Ciyawar Gamba
Ciyawa ce mai amfani kalakala duba da cewa kowace irin dabba na cin ta.
Ciyawan Gamba ta fi kowace kalan ciyawa yin zana mai tsawo ga kyau da yake ana yin zana da kalan ciyawa kamar su tcintciya. Amman zanan Gamba ya fi na tcintciya rufe gida, da wurin magewayi/ yauci saboda tsawons, haka ma yin rudu da buttani
Gamba
Karan Gamba ya fi kowane kara daɗin yin alƙalami.
Ban yi zaton ana samun Gamba a kowane wuri ba idan ba a sahara ba.
Gamba
Ciyawan Gamba sai a lokacin damana taka fitowa. Da zaran iska na yamma ya buga sai ta bushe. Muna yi ma wannan iska kirari da "Na yamma maganin mai tsanwa."
Daga Taskar
Mai Girma Sarkin Rafin Gobir
Mai Girma Isma'il Muhammad Yusuf
0 Comments
Post your comment or ask a question.