Ticker

6/recent/ticker-posts

Ekowas Ba Mu Yarda Da Yaƙi Ba - Ta Farfesa Aliyu Muhammad Bunza

ECOWAS Ba Mu Yarda Da Yaki Ba - Ta Prof. Aliyu Muhammad Bunza

1.              Ya mai shiryar da al’amari,

Ahadun ɗaya tal guda wuturi,

Ya wanda abin da yai ƙuduri,

Ya kasance ce kakai katari,

        Ba sai Ka tsawata masa ba.

 

2.              Gatan bayi Ilaahu Gwani,

Bayan Kai babu duk masani,

Ya mai hasken da ba lagwani,

Mai sa gero ya ɗau bunini,

        Ko da bai ja kara ne ba.

 

3.              Bari in yi salati gun Manzo,

Ɗan Abdullahi mai ƙwazo,

Shakundun masu zozozo,

A fagen daga da gomozo,

        Ba ku gadi gudu da raki ba.

 

4.              Jama’a ku taho ku saurara,

In an ga kure a gyaggyara,

A gaya mini ban da barara,

Duk wanda ya ce da kai: “gyara”,

        Bai so ya ji ka ji kunya ba.

 

5.              Juyin mulki musiba ne,

Mai karya ƙasa ta gurfane,

Jama’a tsaye dole kai zaune,

Karɓar mulki jidali ne,

        Ko ba da ɓarin wuta ne ba.

 

6.              In bindiga tas shigo wasa,

Mariƙanta ciki da barasa,

Kashe rayukka ya zan gasa,

Ƙato bai fara haɓɓasa,

        In ba mai bel ga ƙugu ba.

 

 

 

 

7.              In mai juyi ya yunƙurce,

Mai mulkin ko ya jajirce,

Tilas jama’a su gigice,

Sai hankulla su dabirce,

        Ƙarshen ba zai yi kyawo ba.

 

8.              Don mai abu ja maras abu ja,

Tilas sai an yi ja-in-ja,

Shi ne aka cewa aiki ja,

Matuƙar ta kai ga wurja-

        Njan kowa ba za shi dara ba.

 

9.              Matsalar Nijar idan ka kula,

Sojojin har farar hula,

Manufarsu ƙasar ta zan jalla,

A yi boren kore ‘yan taula,

        Ba turmuje ‘yan siyasa ba.

 

10.         Da ganin juyin da ba darga,

Ba ƙumajin ije riga,

Balle ɓuya cikin malga,

Nazarinmu abin da yah hanga,

          Ba mai cutar ƙasa ne ba.

 

11.         ‘Yan Nijar ke da ikonsu,

Kuma su suka juya mulkinsu,

Sun fi mu sanin muradinsu,

Su ɗai suka san dalilinsu,

          Ba su nemi mu tsoma harshe ba.

 

12.         Juyi in bai yi muni ba,

Bai tarwatsa al’amurra ba,

Bai jefa ƙasa jidali ba,

Sulhi aka yi kwatse gaba,

          Ba farma ƙasa da yaƙi ba.

 

13.         EKOWAS assha da tsarinki!

Duk an bijire wa niyyarki,

Da talakkawa da ‘yan kaki,

Da farar hula na gefenki,

          Ba su yarda a gwabza yaƙi ba.

14.         Wai me yaƙi ya amfana?

Bayan haifar da munana,

A kashe, a tsare, a ƙoƙƙona,

Sirrin kowa a tottona,

Ba a bar wani mai mutunci ba.

 

15.         Lura ga Iraqi aya ta,

Gaddafi ya zo ya fafata,

A somaliya an yi twatwata,

Ga Suriya nan cikin kwata,

          Sudan ba a more yaƙin ba.

 

16.         Ga Bosuiya Hasgobina can,

Afganistan mu leƙa can,

Koma a Ruwanda kacokan,

Rasha, yukiren mu duba can,

          Ba a kai ga biyan buƙata ba.

 

17.         Kun manta Ujukku yaƙinsa,

Basasa abin da taƙ ƙunsa,

Har yanzu muna da mikinsa,

Kanu da ubangizayyensa,

          Ba su yarda ƙasarmu ɗaya ce ba.

 

18.         EKOWAS ki tuna ƙasa ga ta,

‘Yanbanga ke da mulkinta,

Sun yaɗa ta’adda dukkanta,

Sun ɓata tsaro da tsarinta,

          Ba ku yunƙurto a gyara ba.

 

19.         Haka ziƙau za a tura mu,

Mu yi artabo da danginmu,

In tak kicime a ƙyale mu,

Mu kira ceto a kushe mu,

          Ko oho ba za a furta ba.

 

20.         EKOWAS babban kure gun ki,

Cewa a taho a tanya ki,

A shigo Nijar da yaƙinki,

Don ɗai ki biya buƙatarki,

          Ba don sulhi ga juyi ba.

21.         In dai kun lura Ɗanbaba,

Ba Nijar ce buƙata ba,

Ba nan aka son a jibge ba,

Ba su aka son a watse ba,

          Shin ko ba ku gane niyyar ba?

 

22.         Juyin mulkin ga mun duba,

Ba Nijar ce buƙata ba,

Ba nan aka son a jibge ba,

Ba su aka son a watse ba,

          Shin ko ba ku gane niyyar ba?

 

23.         Wane fetur ne cikin Nijar?

Zinari ne cikin Nijar?

Jama’ar me ke cikin Nijar?

Wace alfarma ga ‘yan Nijar?

          In ba ta cikin gida ce ba?

 

24.         An dai shaide su danginmu,

Da uwa da uba ga tsarinmu,

Bodar banza ka ware mu!

A haɗa mu hwaɗa a watse mu,

          Mu mace ba kan tafarki ba.

 

25.         Duk wata boda ku duba ta,

Da Arewa take da danginta,

Jibiya, Illela, sashenta,

Can Kamba ga Dole Kainan ta,

          Ba mu zamto ciki da falo ba.

 

26.         In har yaƙi ya barkikke,

A gidan wa za shi furcikke?

Tsumbul a Arewa ba sanke,

Mu za a mayas duman girke,

          Ba Lagas ko Ibadan ba.

 

27.         Haka ɗai mu tsaya sakin baki,

Ƙarshenta a sa mu yin tsaki!

Yaranmu da ke sako kaki,

A kashe muna su wajen tarki,

          Na ƙiyayya ba jihadi ba.

28.         Ai Chadi riƙonsu juyi ne,

Ga Mali can ta sojan ne,

Borkina da Gini duk zane,

Mulkin karɓe-a-ruga ne,

          EKOWAS ba ta je da yaƙi ba.

 

29.         Mis sa EKOWAS ta gigice,

Kowa ya gane solo ce,

Son rai ya gidadance,

Bumbunkari ɓarin zance,

          Ba za su rufe haƙƙa ba.

 

30.         Matsaloli sun ka yo biga,

Ga yunwa babu mai tanga,

Ka yi aiki ba biyan jinga,

Sufuri ya zan gudan darga,

          Ba a rayu cikin mishaɗi ba.

 

31.         Hangen Nijar ga juyinsu,

Sun lura Ubangizayyensu,

Su ke dabirta tsarinsu

Don ɗai su biya buƙatar su,

          Ba don Nijar ake yi ba.

 

32.         Rikici in za shi ɓarkewa,

Sojoji za a turawa,

In ya gaza ci da cinyewa,

To, mulkin za a juyawa,

          Ba bariki za a zauna ba.

 

33.         Tilas mu gayar da manyanmu,

Senitoci masu kishinmu,

Samman na Arewa yankinmu,

Sun jajirce ga kare mu,

          Ba su yarda a gwabza yaƙi ba.

 

34.         Allah Ya tsare ku dukkanku,

Allah Ya biya buƙatarku,

Kun dai kyauta wa danginku,

Ta tabbata kun yi bokonku,

          Ba satan jarrabawa ba.

35.         Mai kallon ba ku ganewa,

Yau duk kun sa shi ruɗewa,

Fatarmu ku ƙara dagewa,

Ku tsaya tsaf babu juyawa,

          Zai gane ba za ta miƙe ba.

 

36.         Sojoji Allah kare ku,

‘Yansanda wa ka rena ku?

SS ku tsare amanarku?

Mu dai manufarmu kare ku,

          Ba mu yarda a kai ku yaƙi ba.

 

37.         Ga dai yaƙi gida tarshe!

Manya sun hau miyar taushe,

Aka bar ku dawa a tattarshe,

Maƙiya su biyo su tattaushe,

          EKOWAS ba ta zo ta ceta ba.

 

38.         Yaƙin Boko Haram duba,

Kidinapas bas su daina ba,

Neja Delta faɗan gaba,

Da Biafara sui ƙasa babba,

          EKOWAS ba ta/san da wannan ba.

 

39.         Fetur ya ƙara halbawa,

Komai na ƙara borewa,

Albashi na ta zuƙewa,

Ga yunwa na kwararowa,

          EKOWAS ba ta ta da murya ba.

 

40.         In dai EKOWAS ta Allah ce,

Mai burin gyara hali ce,

Mai son harakar lumana ce,

Ta fito fili ta yo zance,

          Ba zancen farfaganda ba.

 

41.         In tsoho za shi ruɗewa,

Ga ido aka fara ganewa,

Leɓen zai ƙara tsukewa,

Muryarsa ta fara shaƙewa,

          Ƙaulinsa ba za a gane ba.

42.         Haka al’amari ka farawa,

Magana in ba ta dacewa,

Take jama’a ke gunewa,

Kowa zai dinga kushewa,

          Ba zai zama mai natija ba.

 

43.         Nijar dai kun ji ƙaulinmu,

Matsayinku a gunmu danginmu,

Kun tabbata ‘yan uwa gun mu,

Tarihi tun a tushenmu,

          Ba sai waƙacin Bature ba.

 

44.         Wata boda tambaɗar shirme,

Da iyakoki na giggilme,

Harshen ga na ‘yan kashe-kame,

Al’adu ga su daddame,

          An sa muna ba da son rai ba.

 

45.         Da Maraɗi da Dosso kun manta,

Illela tuno kirarinta,

Haka Dogon Dutse dukkanta,

Kangiwa a ce a rusa ta,

          ‘Yan Yeldu ba za su motsa ba?

 

46.         Daular Shanghai ga tsarinsu,

Har Oyo takai ga ikonsu,

Suka doshe gabas ga mulkinsu,

Har Nguru Borno bodarsu,

          Kabi ba daula kaɗan ce ba.

 

47.         Gobir makekiya babba,

Ta kai Nupe lokacin gaba,

A shigo Gobir a yo Kwamba,

A nufaci Maraɗi yin zamba,

          Kun san ba za a ƙyale ba.

 

48.         Daular Kanta a rusa ta,

Jangwarzo za a wa cuta,

Gayyar wayyo! Muradinta,

A kashe mu ƙasa a watse ta,

          Ba sulhu suke buƙata ba.

49.         Sarkinmu Sa’adu jigonmu,

Mai alfarma abin sonmu,

Ya jeki Yamai wakiltar mu,

Ya miƙa dukan buƙatarmu,

          Na lumana ba na yaƙi ba.

 

50.         Sarkinmu Sanusi ya kyauta,

Takanas ta Kano ya taka ta,

Da buƙatar kar a fafata,

Ya ce, tilas a sasanta,

          Ba zub da jini muke so ba.

 

51.         Shehunnai dole gai da ku,

Kun sa hikimar ga tsarin ku,

Kun bayyana duk fahintarku,

A taƙaitawar bayaninku,

          Yaƙi bai zan abin yi ba.

 

52.         Bisa kyakkyawar fahimtarmu,

Yaƙin ga da za a tura mu,

Babbar manufa a ƙare mu,

A shigo Legas a yaye mu,

          Ba Nijar ce muradin ba.

 

53.         Wa zai saka kai cikin kogo?

Ko miƙa wuya ga mai sango?

A yi mai yanka kamar rago,

Wab buɗe gaba gaban shago,

          Bai gurfanin sujuda ba?

 

54.         Baubawa bai da ganewa,

Wauta ke sa shi ruɗewa,

In ga wayo na hangowa,

Ga wuya yuƙa ka yankawa,

          Ba a san ta ga datse ƙassa ba.

 

55.         Yaƙɗan zamba ne baba,

Ba tarayya ka yaƙi ba,

Kwakwazo bai faɗan gaba,

Manta da barazanar ƙoba,

          Sababi bai san da laya ba.

56.         Tarayyar duk ƙasa ga ta,

Nijar dukkan jama’arta,

Da Afirka ta yamma dukkanta,

Mun ce “A tsaya, a dakanta”,

          Ba mu yarda faɗa da yaƙi da.

 

57.         Satomi gaya wa Harande,

Sunday, Shedarak, da Ɗankande,

Katin Thomas, janar Monde,

Ku fa ja kunnen Olulade,

          Rigimar nan ba guda ce ba.

 

58.         Ɗanfodiyo namu saurara,

Da Buhari na soja Ɗandaura,

Har Kingibe ɗan uwa ƙara,

Gumi mai wa’azin a gyaggyara,

          Daga ca ake ba ƙire ne ba.

 

59.         Kun manta Borno tushenta?

Zazzau ku karanto manyanta,

Katsinanmu biɗo bayaninta,

Gobir da zubid a tsarinta,

          Tamkar Kabi ban yi ƙari ba.

 

60.         Ka kwatanta Kano ɗabi’arsu,

Launin fata da harshensu,

Addini kasuwancinsu,

Al’adun wartsakewarsu,

          Daidai muke, ba kamar ne ba.

 

61.         ‘Yan Nijar kar a ruɗa ku,

A shigo Nijar a watse ku,

A haɗa ku faɗa da tushenku,

Bayan an watse lardinku,

          Mu duk ba za mu more ba.

 

62.         Da baƙaƙen nan da jajaye,

Da gajejjeru da dogaye,

Hausawan nan da Buzaye,

Sanwai ga Zarma kai waye,

          Ba a san ku da ƙin zumuci ba.

63.         Yarbawa kun ji ƙaulinmu,

Na san Ibo na fahintarmu,

Ku gaya wa duka ƙabilanmu,

Yaƙin ga da an ka tura mu,

          Wallai ba za mu dara ba.

 

64.         Dandanguna me kake hauka,

Kwankwambilo ce ka tura ka,

Borin ga da sun ka sa kan ka,

Iskokin nan da sun sauka,

          Ba tarewa ake yi ba.

 

65.         Bibisi na ta ruɗa mu,

Jamus na ƙara watse mu,

VOA na farautanmu,

Da Faransa ake ta gune mu,

          Mun durmuya ban mu gane ba.

 

66.         Mu fito fili mu fafata,

A ji muryoyinmu twatwata,

Ba ma tsoron a kwaɓa ta,

Yau kowa ba mu wa bauta,

          In ba Allah guda ne ba.

 

67.         Tammat Ali Bunza ya sauka,

Allah roƙon da nai gun Ka,

Ka tsare ni cikin iradarKa,

Ka yi min baiwa da ikonKa,

          Har in mutu ban yi shirka ba.


Prof. Aliyu Muhammadu Bunza,
Talata, Ogusta, 9/82023
12:01 na dare 

Post a Comment

0 Comments