𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Tambaya: Wasu mutane ne suke ce wa: Auren ƙananan
yaran da ba su kai lokacin balaga ba bai dace da koyarwar musulunci ba. Sannan
kuma wai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ma ya auri A’ishah Ummul-Mumineen (Radiya Laahu Anhaa)
ce a lokacin tana ’yar
shekaru goma sha-takwas (18)! Menene gaskiyar wannan magana?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
[1] Aya ɗaya daga cikin Ayoyin Alqur’ani da suka zama hujja
a kan halaccin aurar da ƙaramar yarinya, ita ce Ayar Suratul Talaaq:
وَٱلَّـٰۤـِٔی یَىِٕسۡنَ مِنَ ٱلۡمَحِیضِ مِن نِّسَاۤىِٕكُمۡ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَـٰثَةُ أَشۡهُرࣲ وَٱلَّـٰۤـِٔی لَمۡ یَحِضۡنَۚ ... ٤
Kuma waɗannan da suka ɗebe tsammani daga samun haila daga cikin
matanku, idan kuka yi shakka, to iddarsu watanni uku ne, haka ma waɗanda ba su fara hailar ba.
(Surah
At-Talaaq: 4)
A nan ya tabbatar da iddar macen da ba ta fara
haila ba saboda yarantaka: Cewa daidai ta ke da macen da ta daina haila saboda
tsufa, watau watanni uku. Haka manyan
malaman Tafseer irinsu: Ibn Abi-Haatim, da Ibn Jareer, da Ibn Katheer, da
Al-Qurtubiy, da Al-Jallaalaini, da sauransu suka bayyana. Har ma da As-Shaikh
Abubakar Gummi a cikin tafsirinsa: Raddul Azhaan.
Wanene ya isa a yau ya ce: Waɗannan malaman na-da da na-yanzu, mabiya
Sunnah daga cikinsu da akasinsu, wa ya isa ya ce wai: Ba su yi wa wannan ayar
kyakkyawar fahimta ba a wurin fassarorinsu da nasihohinsu ga al’umma?!
[2] Abu ne sananne kuwa, in ji malamai cewa: Babu
idda ga wannan irin matar sai a bayan sakin aure ya auku gare ta. Sannan kuma
babu saki sai a bayan an ɗaura
mata aure.
Daga nan ya fito fili a bayyane cewa: Auren ƙaramar
yarinyar da ba ta fara haila ba halal ne a addinin musulunci. Domin in da ba
haka ba, da bai hukunta yin idda a gare ta ba.
Wa ya isa a yau ya soke wannan halaccin na Allaah
ga wanda yake son yin aiki da shi daga cikin Musulmi?!
Abu ne sananne ba sai an faɗa ba cewa: Ɗaura aure da ƙaramar
yarinya ba shi ne kuma ke halatta saduwa da ita ba. Saduwa da ita yana halatta
ne kaɗai a
lokacin da ta ke iya ɗaukan
namiji. Shiyasa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya
auri A’ishah (Radiya Laahu Anhaa) bai tare da ita ba sai bayan shekaru uku,
kamar yadda Hadisai Sahihai suka yi bayani.
[3] Game da auren A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa)
kuwa, malaman Hadisi irin su: Al-Bukhaariy da Muslim da Abu-Daawud da
At-Tirmiziy da An-Nasaa’iy da Ibn Maajah da Ad-Daarimiy da As-Shaafi’iy da
Ahmad da Abdurrazzaaq da Ibn Abi-Shaibah da At-Tabariy da Al-Humaidiy da
At-Tayaalisiy da Al-Hakim a Al-Baihaqiy ne suka riwaito ta hanyoyi sahihai masu
yawa a cikin littffansu na As-Sihaah da As-Sunan da Al-Masaanid da Al-Ma’aajim
da Al-Mustadrakaat da sauransu, daga A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) ta ce:
‘Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya aure ta ne a lokacin tana
’yar shekaru shida a Makkah kafin hijira, sannan kuma ya tare da ita a lokacin
tana ’yar shekaru tara a Madinah bayan hijira.’
Wa ya isa ya san haƙiƙanin lokaci da yanayin
aurenta fiye da ita kanta? Kuma wa zai iya bugun-ƙirjin cewa duk waɗannan malaman da malamansu da suka riwaito
wannan maganar da isnadai sahihai ingantatu har zuwa gare ta cewa ba daidai
suka yi ba?!
[4] Abin da ya ƙara nuna cewa a lokacin ƙulla
aurenta da tarewarta, A’ishah
(Radiyal Laahu Anhaa) tana ƙaramar yarinya ce akwai:
(i) Lilo da take wasa a kansa tare da ƙawayenta
har a ranar tarewarta.
(ii) Ga kuma kayan wasa irin na yara ƙanana
da ta ke wasa da su tare da ƙawayenta har a bayan tarewarta.
(iii) Sannan kuma a cikin ƙissar Al-Ifku , inda aka
ƙulla mata sharrin da ya cutar da ita da mijinta da sauran muminai, baiwar
gidansu: Barirah ta tabbatar da cewa: A’ishah ƙaramar yarinya ce wadda take iya yin barci ta bar awaki su cinye garin
abincin mutanen gida.
(iv) Haka ita da kanta ma ta siffata kanta da
cewa: Ita ƙaramar yarinya ce mai sha’awar kallon wasa, a lokacin da Habashawa suke wasa a ranar Idi.
(v) Haka nan kuma a lokacin Hajjatul Wadaa’i ita
da kanta ta ambaci cewa: Ita yarinya ce ƙarama da take gyangyaɗi a kan taguwarta a cikin tafiya.
Waɗannan
duk riwayoyi ne sahihai a cikin Sahih Al-Bukhaariy da Sahih Muslim da sauransu.
Bayan wannan wace magana ce kuma za a yarda da
ita, har ta zama dalilin soke kasantuwar A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) a
lokacin aurenta da tarewarta cewa ƙaramar yarinya ce?!
[5] Sannan kuma ba Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ne shi kaɗai ya
yi irin wannan auren na ƙaramar yarinya ba, ballantana wani ya kafa hujja
da cewa Khususiyyarsa ce. Sahabbai da Malamai masu yawa sun bi irin wannan
hanyar, har ma Aliyyu Bn Abi-Taalib ya aurar da ’yarsa Ummu Kulthum ga Umar Bn Al-Khattaab
(Radiyal Laahu Anhumaa) a lokacin tana ’yar ƙaramar yarinya, a cikin shahararriyar ƙissar da malamai irin su
Sa’eed Bn Mansuur da
Abdurrazaaq da Ibn Abdil-Barr da Al-Baihaqiy da Ibn Ibn Hajr (Rahimahumul Laah)
suka riwaito a cikin littaffansu.
To, wane musulmi ne ya isa yau ya ce: Hanyar da waɗannan manyan magabatan suka bi mummunar
hanyar ɓata
ce, ba daidai ba ce?!
[6] Don haka, Malamai irin su: An-Nawawiy da Ibn
Qudaamah da Ibn Al-Munzir da Al-Baghwiy da Ibn Hazm da Ibn Katheer da Ibn Rushd
Al-Hafeed (Rahimahumul Laah) suka tabbatar da cewa: Malaman Musulunci sun yi
ijmaa’i a kan halaccin mahaifi ya aurar da ’yarsa ƙarama ko ɗansa ƙarami kafin lokacin
balagarsu.
To, waye kuma daga cikin musulmi a yau ya isa ya
ce: Al’ummar musulmi tun a farko ta haɗu ne a kan ɓata ko kuskure, sai shi da mabiyansa a wannan
zamanin na-ƙarshen ne suka gano daidai?!
[7] Sannan kuma kamar yadda Malaman Fiqhu suka
tabbatar, hukuncin wannan auren na yara ƙanana da ba su kai lokacin balaga ba:
Halacci ne kawai, amma ba wajibci ba. Don haka, daga cikin Malamai babu wanda
ya ce wajibi ne a yi wa yaran da ba su kai lokacin balaga ba aure. Amma kuma ba
haram ba ne, saboda da dalilan da suka gabata.
Don haka, babban kuskure ne a hana mai son yin
aiki da wannan halaccin daga cikin musulmi yin aiki da shi. Kuma babu dalilin
tayar da hayaniya da ɗaga
jijiyoyin wuya a kan mas’alar in dai ba da wata muguwar manufa ba ce a ɓoye.
[8] Kasantuwar waɗansu a duniyar yau suna ƙyamar
yin aure da wuri, ko kuma ba ya ba su sha’awa ko ba ya burge su, ko kuma ba shi daga cikin al’adarsu, wannan ba dalili ba ne a kan soke
halaccinsa ga musulmin da ya yi sha’awar yinsa.
Haka nan dai kasantuwar Sahabbai (Radiyal Laahu
Anhum) da Mabiyansu da kyautatawa (Rahimahumul Laah) a zamunnan da suka gabata,
sun yi aiki da wannan halaccin, wannan dalili ne kan cewa halaccin yin auren ƙananan
yara ba keɓantaccen
hukunci ne ga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) shi kaɗai ban da sauran al’ummarsa ba.
[9] Haka kuma dayake kamar yadda kowa ya sani,
sha’awar jima’i ta fi ƙarfi a kan matasa sababbin balaga ne. Ashe wannan
bai zama dalili a hankalce ba ma a kan cewa: Hana yin auren wuri ko takura
hanyoyin samunsa a tsakanin matasan da suka buƙatu gare shi, waɗanda kuma suke da irin waccan siffar da
aka ambata, ta ƙarfin sha’awa wata hanyar buɗe ƙofar
fasiƙanci ne kawai a tsakaninsu ba?!
Wane musulmi ne kuwa da hankalinsa zai yarda da
wannan hanin?
Sannan kuma meye laifin musulmin da ya ɗauki matakin tsare ’ya’yansa (maza da
mata) daga masifar muguwar sha’awar jima’in - wacce duk muka san ba ta da wani
magani - ta hanyar yi musu aure da wuri, tun kafin lokacin balagarsu?!
Kuma wane mai cikakken hankali da lura da basira
ne a yau zai ƙyamaci wannan irin auren?!
[10] Da’awar cewa akwai hatsari mai tsanani da ƙaramar
yarinya sabuwar balaga take fuskanta idan ta zo haihuwa, a nan an bayar da amsa
da cewa:
(i) Da farko dai saboda cigaban da duniya ta kai a
yau a fannonin binciken ilimin zamani masu yawa, ya sanya sai lokacin da
ma’aurata suka ga dama ne suke yarda su ɗauki ciki, ko kuma ma har su haihu.
(ii) Sannan kuma ana ji da ganin yadda yaran mata ƙanana
masu cikunnan-shegu suke ta haihuwa a gidajensu, ba tare da wata wahala ko
matsala ba, kuma ba tare ma da zuwa asibiti ba. To, ta yaya za a ce sai sa’o’insu ma su auren Sunnah ne za su sha ‘baƙar wahala’ a
lokacin haihuwarsu?!
(iii) Sannan kuma masu bibiyan kafofin yaɗa labarai na-ciki da wajen ƙasar
nan sun sha ji da ganin cewa: An samu yarinya ’yar shekaru tara da haihuwa ta haihu, kuma
lafiya ƙalau ba tare da wata matsala ba!!
Duk waɗannan dalilai ne masu ƙarfi a kan cewa: Babu
wata mummunar matsala mai hatsari a kan auren ƙananan yara mazansu da
matansu, fiye da irin matsalar da takwarorinsu manyan balagaggu suke samu,
kamar irin matsalar rashin samun kyakkyawar kulawa tun daga lokacin shigar ciki
har zuwa lokacin haihuwa.
[11] A ƙarshe dai, muna ƙara jaddada cewa a wurin
malaman musulunci hukuncin auren ƙananan yara halacci ne kawai, amma ba wajibci ba
ne. Don haka, kar wani ya kafa dalili da shi a kan mu cewa: Me ya sa a yau ba
mu ganin kuna aura, ko kuna aurar da yaranku ƙanana?
Domin kasantuwar cin nau’in abinci kaza, ko sanya
nau’in tufafi kaza, ko hawa nau’in abin-hawa kaza, ko zama a nau’in gida kaza
ya halatta, wannan bai nuna cewa dole sai kowa ya yi ba. Amma idan har hakan
zai kai ga yin watsi ko kuma ƙaryata wasu nassoshi daga cikin Al-Kitaab
Was-Sunnah , ko zai kai ga a yi musu gurguwar fassara don kare muradan wasu
manya ko ra’ayin
wasu ’yan
duniya, to ya zama dole a fayyace komai.
Sai a ƙara kiyayewa.
[12] Kafin mu dakata yana da kyau mu san cewa: A
wannan zamanin daga cikin malaman musulunci da suka fara rubutu a kan wannan
matsalar ta soke halaccin auren-wuri, da janyo shakku a kan shekarar auren
A’ishah Ummul-Mu’mineen akwai wani Al-Ustaaz Ahmad Muhammad Jamaal, wanda ya
rubuta wannan ra’ayin a cikin Mujallar Al-Faisal ta watan Rabi’un Al-Awwal,
1398H. Amma daga baya ya janye wannan ra’ayin shi da kansa, bayan ’yan kwanaki,
wataƙila saboda ƙarin bincike da kuma raddodin malamai.
Bayan shekaru ne kuma sai wani Dokta As-Sayyid
At-Taweel na Jami’ar Ummul-Quraa da ke Makkah ya sake farfaɗo da wannan ra’ayin, inda shi kuma ya yi
rubutu a kan sa a cikin jaridar Al-Madinah ta ranar 1/Sha’abaan/1404H. Don haka
ne kuma wani malami da yake karatun Dokta a kan Al-Hadeeth Wa Uluumuhu:
As-Shaikh Khaleel Ibraaheem Mulaa Khaatir, mazaunin Madinar Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), ya rubuta masa kyakkyawa kuma
gamsasshen martani a cikin wani ɗan
littafi da ya sanya wa suna: Zawaaju As-Sayyidah A’ishah Wa Mashruu’iyyatu Zawaajil
Mubakkir a shekarar 1405H.
Allaah ya shiryar da mu, ya ƙara mana fahimta a cikin
addininmu, kuma ya kare mu daga sharrin masharranta, a duk inda su ke.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.