NA
Abu-Ubaida Sani
08133529736
abuubaidasani5@gmail.com
Wak'ar jajen hatsarin mota da Dr. A. Y. Gobir ya yi, ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, 2018; tare da fatan Allah ya ba shi lafiya, ya kuma sa kaffara ne.
- Na yi shirin adda da wuk’ak’e,
Na d’au gariyo hannuna.
- Na d’au sandata da kulake,
Na sa’ba takkwabi gefena,
- Na d’au mashina da na gada,
Tsitaka na nan hannuna.
- Barandamina na wasa shi,
Na d’au kibbau a kwarina.
- Majaujawa na d’au wannan,
Al’amuda na sanya gefena.
- Na d’au baka na rik’e zarto,
Gatari na nan hannuna.
- Na sha d’amarar kayan sulke,
Babbar garkuwa ke hannuna.
- Na yo huci, zumbur zabura,
Na bar Sakkwato dangina.
- In na yi taku sai an girgiza,
Za ka ga ramin sawu na.
- In na hau dutse sai ya dangaza,
Za ka ga garin bayana.
- In na bi daji sai ya bushe,
Za ka ga tsirrai sun k’una.
- Idan na bi kogi sai ya tsotse,
Tsabar zafin k’albina.
- Idan na ga tsuntsu sai ya fad’o,
Don hucin numfashina.
- Yau dai ko ni ko ita,
Ta ta’ba gefen rayina.
- Ba mai ba ni baki in tsaya,
Ana tsoron zafin raina.
- Ina tafiya sai na yi birki,
Abin mamaki a gabana.
- Tsohuwa da rufi na gani,
Ta tare hanya wurin bi na.
- Na d’ano kibiya na ta’be baka,
Na saita ta da mashin hannuna.
- Na zaro takobina d’in nan,
Na d’aga sandar dukana.
- Kan na d’au sauran kaya,
Kalamanta sukash shiga kunnena.
- “Idan ka kar ni gidan duniya,
Lahira tabbas ka k’una!
https://www.amsoshi.com/2017/08/22/duniyata-kashi-na-farko/
- Ni sunana ikilasi,
Tawakkali kuwa lak’abina.
- Kana da buk’atar taimako,
Ka bi ni ka ji su kalamaina.
- Ka yi shirin yak’i na gani,
Bai taimakonka tunanina.
- Tsautsayi da kake nema,
Tai tafiyarta wurin kwana.
- Sannan jakadar Allah ce,
Ba ta da laifi d’an d’ana.
- Tsautsayi da kake kallo,
Ba ta dare sai dai rana.
- Domin idan ta ziyarce ka,
Ga kai Allah na k’auna.
- Ka san tana rikid’ar siffa,
Fara ko bak’a mummuna.”
- Na zare ido na shiga thinking,
Don su biyu ne a tunanina.
- Muguwa mai bak’in kaya,
Ita ats tsautsayi guna.
- Mai zuwa da farin kaya,
Nasara sunanta tunanina.
- Ikilasi sai ta yi d’an tari,
Ta katse dukka tunanina.
- “Mace d’aya ce ba biyu ba,
Takan sauya ne d’an d’ana.
- In dai gajarce ma zance,
D’iya ce ‘ya ta cikina.
- A har kullum in ta zo ta,
Burinta ana tuna sunana.
- Idan ma an manta iklas,
Tawakkali duk d’ai na.
- Idan ta zo da farin kaya,
An fi yin tunanina.
- Idan ta sanya bak’in kaya,
Akan ma manta sunana.
- Ga shi kamar kai a yanzu,
Fed’es! Ka manta zancena.”
- Na yo ‘yar ajiyar zuci,
Kalaman sun tafa k’albina.
- Na mai da kibau cikin kwari,
Na sauk’e kayan yak’ina.
- Ta yi murmushi ta matso kusa,
Ta yo furucin k’arshe guna:
- “Duk wani mai so ya tsira,
Ya bibiyi dukka kalamaina.
- Ya je makaranta bid’ar saura,
Malam ya san zancena.
- Manta ni bak’in jahilci ne,
Dole ake tuna sunana.
- K’aryata ni ko kafirci ne,
Dole a yarda da zancena.
- Ziyarar ‘yata tilas ne,
Kasance cikin ko-ta-kwana.
- Ba shirin yin yak’i ba,
Shirin tunanin sunana.
- Ni ko zan zo a gareka,
In shiga cikin zuci in zauna.
- In sanyaya maka tunani,
In sa ka ji rai ya bar k’una.”
- Tana fad’in haka sai ta ‘bace,
‘bat! Ba ta a gabana.
- Na yi lankwat na yo kasak’e,
Kalaman sun shiga rayina.
- Ashe lallai na yo wauta,
Na so fita addinina.
- Dalilin ma kenan da ya sa,
Na manta gishiri girkina.
- Na fara baiti tor-tor-tor,
Ba godiyan mahaliccina.
- Na fara wak’a sar-sar-sar,
Ba salatin mazona.
- Yafe Allah na tuba,
Sallu alaihi manzona.
- Dad’o tsira da amincinka,
Gare shi macecin rayina.
- Saka da iyalai da sahabbai,
Da masu bin sa da k’auna.
- Na yi addu’a ya Allah,
K’ara lafiya da tsawon kwana.
- Ga malam tare da imani,
Y. A. Gobir limamina.
- K’ara masa arziki da bud’i,
Da juriyar addinina.
- Shiryar da zuriya tasa,
Su zam marik’a addinina.
https://www.amsoshi.com/2017/06/22/ta-jamia-mai-yar-jaka/
- Da mu da shi da iyalanmu,
Ka sa ranar k’arshen kwana-
- Furucin k’arshe daga bakinmu,
Shahada ce mai hana k’una.
- Amin Allahu ka amsa,
Ba don mu ba mak’agina.
- To a nan zan ja birki,
Na tattare duk ‘yan kayana.
- Abu-Ubaida d’a ga Sani,
Ga matambayin sunana.
- Yawan baitukanta saba’in ne.
Mi ta nazari dangina.
https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/
3 Comments
[…] Na Tinkari Tsautsayi Da Shirin Yak’i: Tawakkali Ta Tsai Da Ni […]
ReplyDelete[…] Na Tinkari Tsautsayi Da Shirin Yak’i: Tawakkali Ta Tsai Da Ni […]
ReplyDelete[…] Na Tinkari Tsautsayi Da Shirin Yak’i: Tawakkali Ta Tsai Da Ni […]
ReplyDeleteRubuta tsokaci.