TAMBAYA (03)❓:
Assalamualaikum warahmatullah. Fatan muntashi lfy
yakokari. Allah yayimn jagora ameen.
Dan Allah malam me menene gaskiyar wannan (👇)
FROM DR ISAH ALI PANTAMI.
IYAYENMU MATA GA WATA FATWA, DON ALLAH ADAURE AYI
1.Idan ki katashi da asuba kafin ki yi wa kowa
magana sai ki dafa kan yaro koda yana barci sai ki karanta.
(Ihdina ssiradal mustakim ) 41 ki kwana 7 ban da
fashi, to koda yaro ya fara rashin ji Wallahi zai daina, wannan mujarrabi ne
kada a yi sakaci, ku yi wa yaran ku za ku ga natsuwa ta mamaki a tare da su
2. Idan yaranmu suna cikin barci a tofa musu inna
anzalnahu kafa daya a gabansu da kirjinsu kafa dai daya bazasu tafa kusantar
wani da miji ba inba mijinsu ba haka maza ma
3.Uwa takaranta Suratul Fatiha daga farko zuwa
karshe kafa arba'in da daya 41 tsakanin magariba da Isha. Allah zai shiryarmata
yaranta su zama masu hankali masu ladabi
da biyayya da tausayin iyaye
3.Idan yaranmu zasu kwanta suyi barci sai a tofa
musu Bismillah a midigarsu kafa bakwai Yana Buda kwakwalwa
4.Don Allah ki turawa kowa kada ki manta da mutum
ko da daya, Rabbi gifirli minkulli zambin wa'atubu ilallahi idan kika turawa
kawarki wannan, Allah zai yaye miki
kowacce irin matsala idan kika dogara da Allah.
Allah Ya datar da mu, domin QudurarSa.
AMSA:
USMANNOOR: Wannan karya ce kawai aka yiwa Malam.
Sunan wannan laifin "Plagiarism" ma'ana neman suna da sunan wani
wanda ya shahara kuma babban laifine ko a hukumance ballantana kuma a addinance
Akwai wadanda kawai suke zama su tsara rubuce
rubuce marasa tushe irin wadannan kuma su danganta hakan ga Malaman addini
Karya suke masa kuma indai basu nemi yafiyar
malamba to tabbas Allah ba ya yafe laifin wani akan na wani
A iya sauraren karatuttukana da kuma binciken da
nake ban taba jin makamanciyar wannan addu'ar ba daga bakin malaman Ahlus Sunnah
wal jama'a
Kara karanta addu'o'in zaki fahimci da akwai
kuskure dayawa da kuma karancin ilimi. Kamar abin da marubucin ya ce wai idan katashi
kafin kayiwa kowa magana (To wanene ya ce idan addu'a zata amsu saidai sharadin
hakan yazamo ba wanda zakayiwa magana da asubar fari ?)
Wai a kwana 7 banda fashi, kenan idan aka kwana 6
sai wani uzurin yasa akai fashi a kwana na 7 shikenan addu'ar bazata amsu ba
kenan (Inaga ko marubucin bai karanta hadisin "Innamal a'amali
binniyyati" ba) la'akarida duk niyyar da uwar yaron tayi baza'a amsaba sai
an jera kwanaki 7 cir. Wannan ma bidi'a ne a addini
Da ya ce ko da yaron ya fara rashin ji wallahi zai
daina, to a wanne hadisin ya dauko wannan addu'ar, na tabbata dai marigayi
Shaikh Sa'id Alqataani bai kawota ba a cikin Hisnul Muslim. Idan kuma marubucin
yana da hujja to kice wadanda sukai miki sharing rubutun su tambayesa ya kawo
hujjar (Ballantana ma bazai samu hujjar ba a cikin sahihan hadisai)
Na 2 ya ce a tofa Suratul Qadr, to ina marubucin
yabaro karanta Surorin Mu'awwidathayn (Falaqi da Nasi) da qarin Suratul Ikhlas
(kamar yanda Shaykh Pantami ya kawo hujjarsa a cikin Sahihul Bukhari hadisi mai
lambata 5748) a tofawa yara don nema musu kariya daga mutum da aljan ? Ina ya
baro sahihin hadisin da Ma'aiki SAW ya ce: Duk wanda ya kwanta da alwala kafin
yayi bacci, Allah SWT zai sa Mala'iku 2 suyi gadin mutum har gari ya waye ?
Na 3, naji marubucin ya ce uwa ta karanta Fatiha
sau 41, a ina aka iyakance adadin Fatiha sannan kuma tunda Ma'aiki SAW aka
saukarwa da Qur'aninnan sai mu tambayi marubucin shin Ma'aiki SAW ya taba
karanta Suratul Fatiha sau 41 ga yar sa Nana Fatima ko ga dansa Ibrahim ?
Shin Annabi SAW da sahabbai su suka fimu fahimtar
Qur'ani sai suka manta basu koyarda falalar hakan ga yayansu ba ko kuma shi
marubucinne yayi qiyasi ya gano hakan, har ya sha'afa bai kawo mana hujja ba ?
A tofa musu Bismillah kafa 7 a madiga, wanene ya
koyar da hakan ? Ma'aiki SAW, sahabbai, tabi'ai ko kuma tabi'uttabi'un ?
Na 4 menene hujjar marubucin na tabbatar da cewar
Allah zai yaye damuwar duk wanda yayi sharing saqonnasa ? Da ya ce a turawa
kowa kada a manta da ko mutum daya, (indai har ya tabbata rubutun haka yake
daga asalin wanda ya rubuto) to tabbas marubucin yana fama da cutar jahilci
domin kuwa Annabawa da Manzanni ne kawai sukeda tabbacin ga abin da zai faru ga
wane shima sai Allah ya sanardasu domin kuwa babu masanin gaibu sai Allah SWT.
Kuma sanin kanmune Annabta ta kare daga kan Ma'aiki SAW kamar yanda ya fada a
sahihin hadisi
Don haka irin wadannan yaye-yayen rubuce-rubucen
sunanan sunata yawo a media platforms kuma marasa ilimi ne suke yadasu don wata
manufa tasu suna dilmiyar da wasu a rashin sani. Allah yasa su gano
kuskurennasu tukunna domin kuwa saima sun gane mistake din sannan zasu tuba
A karshe kuma zanso na nusar dake irin addu'ar da
Annabi SAW yake yiwa jikokinsa wato Hassan da Hussaini bin Ali (Allah ya kara
musu yarda baki daya) wadda ta tabbata a cikin sahihan hadisai, kamar yanda
Shaikh Sa'id Alqataani (Rahimahullah) ya kawo a cikin littafinsa na Hisnul
Muslim (Asaka mawallafin littafin a addu'a domin kuwa a satinnan ya koma ga
MahaliccinSa)
Inda ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan
addu'ar (Harma ya ce babanku {Annabi Ibrahim AS} yana yiwa yayansa {Annabi
Ismail da Ishaq} ga addu'ar kamar haka:
أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.
"O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min
kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah"
Bi ma'ana: "Ina neman muku tsari da kalmomin
Allah cikakku daga dukkan shaidan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani
mai kambun baka, mai cutarwa"
(Shaykh Pantami yakawo hujjarta a cikin Sahihul
Bukhari hadisi mai lambata 3371)
Sannan kuma tun ran gini tun ran zance, akan yi
tuya a manta da albasa ma'ana mutane sukan manta da addu'ar da Annabi SAW ya
koyar kafin tarawa da iyali, wadda rashin yinta kan iya kawo yiwuwar a haifi
yaro kangararre yazo ya dameku ya dami al'umma da shaidanci domin kuwa sakacin
rashin neman tsarin Allah ne daman yasa shaidan kan shafi abin da Allah ya
azurta ma'aurata tunma kafin a haifi yaron, addu'ar itace kamar haka:
بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
"Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan,
wajannibish-shaytana ma razaqtana"
Ma'anarta: "Da sunan Allah. Ya Allah! Ka
nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka
azurta mu da shi"
Sannan kuma shima Prof. Pantami yakawo wannan
addu'ar harma ya kafa hujja da cewar tana cikin Sahihul Bukhari tareda Fathi
4/181, harma ya ce ba abin mamaki bane idan kaga shaidanin yaro a wannan
zamanin, kana bin salsala zakagano iyayensa basuyi waccan addu'ar bane
Don haka wadannan sune wasu daga cikin sahihan
addu'u'o'in da suka inganta daga Ma'aiki SAW, batun wadancan kuma a barsu a
inda suke. Muna roqon Allah ya bamu ikon fahimtar addini dakuma aiwatar dashi,
ya Allah ka tabbatardamu bisa tafarkin magabata na qwarai (Salafus salih)
Wallahu ta'ala aalam
Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu
anla'ilaha illa anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk
Amsawa:
✍Usman
Danliti Mato, Usmannoor_Assalafy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
WHATSAPP👇
https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX
https:///
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.