Ticker

6/recent/ticker-posts

RUWA NA {ASA SAI GA WANDA BAI TONA BA (Muhallin Karin Magana A Farfajiyar Binciken Ilmi)

Takardar da Aka Gabatar a Taron {ara wa Juna Sani na [aliban Babban Digiri na Uku da na Biyu (Ph.D & M.A) a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato Ranar Asabar, 05/08/2023 da Misalin 10:00 na Safe.

www.amsoshi.com 

RUWA NA {ASA SAI GA WANDA BAI TONA BA
(Muhallin Karin Magana A Farfajiyar Binciken Ilmi) 

Daga 

Aliyu Muhammad Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto
Email: mabunza@yahoo.com
Website: www.alibunza.com
Phone Number: 08034316508

Tsakure

Ga al’ada, duk harshen da ba shi da wadatattun karin magana akan yi masa kallon naƙasasshen harshen da ba zai iya miƙewa ya yi kuka irin na kakansa mai nisa ba. Wannan bincike, an tsara shi da manufar fito da irin gudunmawar da Karin magana ke bayarwa ta fuskar haska wa masana da ɗalibai zurfin ilimin kakanninmu na naƙaltar makamar ƙabali da ba’adin rayuwar zamaninsu da namu. Hakan na daga cikin dalilan da suka hana  al’adunmu  su yi ɓatan dabo. Sakamakon haka, takardar tana da muradin ]ora mai bincike kan tafarkin da ya kamata ya bi, ya kai ga nasarar kowane irin bincike da yake so ya gudanar. Takardar ta yi ƙoƙarin sarrafa karin maganganun da suka taɓo ɓangarorin  zamantakewar Hausawa  guda 125. Alaƙar da ke tsakanin fasahar karin magana da waƙa ita ta sanya aka ƙawata wasu bayanan da waƙoƙin baka guda 10, sai rubutacciyar waƙa guda 1. Takardar ba ta kawar da kai ga bibiyar hanyoyin bincike tare da hanyar ɗora aiki ba. Wasu daga cikin sakamakon da binciken ya gano sun haɗa da: Duk wata dabara da za a bi ta binciken kimiyya, ko fasaha ko wani ilmi na ko mene ne, idan aka sa adabin karin maganan Hausa gaba za a samu sirrin gudanar da shi. Karin magana taron dangin masana ne da }wararru a fannoni daban-daban, don haka hannu da yawa ne an ko ce, yana maganin miya yamamma. a ƙarshe, an raɗa wa takaradar suna da:  RUWA NA {ASA SAI GA WANDA BAI TONA BA (Muhallin Karin Magana A Farfajiyar Binciken Ilmi).

Gabatarwa

Al’ummar da duk aka arzuta da harshe an ba ta abin da za ta zauni duniya a ilmance,  da karatun abubuwan da ke wakana a ciki. Babu wani zamani da adabin masu adabi ba ya aiki, sai zamanin da masu adabi suka wofintar da adabinsu. Tunanin wannan bincike shi ne, kallon irin gudunmuwar da karin magana ya yi wa magabatanmu suka kasance nagartattu wajen karatun duniyar lokacinsu. Idan aka sake sa natsuwa, za a ga duk wata dabara, da fasaha, da kimiyyar lokacinmu, karin maganganunmu sun da]e da }yallaro su, tun ba mu kasance a duniya ba. Don haka nake son kalato wasu sassa na karin magana da suka yi zuzzurfan karatun bincike, da ]ora mai bincike kan tafarkin da ya kamata ya bi, ya kai ga nasarar kowane irin bincike yake }udurin yi. Tunanin masu ganin a yi dai mu gani, da masu fa]ar: “anya!”, Da masu yi wa adabinmu kallon hadarin kaji, ya sa na yi wa binciken take: “Ruwa na }asa sai ga wanda bai tona ba”.

Kadabar Bincike

[alibin ilmi zai so ya ji ina ne iyakokin wannan tunani? Domin sanin farfajiyar karin magana yawa gare ta. To! Ba kwasan karan mahaukaciya zan yi wa karin  magana ba, ba kuma salon za~i son ka zan yi ba. Duk wani karin magana da bincike ke iya kasancewa babban jigonsa ire-irensu ne zan kalato. Ban ke~e wa zamani, ko rabe-raben karin magana, wani fasali mai cin gashin kansa ba, domin wani fage ne da ake son a yi wa kadada cikin farfajiyarsa. Ba tare da rarrabewa ba, za a tsintsinto karin magana da ke da }unshiyar bincike, na kowane mataki na bincike, a yi fashin ba}insa, a ga hasken da ya bai wa masana da ]aliban ilmi na bincike. Kadadar wannan bincike ta farko ita ce, karin magana. Kadada ta biyu, karin maganar da ke da }unshiyar bincike na kowane mataki. Kadada ta uku, ya kasance karin magana gama-gari da ya da]e cikin kunnuwan Hausawa da suka taras kaka da kakani.

Mene ne karin Magana?

Bisa ga tsarin fashin ba}in, ‘ba ni ba}i in ba ka fassara’, za mu ce, karin magana, kalmomi biyu ne ]aya ta goyo ]aya suka kasance kalma ]aya. Za a ce, magana ce da aka kakkarya ko aka dun}ule aka ta}aita ta domin adana ko isar da wani sa}o. Wannan ne dalilin magabata da ke ce wa karin maga gajeruwar jimla mai }unshe da babban sa}o (Galadanci, 1975, Kiyawa: 1980 Bada, 1995, Furnis, 1996, da [anyaya, 2017). Ban }i su ba, amma na so in ji, wa ke }ago jimlolin? Mene ne }unshiyarsu? Me za a taras ciki a ce musu karin magana? A ]an nawa bincike na gano “}wararrun magabata” ke }ago jimlolin. {unshiyar jimlolin wani karatun hikima ne na fannoni daban-daban na rayuwa. Matu}ar ba a samu }ololuwar tunanin hikima wanda ya yi canjaras da gaskiyar rayuwa ba; ba zai kasance karin magana ba. An ce, cikin }ira aka da]i, don haka nake ganin:

Karin magana gajeruwar jimla ce da magabata }wararru a fannonin rayuwa daban-daban, gogaggu ga sanin jiya da yau, wayayyu ga rayuwar zamunansu suka }ir}iro. Za a samu jimlolin }wangaggu ga nahawunsu, tare da hikimomin gagara misali wa]anda ba sa musantuwa ga wanda suka taras kuma babu zamanin da zai wofintar da su.

 


 

Mene ne Bincike

Bincike a matsayinta na kalma tana da fassarori da lafuzan furucinta daban-daban a karuruwan harshen Hausa, (Bunza 2017:2). A fagen nazarin ilmi kalmar da ta shahara ga fashin ba}in bincike ita ce: “Research” kalmar “research” tana da ]agwarin “re”. Idan aka cire ]agwari sai ta koma “search”. To! Idan kalmar “search” ita ce, “bincike” a Hausa. Kalmar “research” tana ]aukar ma’anonin; tottoniya, tone-tone, sake bita, mayar da gani, sake lisafi, kokkomawa, sake lale, ga su nan dai. A wajen Bahaushe:

Bincike na ]aukar ma’anar biyar abi daki-daki, da nufin gano wani abu da aka sani, ko ba a sani ba, ko ake son a }ir}iro, ko ake son a sake wa fasali. Sai an kammala bincike ake yin tottoniyar sake bita domin a mayar da ganin da ake son a yi wa wata matsaya muhimmiya a kai.

 

A yau, dukkanin harkokin cigaban duniya na ilmi na kowane fanni ga bincike ya dogara. Masana koyaushe kan bincike suke domin fito da wani abu sabo, ]aliban ilmi koyaushe a kan bincike suke domin gano wani abu sabo. Ke nan, bincike ya kasance na kowa, don haka yake da darasi mai cin gashin kansa a kowane fannin ilmi. Don haka nake son in }yallaro; shin kafin a haifi uwar mai sabulu yaya belbela take? Tana da farinta? Ko sai da ta yi wanka da sabulun? Idan da farinta aka taras da ita, to mai sabulu ta rage kuri, da doro, da kirari, ko mahaifiyarta haka ta taras da belbela fara tas!

Hanyar [ora Bincike

Kalmomin matashiyar bincike babu sabon abu a ciki, amma ƙudurin binciken sabo ne a farfajiyar karin magana. Na ]ora wannan bincike a kan tunanin Bahaushe da ke cewa: “Rashin sani ya fi dare duhu.” Abin da duk Bahaushe bai hango ba za a ji shi yana cewa: “Abu kaza ya shige mini duhu. Duhun shi ne “rashin sani”. Rashin sani babban duhu ne domin shi ne ya sa karen gwauro ya kori bazawara. Da ta san karensu ne, me zai wahalar da ita da ti}a gudu? Idan za a tuna, rashin sanin shi ya sa kaza ta kwana a kan dami da yunwa. Da ta san kan dami (in gero/dawa/maiwa) take, ai da komai ya yi, an ba gwauro ajiyar mata. Da ]aliban ilmi sun fahimci sirrin da ke cikin karin magananmu na bincike; da sun huta da kama-kamen ra’o’in da ba su kai masu su ganga ba, bale su fitar da wanda ke tsakiyar kogi. Wannan bincike a kan haka zai tafi, yana yi yana hango ma}asudinsu bisa ga hanyar da aka ]ora shi.

Kayan Aiki

 Babu aikin da zai kai ga nasarar ma}asudinsa ba tare da an tanada masa nagartattun kayan aiki ba. Kayan aikin da na tanada wa wannan bincike su ne:

ü Fitattun karin maganar da suka gabata masu jigon bincike

ü Sababbin karin maganar da zamani ya haifar masu jigon bincike

ü Karuruwan magana }wararru a fitattun sana’o’in gargajiya

ü Karuruwan magana da ke da ala}a da fasahohin Bahaushe

ü Wasu labarai na ha}i}a ko }agaggu da ke tabbatar da }unshiyar karin magana masu }unshiyar bincike

ü Matakan bincike daga masana bincike da suka yi canjaras da karin maganar bincike

ü Wasu sassan adabin baka da ke fashin ba}in karin maganar da suka shafi bincike.


 

Dabarun Bincike

Kayan aikin da aka tanada akwai dabarun da aka bi wajen tantance su, da nazarin su, da taskace su, a rubuce:

i.            Na farko, an yi }o}arin samo wasu ayyukan ilmi da aka yi kan karin magana musamman kundayen binciken samun wata takardar shaidar samun wata daraja ta karatun Hausa, ko wani fanni da aka yi garkuwa da karin maganar Hausa.

ii.            An tunkari ayyukan da suka ke~anta na }amusoshi na karin magana na Hausa domin }yallaro fashin ba}insu.

iii.            Ba a yi ko oho da mu}alu da mujallun da aka gabatar ko aka wallafa ba. An yi amfani da su sosai.

iv.            An ce, zamani riga, don haka aka shiga rigar Intanet, da Kib]au, da Wasap, da kafafen sada zumunta, domin farautar abin da za a nazarta.

v.            An samu tattaunawa da wasu masana adabi, da ]aliban ilmin adabi, da na Hausa gaba ]aya, domin samun gudunmuwarsu.

vi.            An mayar da hankali ga wasu fitattun ayyukan da aka yi a kan Dabarun bincike cikin harshen Hausa da Ingilishi, da ke tafiya da duniyar binciken wannan }arni, domin a dace da abubuwan da ake son a tabbatar na gudunmuwar Bahaushen karin magana.

vii.            An yi duba cikin ayyukan da aka yi kan karin magana a Ingilishi, da Igbo, da Yoruba, da Larabci, domin rage wa aikin tsawo idan ya yi canjaras da wani/wasu daga ciki. Rashin samun haka, ya ba da }arfin guiwa na cewa, a matsa gina, ruwa na }asa sai ga wanda bai tona ba.

Sai an San Nauyin Kaya Ake Jingar Daukar Su

A tunanin karin magana, wajibi ne ga mai bincike ya tsaya, ya san me yake son ya yi bincike? Tun gabanin a yanke shawarar bincike a kula da shirin shiga ruwa tun daga tudu ake fara shi. A tuna da tunanin Bahaushe da ke cewa, da muguwar rawa gara }in tashi. Shin fagen da za a yi bincike sabo ne, ko tsoho ne? In sabo ne, a yi shawara da magaba, babbar yatsa ko ba ta cin tuwo ta iya ~are malmala. In kuwa an ta~a bincike mai kama da shi, ga na gaba ake gane zurfin ruwa. A tabbata }udurin binciken akwai wadataccen }wazo na fuskantar matsalolin da za a tunkara a ciki, kada a yi rowarsa abin ya kasance gara jiya da yau. Haka kuma, kada a bu]e gaba da yawa, a yi kwasan karan mahaukaciya, ko shifcin Gizo, domin Wazirin Gwandu Malam Umaru Nasarawa ya ce:

Komi kakai kai dai bi]o daidai da kai,

Kwa] ]auki kaya sun fi }arfinai ga kai,

Yaf fara hanya tabbata mishi ba ya kai,

Tafiya ka]an na shi kai shi ]ora ta}ai-ta}ai,

Ko dai shi yas, koko shi fa]i su hau shi

 

Kowa da Bukin Zuciyarsa Ma}wabcin Mai Akuya ya Sayo Kura

Ka da mai bincike ya ru]u da ruɗar da wasu ke yi wa fagen nazarinsu na kirari, ya kula da cewa, kowane bakin wuta da irin nasa haya}i. Fannonin ilmi ba hanjin jimina ba ne, da za a ce, akwai na ci akwai na zubarwa, jejjere suke tafiya kamar kashin awaki. Abin da kake sha’awa shi za ka yi bugun gaba da shi, ya kasance, zakaranka ra}uminka. Sai akwai sha’awa, da so, }wazon mai }wazo zai bayyana, domin an ce, dama ka damun dawo in babu dama ana dama shi gaya.A a}idar bincike, kowane allazi da nasa amanu domin bakin wani ba ya su]e wa hannun wani miya. Sha’awarka ta jagoranci za~en fagen nazarinka, shi ka]ai zai ba ka damar fito da wani abu a yi madalla da cewa, ka fitar da suhe wuta. Masana na cewa, bincike tuwo ne kowa ya ]ebo da zafi bakinsa. Binciken ilmi sha’awar mai shi ka sa shi nacewa har ya fito da wani abu sabo, ba a ja ta haka nan ba. Sha’awa ke ba da tazarar }a}ale, da }ara wa Borno dawaki, a sihirce tunanin mai karatu, abin da ya riga ya sani ya ganshi cikin wata sigar da bai zata ba. Dubi yadda maka]a Sani [anbol]o Waramu ya fito da sha’awarsa ta noma:

Jagora:       Kun san layun tsari gare ni,

          :        Mi al layun tsarin ka Mamman?

          :        Dun}ullan dawo gami da nono,

          :        Ko wassha su ba shi jin kasala,

          :        In ko an yi gardama a dama,

          :        Rabbana Allah Ka taimake mu,

          :        Mu samu fitak kai cikin tukunya.

 

Wuyar Aiki Ba a Fara ba

Bayan za~en fagen bincike da samun sha’awa a kansa, masana bincike sun ce, samun taken bincike shi ne rage zango, mai zuwa sama ya taki faifai. Nagartaccen take shi ake ce wa, abin nema ya samu matar Mallam ta haifi allo. Raggon take na nan zamansa na ba a yi komai ba an raki ba}o ya dawo. Gina take a kan raddi sunansa “ba ta mutu ba ta ɓalkace. [ora shi a kan tambaya, zai kasance “ba cinya ba }afar baya”. Kurakuran nahawu ga take ya zama “Koya sa}a da mugun zare”. Dole a yi wa take kadada, ka da ya kasance daji ba ka da gambu. An so }walailaice kadadar take ya zamo nashin }asa babu kure. A yun}urin }walailaice kadadar take, a kula da abu biyu: Mai ɗaki ]ai shi ya san gefen da yake tarara, duk da haka, mai baibaya, ya san gefen da ya toshe matararar ruwa. Ka da a yarda taken aiki ya yi takin sa}a da }unshiya, ita kuwa }unshiya, ka da ta yi wa take reto, bu}ata su kasance, tangam mai zuwa hajji ya gamu da Annabi (SAW). A fagen bincike, take shi ne fuskar aiki, fuska kuwa ita ke sayar da riga. Take shi ne uban wa}a, sauran babuka da fasula ‘yan amshi ne wani ba shi yi sai da wani. Idan tsakanin take da }unshiya kumbu ya gamu da marufi, abin da duk zai biyo baya cikon sunna ne makaho da waiwaya. Take da }unshiya tafiyar Buzu da ru}umi suke yi, idan suka yi bambarkwai, an yanka ta shi, domin maka]a Sani Aliyu [andawo cewa ya yi:

Jagora:       An ce kowag ga raƙumi shi ga Buzu ga,

          :        Ra}umi cikin daji.

Yara:          Amma ga shi ban ga Buzu ba.

Gindi:         Shehu sauran mazan hwarko,

         :          Mu zo Gwambe in gano Sarki.

 

Sanin Wurin Bugu shi ne {ira

Hausawa sun tabbatar da cewa, abin da duk wayo ya ~oye hankali na gano shi. A al’adance, hankali ka gani ba ido. Mai bincike bi]ar wani abu yake yi, an ko ce mai bi]a ya bar jin gajiya. Dagewa ga mai bincike dole ne domin mai nema yana tare da samu. Jajircewa ga bincike wani babban makamin dacewa ne, domin mai ha}uri yakan dafa dutse in mai izan wuta ya jure. Ba a yanke }auna ga rashin kai ga bu}ata ko da an kai {aura Wambai saboda ko bayan tiya akwai wata caca. Sanin wurin da za a bincike kamar ganin maciji ne a huta da biyar sawunsa. Idan mai ginan ramin abu ya kai ga wutsiyarsa, kada ya sake jiki sai ya kai ga kansa, ya ri}a hannunsa, sanin cewa ganin Dala ba shiga birni ba. Abin da ake nufi da bincike ha}a ta kai ga wadataccen ruwa. A matsakaiciyar fassara in ta yi ruwa rijiya, in ba ta yi ba masai. Babu laifi idan ruwanka ba su isa wanka ba ka yi alwala a ci gaba da tafiya. An fi da son mai bincike ya kasance ganau ba jiyau ba, in yana matakin jiyau ya matsa }aimi sai hankaka da mai aya sun gana, a fassarar maka]a [ansani Dabere Bunza:

Jagora:        Hankaka mai aya an gana,

Yara:          Kura tai karo da garken jakkai

Gindi:         Yau da borin goje kana da borin tashe

 

Ba a san Tafkin da ke Makara da Ruwa ba

A }a’idar bincike, ba a rena hujja, ko wata dama komai }an}antarta. Magabata sun ce, idan ra}uminka ya ~ata ko cikin akurki ka le}a domin da rashin tayi akan bar arha. Da yawa ana zaton wuta a ma}era ba a samu ba, a same ta a masa}a. Tsintuwar dami a kala ba mawuyancin abu ba ne, adabi ya tabbatar da shi, kamar yadda ya tabbatar da zomo ba ya kamuwa daga zaune. Ba a rena hujja komai }an}antarta a bincike, sau nawa }ilu ke jawo balau? Ai ]an hakin da ka raina shi ke tsone maka ido. Tottoniya na son a fe]e biri har wutsiya har sai an ga abin da ya kwance wa Buzu na]i yadda maka]a Bage [ansala Argungu ke cewa:

Jagora:       An ce Buzu inda duk yake,

          :        Yay yi na]i bai walwale shi ba,

          :        Ranar bara da za ni Yawuri

Yara:          Na ishe Buzu za shi yin ji}o,

:        Duk rawani nai ya zube }asa.

Gindi:         A ci dai ba don a }oshi ba,

:        Garin kwaki ya yi taimaka

 

Yawon rangadin gani da ido ya ba Bage [ansala cin nasarar ganin abin da ya ture wa Buzu na]i.

Da Haka Muka Fara Kuturu ya ga mai {yasfi

Kome ake son a yi bincike a ri}a kulawa da mafarinsa, ko musabbabinsa, ko tushensa, saboda wurin da an ka hau ice (itaciya/bushiya) duk nan ake sauƙa. Ga alamu ko mafarin abin da ake son a yi bincike wata ƙofa ce da za a bi cikin natsuwa domin ba banza ba }uda a warki. Samun tabbacin }uda ba su bin mai kayan gawai shi zai ba mu damar tambayar in babu }ira me ya ci gawai? Muradin bincike shi ne, lura da ba}on abu da yadda ya sa~a da al’adarsa domin masana sun ce, tsuyen da ka zama gwaiwa tun yana }arami ake ganewa. In ana binciken ilmi, duk wani abu aka ci karo da shi mai ala}a da abin da ake nema adana shi ake yi bisa ga riwayar Dakarkari da ke cewa, mai ginan ~era ya tono wutsiyar maciji ya yi sa’a babba. Mai bincike a kan maka]an Hausa ya ci karo da masassa}in ganga an ta}aita masa jewa]i. Da an ankara da mafarin abin da ake son a yi bincike, shi za a tunkara gadan-gadan domin Maka]a Gambo Fagada ya ce:

 

Jagora:       Halin duniya na ba ni tsoro,

          :        Wai ga maciji ana ta biyat shayi da sanda,

          :        To! Ga ~arayi

          :        Shin mit bi]i mai wa}ar barayi?

 

A dai sa himma, in an ga hanya gida ta nufa, domin komai nisan dawa da karkara kusa.

In ba ka san Gari ba Saurari Daka

Daga cikin nagartattun dabarun bincike akwai share fagensa da binciken ayyukan da suka gabata a matakai daban-daban. Mai bincike a koyaushe kunnuwansa a bu]e suke na sauraron tsegumi, jita-jita, ra]a, baa, gaskiya da }arya, }aramar magana da babba a gunsa duk sunansu magana bincikensa zai tabbata zubinsu da tsarinsu. Magabata sun tabbatar da matambayi ba ya ~ata, domin ita tambaya mabu]in ilmi ce. Mai bincike mai neman sanin gari ne, Hausawa ko sun ce, da ]an gari akan ci gari. Bu}atar ]an gari ga garin da za a kai wa harin ya}i wata kinaya ce na mai bincike ya san da cewa, hannu ]aya ba ya ]aukar jinka. Tunanin Bahaushe na fa]ar kashin ba}i sai taro, wata fassara ce ta hannu da yawa maganin miya yamamma. Idan aka yi wa bincike taron dangi ya fi tsafta da ku~uta ga manyan kurakurai. Saka mataimaka a fannonin bincike daban-daban zai bu]e wa mai bincike }wa}}afin da zai fito wa aikinsa mabambanta da za su ba shi damar sanin hanyoyin da zai bi. Tamkar yadda maka]a Dr. Ibrahim Naramba]a ke cewa:

Jagora:       Ah! Ji wanda bai san hanya ba,

:        Ya yi sabko,

:        Amma fa ya ~ace ya dawo.

Yara:          Ila da yat tahi bai ]ora tambayar kowa ba,

Gindi:         Ginshimin Haliru Uban zagi na Malam Isa

          :        Gagarun jikan Shehu Iro mai Shanawa.

 

Tafiya da Waiwaya Tana Maganin Mantuwa

Babu shakka tafiya da waiwaya ba mantuwa kawai take magani ba, har makuwa tana magani. Bitar ayyukan da suka gabata su ake nufi da a ri}a sara ana duban bakin gatari. Komai }asurar masani da ]alibin ilmi sai da ya dafi kafa]ar wani aka ga tsawonsa. Muradin bita tabbatar da gaba da gabanta, Muradin babu wanda ya koyar da kansa masana sun ce, da koyo akan iya. Sanin cewa, kama da wane ba wane ba ne, ake son kowane bakin wuta a fayyace irin nasa haya}i. Komai }an}antar aiki a mutunta shi domin du}a wa Wada ba ya hana a tashi da tsawo. Idan mai bincike ya kiyaye da, ga na gaba ake gane zurfin ruwa, a wajen bita ya sani cewa, cikin }ira ake ɗa]i. Mai bita mai fa]a]en kama wani abu ne, Hausawa sun ce, mai fa]a]e ba ya tayar da hannuwansa sama. Manufar bita tanka]e da rairaya, ba komai ake kwashewa ba, ba komai ake zubarwa ba, dole a kasance ido ga kifi, ido ga bado. A farautar kayan aikin bita ba a cewa, komai lauje ya kamo haki ne, kuma tilas a nisanci kirarin matsoraci. Ga fashin ba}in bita a bakandamiyar Dr. Ibrahim Naramba]a:

Jagra:           Na jiya [andawo.

Yara:           Ya yi tai uwar wa}a sai nai tau.

Jagora:       Na jiya Akwara.

Yara:          Ya yi tai uwar wa}a sai nai tau.

Jagora:       Na jiya Gurso.

Yara:          Ya yi tai uwar wa}a sai nai tau.

Jagora:       Na jiya Janki]i.

Yara:          Ya yi tai uwar wa}a sai nai tau.

Jagora:       Ai tun da Nagaya.

Yara:          Ya yi tai uwar wa}a sai nai tau.

Jagora:       Dodo Malamin Wa}a Kundumi Magajin [an~aidu.

Yara:          Ya yi tai uwar wa}a sai nai tau.

 

Dr. Naramba]a ya yi adalci ambaton magabatan da suka riga shi }aga bakandamiya (uwar wa}a), kuma babu shakka ya ji su, ya saurare su. Kan haka yake son ya }ago tasa sabuwa bayan bitar da ya yi na wa}o}i irin ta.

In an ga ta |arawo a Dubi ta Mai Kaya

Mai bincike al}ali ne, dole ya ri}a sara yana duban bakin gatari. Babu hujja ko maganar da ba ta da muhimmanci gare shi, sai wadda ta kasa tsayi da }afafunta. Idan ya gano laifin ~arawo na sata, to ya binciki ina ne mai kaya ya ajiye kayansa da aka sata? In aka tabbatar da in ~era da sata ko daddawa da wari, nan za a gano matakan hana wa ~era sata, da dabarun rage kaifin warin daddawa. Tilas bincike ya kasance bugi sa bugi taiki, ta haka ka]ai za a tantance hasashen, ba ni na kashe zomo ba rataya aka ba ni. Tunanin zama da ma]auki kanwa shi ke kawo farin kai ke hana mai bincike yi wa hujjoji bugun goro. Faɗar Bahaushe da ke cewa, ko Kwara tana da tsibiri dogon karatu ne mai rusa gajeren tunani, domin ba dole ne mai kamar maza ka maza ba. Nagartaccen bincike bai ta~a yanka ta tashi ba domin ba zai rage tazarar a sake lale ba. Bu}ata dai binciken ilmi ya kasance raba gardama kamar yadda Alhaji Mamman Gawo Filinge ya yi da ‘yan amshinsa na kore zargin matsegunta inda ya ce:

Jagora:       Kura cikin garken rago,

          :        Ko sau ]aya ba ta fasa garken ba,

          :        In ta ta~a ku hwa]i ga ku?

Yara  :        A’a Malam ba ta kutsa ba.

Jagora:       Haka nika tammaha!

Gindi:         Ya Allah gyara,

          :        Wahabu Ka taimaki ‘yan Nijar.

 

Bu}atar Dara a Kasa

A koyaushe aka ]ora harsashen tottoniya wani abu ake son a gano sabo, ko wanda ya ~ata, ko wanda ake ta}addama a kansa. Buƙata ka da aiki ya kasance jita-jita hadisin Bamaguje, ka da a yarda ya zamo labarin }anzon kurege. Dole akwai abin da ka gano cikin jewa]in da aka yi na bincike ka da ya kasance shigan }adangare Shantu. Tabbatar da binciken wasu kirarin matsoraci ne, ba bincike ba ne. Kushe kowa ba karatu ba ne, ko da an ga kuskure ba a rama gayya da hushi. Ana son a ji, shin ya~i ne ka yi wa katangar ko yaso ne ka yi wa rijiyar. To me ya sa ka yi haka? Le}o sabo ko wace kafa ka toshe? Matu}ar ba a gano komai ba, to, ba a binciko komai ba. In ta tabbata haka, aikin ya zama aikin banza yi wa kare wanka. Binciken duk da ba ya da sakamako an yi sammakon banza domin da mugunyar rawa gara }in tashi. Maka]a Dr. Ibrahim Naramba]a ya ce:

Jagora:       Shin kowag ga wuta

          :        An ka ce a ]ebo wa ka zuwa?

Yara:          Wanda yag gani ka zuwa,

          :        Kowas shaida shi ka shan rana,

          :        In bai tai ba yai batun banza,

          :        Ko can yanzu shi batun banza,

          :        Da]in hwa]i garai.

Gindi:         Ya ci maza, ya kwan shina shire,

          :        Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.

 

Wanda ya ce ya ga wuta bai ]ebo ta ba, ya yi }arya, haka nan wanda ya ce, zai yi binciken abu bai ba da sakamakonsa ba yake.

Shirin Shiga Ruwa Tun Tudu Ake Kimtsa Shi

Idan an daidaita a kan matashiyar da za a ]ora aiki a kai, a tabbatar da an yi wa fitilun kalmominta mazarin in til, in ƙwal, rinin mahaukaciya. A yi wa kalmomin matashiya zubi biyu. Akwai fitilun kalmomin gina aiki wa]anda a kansu aiki zai tsayu, su za a yi wa twa-da-twa wankin ]an Kanoma mashaya. Duk wani abin da ya shafe su a nagartar da fayyace shi da gawurtattun hujjoji. Ka da a bari su yi canjaras da aikin kowa domin kauce zurmugu]]u. Idan aro kalmomin aka yi a nuna ma}aginsu. A tabbata ba kai ka kashe zomo ba, rataya aka ba ka. Sauran kalmomi ‘yan rakiya, in sai da su zuciyar aikin za ta tabbata dole a ware musu babin kansu domin ya zama gadon fe]e aiki irin aikin sitari da tayoyi ga mota, ko direba bai so ba wurin da suka dosa can mota ta nufa. Idan nahawun kalmomin matashiya ya diaidaitu, shi zai yi wa }unshiyar aiki “ki]a” shi kuwa aikin yai “amshi” daidai da kalmomin da aka girka shi a kai. Hausawa sun ce, in kifi ya tashi lalacewa ga kai yake ru~ewa. Da an samu matsala ga marshiyar aiki ba ta da filin gyara mai neman beli ya mari uwar Al}ali. Sake wa matashiya tsari kasawar bincike ne, cirata daga gare ta zuwa ga wata ya nuna tsuntsun da ya kirai ruwa, ruwa sun ci shi. {udurin shiga bincike irin na shirin shiga ruwa ne ga masunci ko fagen artabu ga maya}i. Aliyu Dandawo a wa}ar Sarkin Kabi Sama ya ba mu shawarar shirin fuskantar ya}i da cewa:

Jagora:       In tahiya ta tashi,

:        Ka sa a shirya dawaki,

:        A ]aura damman masu,

:        Ko suna taya fansa,

:        A tabbata wa maza,

:        Ba a girsuwar mai }arfi.

Yara  :        A yanzu wa am madadin Mainasara ba kai ba?

:        Shugaban tahiya Sarkin Kabi mai Sudani,

:        Ila marin rugga ]an Ya}uba sa gurfani.

 

Idan ba a shirya kayan farauto hujjojin bincike ba, matashiyar aiki ba ta zama da gindinta. Idan matashiya ba ta tsaya a kan }afafunta ba, ba a yi komai ba an raki ba}o ya dawo.

Sakamakon Bincike

    Hausawa na da ra’ayin cewa, ~eran gida ba ya da mai. Duk al’ummar da aka yi wa mulkin mallaka na ci da }arfi a }ar}ashin kowace a}ida, ko addini, sai an rusa musu kyawawan ]abi’unsu an cusa musu na ba}in haure. A tsarin ilmin boko, Turawa sun yi tsaye ga kore duk wani ilmi da ba su zo da shi ba a matsayin ilmin gargajiya. To, su nasu da suka gada kaka da kakaninsu na mene ne? Ba dai za a a kira shi ilmin zamani ba, domin an yi shi tun gabanin zamunansu? Wannan ]an bincike nawa ya ]an ba mu haske kan abubuwa uku:

1.     Duk wata dabara da za a bi ta binciken kimiyya, ko fasaha ko wani ilmi na ko mene ne, idan aka sa adabin karin maganan Hausa gaba za a samu sirrin gudanar da shi.

2.     Da za mu sa natsuwa sosai a cikin karin maganan Hausa ka]ai za mu iya }ir}iro ra’o’in bincike da yawa mu huta da kwashe-kwashen ra’o’in da ba su yi canjaras da tunanin magabatanmu }wararru ba.

3.     Karin magana taron dangin masana ne da }wararru a fannoni daban-daban, don haka hannu da yawa ne an ko ce, yana maganin miya yamamma.

4.     Karin magana daji ne ba ka da gambu. Babu abin da ke }ar}ashin gizagizan sararin Subhana da bai ta~o ba. Ilmin bincike wani ]an leza ne daga cikin dakakin ilmi, idan har an samu rassansa da karin magana ya kakkamo, to a matsa }aimin bincike, da wuya a samu fannin da bai ta~o ba.

5.     A }arshe, za mu ga cewa, duk wani aikin bincike na ilmukkan karatun Hausa, idan ba a gayyato karin magana ba ko an yanka tana tashi. Idan an yi ko oho da karin magana, ba za a samu nagartaccen sakamako ba.

 

Na]ewa

Ilmi daga cikin al’adun mutane aka }ago shi babu al’ummar da aka yi wa wahayin yadda za ta tunkari abubuwan da ke yi mata barazana sai dai ta taras da su cikin al’adunta. Wanda duk aka sa ya wofintar da al’adarsa ya ]auki na wasu an toshe masa }ofofin bun}asa tunaninsa. A duban wannan ]an bincike, akwai alamar cewa, lallai mulkin mallaka ya yi tasiri ga zukatan ‘yan boko musamman wa]anda karatun Hausa ya rufa wa asiri suka dawo suna ya}i da shi. An sihirce musu }wa}walwa har suna ganin babu wani cigaba ga ilmi in ba Ingilishi aka ]auka tafarkin ilmi ba. Wannan ta sa, aka manta da irin taskokin hikima da wayo, da ilmi, da fasaha, da kimiyyar da ke cikin karin maganar Hausa; har wasu suka soma salwanta ba a adana su ba. Ya kyauta a ce, mun fara rarraba karin magana cikin kowane fanni na karatun Hausa ya jagoranci bincike-binciken da ake son a yi a fannin. Kowa a ka rinjaya ga kiyaye karin magana an fi shi wayo da sanin dabarun zaman duniya. Don haka a cikin koyar da dabarun bincike a kula da “Taskar karin Magana”.

 

Ratayen Karin Maganar  da Aka Sarrfa

 

1.                 A ri}a sara ana duban bakin gatari.

2.                 A yi dai mu gani.

3.                 Abin da wayo ya ~oye, hankali ke gano shi.

4.                 Abin nema ya samu, matar Malam ta haifi allo.

5.                 Aikin banza yi wa kare wanka.

6.                 An koya sa}a da mugun zare.

7.                 An nemi wuta ma}era an rasa, an je masa}a aka samu.

8.                 An rage zango mai zuwa sama ya taka faifai.

9.                 An yanka ta tashi.

10.             Ana cikin gina ga wutsiya.

11.             Ba a rama gayya da hushi.

12.             Ba a san maci tuwo ba sai miya ta }are.

13.             Ba a san tabkin da ka makara da ruwa ba.

14.             Ba a yi komai ba, an raki ba}o ya dawo.

15.             Ba banza ba, }uda a warki.

16.             Ba cinya ba }afar baya.

17.             Ba mai kamar maza ka maza ba.

18.             Ba ni na kashe zomo ba, rataya aka ba ni.

19.             Ba ta da filin gyara, mai neman beli ya mari uwar Alkali

20.             Ba ta mutu ba ta ɓalkace.

21.            Babbar yatsa ko ba ta cin tuwo ta iya ~are malmala.

22.             Bakin wani ba ya su]e wa hannun wani miya.

23.             Ban sani ba, ta raba ni da kowa.

24.             |eran gida ba ya da mai.

25.             Bu}atar dara a kasa.

26.             Bugi sa bugi taiki.

27.             Bugun goro.

28.            Cikin }ira aka ɗa]i.

29.             Cikon sunna, makaho da waiwaya.

30.             [an hakin da ka raina, shi zai tsone maka ido.

31.             Da ]an gari akan ci gari.

32.             Da gina sabuwar rijiya gara yaso.

33.             Da haka muka fara, kuturu ya ga mai }yasfi.

34.             Da koyo akan iya.

35.            Da mugunyar rawa gara }in tashi.

36.             Da sabuwar katanga gara ya~i.

37.             Daji ba ka da gambu.

38.             Dama ka damun dawo, in babu dama ana dama shi gaya.

39.             Du}a wa Wada ba ya hana ka tashi da tsawonka.

40.             Fe]e biri har wutsiya.

41.             Fitar da suhe wuta.

42.             Fuska ke sayar da riga.

43.             Ga maciji ana biyar shayi da sanda.

44.            Ga na gaba ake gane zurfin ruwa.

45.             Gaba da gabanta.

46.             Ganin Dala ba shiga birin ba.

47.             Ganau nike ba jiyau ba.

48.            Gara jiya da yau.

49.             Ha}a ta kai ga ruwa.

50.             Hanjin jimina akwai na ci, akwai na zubarwa.

51.             Hankali ka gani ba ido ba.

52.             Hannu ]aya ba ya ]aukar jinka.

53.             Idan ra}uminka ya ~ata ko cikin akurki ka le}a.

54.             Ido ga kifi, ido ga bado.

55.             In an bi daga-daga na }urya ya sha kashi.

56.             In an ga hanya gida ta nufa.

57.             In an ga ta ~arawo a dubi na mai kaya.

58.             In ba ka san gari ba saurari daka.

59.             In babu }ira me ya ci gawai?

60.             In |era da sata ko daddawa da wari

61.             In da fata ta fi laushi nan ake mayar da jima.

62.             In ka ji namu da mai shi.

63.             In kifi ya tashi lalacewa, ga kai yake ru~ewa.

64.             In ruwanka ba su ishe ka wanka ba, ka yi alwala.

65.             In ta yi ruwa rijiya, in ba ta yi ba masai.

66.             In til, in ƙwal, rinin mahaukaciya.

67.             Jejjere kamar kashin awaki.

68.             Jita-jita hadisin Bamaguje.

69.            Kallon hadarin kaji.

70.             Kama da wane, ba wane ba ne.

71.             Kashin ba}i sai taro.

72.             {ara wa Borno dawaki.

73.             {aramin sani }u}umi ne.

74.             {aura Wambai.

75.             {ilau! Ya jawo balau!

76.             Ko bayan tiya akwai wata caca.

77.             Ko Kwara tana da tsibiri.

78.            Komai ya yi, an ba gwauro ajiyar mata.

79.             Komi lauje ya kamo haki ne.

80.             Komi nisan dawa da karkara kusa.

81.            Kowa da bukin zuciyarsa, ma}wabcin mai akuya ya sai kura

82.             Kowa ya ]ebo da zafi bakinsa.

83.             Kowa ya ga ra}umi ya ga Buzu.

84.             Kowane allazi da nasa amanu.

85.             Kowane bakin wuta da irin nasa haya}i.

86.            {uda ba su bin mai kayan gawai.

87.            Ko kamin a haifi uwar mai sabulu belbela tana da farinta.

88.             Kumbu ya gamu da marufi.

89.            Kwasan karan mahaukaciya.

90.             Labarin }anzon kurege.

91.             Magani sai da bi]a.

92.             Mai bi]a ya bar jin gajiya.

93.             Mai ]aki shi ya san gefen da yake tarara.

94.             Mai fa]a]e ba ya tayar da hannunsa sama.

95.             Mai ginan ~era ya gamu da maciji ya yi sa’a babba.

96.             Mai ha}uri yakan dafa dutse, in mai izan wuta ya jure.

97.             Mai nema yana tare da samu.

98.             Matambayi ba ya ~ata.

99.             Na babban mahaukaci, “duk duniya”.

100.        Nashin }asa babu kure.

101.       Rashin sani karen gwauro ya kori bazaura.

102.       Rashin sani, kaza ta kwana kan dami da yunwa.

103.       Rashin sani ya fi dare duhu.

104.       Ruwa na }asa sai ga wanda bai tona ba.

105.        Sai an ga abin da ya ture wa Buzu na]i.

106.       Sai an san nauyin kaya ake jingar ]aukar su.

107.        Sanin gari.

108.        Sanin wurin bugu shi ne }ira.

109.       Shifcin gizo.

110.        Shigan shantun }adangare.

111.       Shirin shiga ruwa tun tudu ake fara shi.

112.        Tafiya da waiwaya tana maganin mantuwa.

113.        Tambaya mabu]in ilmi.

114.        Tangam! Mai zuwa Haji ya gamu da Annabi (SAW).

115.        Tsintuwar dami a kala.

116.        Tsuntsun da ya kirai ruwa, ruwa sun ci shi.

117.        Tsuyen da ke zama gwaiwa tun yana }arami ake ganewa.

118.        Twa-da-twa wankin ]an kanoma mashaya.

119.        Wada duk ka ce, haka na ce kirarin matsoraci.

120.        Wurin da aka hau ice nan ake sauka.

121.        Wuyar aiki ba a fara ba.

122.        Zakaranka ra}uminka.

123.        Zama da ma]aukin kanwa, shi kan kawo farin kai.

124.       Zamani riga.

125.        Zomo ba ya kamuwa daga zaune.

Manazarta

 

Bunza, A. M. (2006).  Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Publications    Limited.

 

Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Al-Ibrash Publication Plc.

 

Bunza, A. M. (2017) Dabarun Bincike: (A Nazarin Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa).Tetfund Publications, Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya (1981). Rayuwar Hausawa. Lagos: Thomas Nelson (Nigeria)Limited.

 

Ɗangambo, A. (1984). Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa   ga Rayuwar Hausawa. Kano: Maɗaba’ar Triumph, Gidan Sa’adu   Zungur.

 

Ɗangambo, A. (2008). Rabe-raben Adabin Hausa (Sabon Tsari). Zaria: Amana Publishers Limited.

 

Fennegan, R. (1970). Oral Literature In Africa. London: Oxford   University Press.

 

Furniss, G. (1996). Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa,
      International African Library Edinburgh: Edinburgh University        Press,Ltd.

Green, K. (1966). Hausa Ba Dabo Ba Ne. London: Oxford University    Press.

 

Koko, H. S. (2011). Hausa Cikin Hausa. ISBN. 978-978-919-267-0.

 

Madauci, I., Isa, Y., & Daura, B. (1982). Hausa Costoms. Zaria:   Northern Nigerian  Publication Company.

 

Nahuce, I. M. (2008). “Karin Maganar Hausa a Rubuce.” Kundin Digiri          na Biyu (M.A). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,       Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

 

Shuni, M. A. (2023). “Nazarin Amfani da Karin Maganganun Hausa na          Mutane Masu Bukata ta Musamman.” Kundin Digiri na Biyu (M.A).         Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu   Ɗanfodiyo.

 

Skinner, A. N. (1988). “Lexical Incompatability As a Mark of Karin      Magana.” Cikin Furniss, G. da Wasu (Editoci). Studies in Hausa          Language and Linguistics in Honour of F. W. Persons, London.

 

Umar, M. B. (1987). Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph Publishers.

 

Yakasai, S. A. (2019). “Nazarin Ma’ana a Muhallin Magana: Tsokaci a Kan Zaɓaɓɓun Karin Maganganun Hausa na Mutane Masu       Bukata Ta Musamman.” Ɗunɗaye Journal of Hausa StudiesVol. 2, No. 2 Pp.13-22. Sokoto:Department of Nigerisan Languages,          Usmanu Danfodiyo University.

 

Yunusa, Y. (1989). Hausa a Dunƙule. Kano: Maɗaba’ar Trium, Gidan   Sa’adu Zungur.

Post a Comment

0 Comments