Ticker

6/recent/ticker-posts

Babi Na Daya Gabatarwa - Daga Tahamisin Wakakken Ka’idojin Rubutun Hausa


Babi Na Ɗaya

Gabatarwa

1.  Har kullum da nai nufin faro furci,

To Allah ke a fari Sarki Majiɓinci,

Na kiri Alimun Azizun Makaɗaici,

Ƙara min hikkima da ilmi Mawadaci

Mai hikima buwaye Sarkin ƙagawa.

 

2.  Na yi salati gun Nabiyi HabibinSa,

Da iyalai har da dukka Sahabunsa,

Sa mana masu dauwama a tafarkinsa,

Tashe mu da su a lahira daf gefensa,

Manzon nan da an ka aiko shiryarwa.

 

3. Sai mu yi godiya ga Allah da daɗawa,

Salati ga nabiyu babu ranar ƙarewa,

Kan bautar Ubangiji ba mu ɗagawa,

Dukka haninsa mui na’am sai amsawa,

Don baiwarSa gun mu ta wuce ƙyargawa.

 

4.  Ya ƙage mu kan halitta kyawawa,

A halittunSa ba ya ɗan Adam gun burgewa,

Don Shi ya faɗa da kansa, mu ba mu musawa,

Yai muna ɗaukaka da harshen sadarwa,

  Tarin laffuza da zancen furtawa.

 

5.  In bayan Ka Rabbu da mun dabirce,

Duk lamurranmu da tuni sun lalace,

Ji da ganinmu Rabbu sai da ka lamunce,

In ba taimakonka da mun susuce,

  Mun rikice mu dambale sai ruɗewa.

6.  Kai kai harsuna ka shiryar da mutane,

 Da su muka zantuka a ƙauye da birane,

 Hikimar Jalla ce muke rubutunmu na zane,

 Ya bambanta harsunan nan ga mutane,

  Ga su wuri guda abin na saɓawa.

 

7.  Duk hikimar mutum ga harshe ka saka ta,

 Wajen magana da nazzari sai mun sa ta,

 Ko da bincike na ilmu dolenmu a sa ta,

 Masu fasaha da sha’irai ke mulkinta,

  Nan aka gane haziƙi mai burgewa.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

Post a Comment

0 Comments