tana rama azumman da ba ta yi ba a lokacinsa, amma ba za ta rama sallolin ba.

NIFASI: Jini ne da ke fitowa saboda dalilin haihuwa, Mafi yawan kwanakinsa kwana arba’in ne saboda hadisi sahihi da ya zo a kan haka. Don haka, idan ya kai kwana arba’in sai mace ta yi wanka, ta cigaba da sallah, da sauran ayyukan ibada. Haka ma idan ya ɗauke kafin cikan kwanaki arba’in ɗin. Hukuncinsa daidai da haila ne.

ISTIHAALA: Jini ne da yakan fita a dalilin wata matsala ta rashin lafiya a cikin mace. Yakan zama ya karu a kan adadin kwanankin haila a wurin mace. Hukuncinsa: Ba ya hana komai daga cikin abubuwan da haila ko nifasi ke hanawa. Sai dai dole ne mai Istihaala ta sake alwala ga kowace sallah. Kuma tana iya yin wanka ta haɗa salloli biyu da suka haɗa lokaci: Azahar da La’asar ko Maghriba da Isha’.

[4] Daga cikin waɗannan matsalolin, duk wanda ya janyo wanka kafin a samu tsarki, kamar fitar maniyyi ko haila ko nifasi, shi ne ake kira: Babban

kuma Wanda kuma ya janyo alwala, kamar fitar fitsari ko kashi ko maziyyi da sauransu shi ne: Ƙaramin Hadasi.

[5] Kuma waɗannan abubuwa suna zama hadasi ne kaɗai idan sun fito ta fuskar lafiya ta hanyar da aka saba, amma duk lokacin da suka fito ta fuskar rashin lafiya, kamar idan suka wuce iyaka a wurin yawa da lokacin fitarsu, to sun zama larura. Kuma ba za su hana komai ba na sallah ko azumi ko ɗawafi da sauransu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments