Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halasta A Cigaba Da Girka Abincin Da Mamaci Ya Bari?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam alaikum Mallam, tambayata a yau ita ce, shin idan mamaci ya bar abinci, watau kayan abinci kamar masara ko shinkafa ya halasta a cigaba da girka shi, ko sai an yi rabon gadonsa tukunna? Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, Game da girka abincin da mamaci ya rasu ya bari za a dubi abin ne ta fuskoki guda biyu kamar haka:

1. Girka abincin da ya bari domin buqatar iyalansa kafin a raba gado, wannan ya halasta iyalan mamaci su girka abincin da ya bar masu domin su ci, saboda dama ai su ya tattalar mawa ba waninsu ba, sai dai ana son a hanzarta raba gadon saboda kar a yi ta cin dukiyar tana ja baya ba tare da an raba ta ba, saboda a cikin yara wata qil akwai wanda ba ya amfana sosai da wannan girkin kasancewarsa bai qware da cin abinci ba.

2. Girka abincin da mamaci ya bari don a raba wa masu zuwa ta'aziyya, wannan ya saɓa wa sunnar Manzon Allah , saboda lokacin da Ja'afar ɗan Abu Ɗalib ya rasu, Annabi sai ya ce: "Ku yi abinci ku aika wa iyalan Ja'afar, saboda mai shagaltarwa ta zo masu". Wato mutawa ta zo masu. Tirmizhiy 998, Abu Dáwud 3132, Ibn Majah 1610.

 Wannan hadisin ya nuna cewa idan aka yi wa mutanen wani gida mutuwa, to aika masu da abinci aka shar'anta a yi, ba wai su ɗin su ɗebo abincinsu su riqa dafawa mutane ba kamar yadda ake yi a wasu wurare a halin yanzu, yin hakan ya saɓa wa sunnar Annabi .

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments