Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mijin Da Ya Siffanta Matarsa Da Mahaifiyarsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, malam. Barka da rana, yaya aiki? Allah ya yi mana jagoro, ya saka maka da alkhairi. Malam, don Allah ya hukuncin auren da miji ya ce da matar, yana mata kallon Kirista saboda irin ɗabi’unta? Sannan kuma ya ce, yana mata kallon uwarsa: Yadda ba zai haɗa gado da uwarsa ba, haka ita ma ba zai haɗa shimfiɗa da ita ba?!

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

1. Yana daga cikin haƙƙoƙin mace a kan mijinta, ya kiyaye harshensa a kanta, kar ya riƙa munana mata a wurin zagi ko aibatawa. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

سِبَابُ الْمُسْلِمِ فُسُوقٌ ، وَقِتَالُهُ كُفْرٌ

 Zagin Musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙi da shi kafirci ne.

Kuma an taɓa tambayar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) game da haƙƙin matar ɗayanmu a kansa?  Sai ya ce:

أَنْ تُطْعِمَهَا إِذَا طَعِمْتَ، وَتَكْسُوهَا إِذَا اكْتَسَيْتَ، وَلَا تَضْرِبِ الْوَجْهَ، وَلَا تُقَبِّحْ، وَلَا تَهْجُرْ إِلَّا فِي الْبَيْتِ

 Shi ne: Ka ciyar da ita idan ka ci, ka tufatas da ita idan ka tufatu, kar ka bugi fuska, kar ka munana, kuma kar ka ƙaurace sai a cikin ɗaki.

2. Sannan kuma kamanta ta da kirista babban abu ne mai hatsarin gaske, domin zai iya ɗaukar ma'anar kafirtawa. Abu ne sananne kuwa cewa, duk lokacin da wani ya kira ɗan'uwansa da kalmar 'kafiri', to ɗayansu ya komo da ita, kamar yadda ya zo a cikin Hadisi sananne daga bakin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Allaah Ta'aala ya kiyaye.

3. Amma kamanta ta da mahaifiyarsa shi ake kira: ZIHAARI , wanda Allaah Ta'aala da kansa ya siffata masu yinsa da cewa:

وَإِنَّهُمْ لَيَقُولُونَ مُنْكَرًا مِنَ الْقَوْلِ وَزُورًا

 Kuma lallai ne, suna faɗin abin ƙyama na magana, kuma da ƙiren ƙarya.

4. Don haka, abin da ya wajaba ga mai aikata wannan shi ne: Bayan tuba da istigfari sai kuma dole ya yi Kaffara: Ya nemi baiwa ya 'yanta ta; in kuwa ba zai iya ba sai ya yi azumin watanni guda biyu a jere; idan kuma ya kasa, to sai ya nemo talakawa guda sittin ya ciyar da su.

5. Sannan kuma dole ne ya fara yin wannan kaffarar tun kafin ya ƙara komawa ga saduwa da matar, kamar yadda Allaah Maɗaukakin Sarki ya ambata a farkon Suratul Mujaadalah.

قَدْ سَمِعَ اللَّهُ قَوْلَ الَّتِي تُجَادِلُكَ فِي زَوْجِهَا وَتَشْتَكِي إِلَى اللَّهِ وَاللَّهُ يَسْمَعُ تَحَاوُرَكُمَا ۚ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ بَصِيرٌ

Lalle Alla Ya ji maganar wadda ke yi maka jãyayya game da mijinta, tanã kai ƙãra ga Allah, kuma Allah nã jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments