Anya dai a 1806 Gusau ta zamo hedikwatar Katsinar Laka kuwa?

    Bayan wannan rabon da Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya yi a wannan shekarar (1806) jagoran wannan yankin na Katsinar Laka, Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa ya koma Yandoto inda ya fito domin ya ci gaba da gudanar da ayyukan jaddada Addinin musulunci kamar yadda aka umurce shi amma ya samu mummunar adawa daga Malaman Yandoto da basu aminta da da'awar Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da Mataimakan shi ba har ma suna jifar Malam Sambo Ɗan Ashafa da wasu kalaman dake nuna koda an bashi jagorancin wannan yankin ba dai shi ne ya ƙirƙiri Yandoto ba. Suka hana shi zama lafiya har ma ya dinga jujjuya wuraren zaman shi ya zuwa Chediya (Chediya a halin yanzu hedikwatar gunduma ce a cikin Masarautar Tsafen Jihar Zamfara) da Wonaka da Rawayya da Kamani da sauran su.

    Daga baya ne  ya samar da Gusau a cikin shekarar 1811 a matsayin sabuwar hedikwatar shi.

    A duba Infak'ul Maisur na Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio da Gusau Ta Malam Sambo wallafar Bello Muhammad Gusau Da Sa'idu Muhammad Gusau (1979, 1980, 1982, 1984 da bugun 2012) da kuma Littafin Mai Dubun Nasara ( Rayuwa, Halaye, Saƙonni da Jawaban Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji (Dr.) Muhammadu Kabir Ɗan Baba OFR) Wallafar Aliyu Rufa'i Gusau, 2014 domin ƙarin bayani.

    Daga Taskar

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    ÆŠanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.