Ticker

6/recent/ticker-posts

Hausa

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Hausa

8.  Hausa tana cikin harasan magabata,

 Cikin tsaranta Rabbu shi ne ya ɗaga ta,

Ya sauƙaƙa laffuza da tsarin harufanta,

Kalmominta har da tsarin jimlarta,

  Ba tamka gare ta sauƙin ganewa.

 

9.  Don haka nan Afirka ta zam shakundun,

 Ta haɓɓaka tai kama da teku ruwa kundun,

 Wasu ‘yan harsuna, su faɗa ciki tsundum,

 Ta yo mamaya ta zamto shakundun,

  In an ambace ta ba mai motsawa.

 

10. Ta bunƙasa ta zamo harshe babba,

 Wannan nahiya kusan ba wani babba,

 Ba lungun da Hausa ba ta kutsa ba,

 Kai har Chana yanzu ni ban ɗebe ba,

  Ta shiga duniya ga tsarin sadarwa.

 

11. Gun nazari ku lura nan taf fi fitowa,

 An yo digiri cikinta sun wuce ƙirgawa,

 Ana nazarinta har ƙasashen Turawa,

 Ga ta da maluma suna ilmantarwa,

Masana sun yaba da Hausa ga koyarwa.

 

12. Masana harsuna tuni sun ka amince,

 Sun daddale ta har sun ƙwanƙwance,

 Sun yarje ma Hausa ikon Allah ce,

 Ta haɓɓaka duniya abin ai ta kwatance,

  Babu kamar ta yaɗuwa mai dogewa.

 

13. Ga ta da hanƙurin wuya ga kutsawa,

 Al’adunta na da tsarin burgewa,

 Gun adabinta nan ake ilimantarwa,

 Ga harshenta na da sauƙin kamawa,

  In aka zo fagen aro ta fi ƙwarewa.

 

14. Ta dai mamaye Afirka da gefenta,

 Kai ka ce wutar da daji taka rurinta,

 Haka taka mamayar harasan gefenta,

 Har ma ƙetare tana baje kolinta,

  Ta yi barazana ga harshen Turawa.

Post a Comment

0 Comments