Ticker

6/recent/ticker-posts

Basakkwaciya

Ya ke Basakkwaciya!
Saurari kalmomi daga zuciya.

Don ke zan taka tun daga Zariya,
In tsallake tekun Bahru Maliya.

Duk wata soyayya in ba taki ba,
Daidai ta ke da cin ganyen tumfafiya.

Ke na ke hange a cikin idanuwa
Ba ruwana da wata baturiya, ko ƴar Italiya.

Kafin soyayyarki, zuciyata zindir ta ke,
Sai kaunar ki ta lulluɓe ta da jallabiya.

Ke ce tauraruwa ta tilo ƙwarai,
A can faɗin sararin samaniya.

A can cikin taskar mata masu tsada,
Ke ce dai kaɗai kyakyawar zinariya.

Kar ku cece ni ko da kun ga zan nutse,
Domin soyayyarki ita ce ambaliya.

Kan ki ba batun Naira ko Fam na Ingila,
Gare ki zan iya kashe miliyoyin gangaliya!

Taka lafiya a sannu-sannu Sahibah.
Dole in miki kirari ya ke Sarauniya

Zan iya daina barci har abada,
Don in dunga tashin ki sallar safiya.

Dubin zubin nata na zuciya, sam ita babu hayaniya.
Ko dan na samu salama dole na bi ki babu ƙiriniya.

Aure da ke ba shi dan a kanki sai na yi mamaya.
Kin kira ni, Jamil na Buthaina, fatana ki zame min halaliya

Jiƙon ƙauna kin ba ni, to taya ya zan miki zamiya?
Daɗi da ba daɗi mu zauna, in kin ji yunwa zan baki kunu na tsamiya

Son ki ya shige zuciya ba sauran ƙafiyya
Sai dai in yi addu'a Allah Ya ƙara miki lafiya

Na san zaku murmushi wasu ko dariya
Domin kun ɗauka cewa ina ta hauragiya!

Hauragiya na ga wanda bai san zaƙi,
Da zafin da soyayya ke da shi ba a gaskiya.

©Potter

26/09/2023.

Post a Comment

0 Comments