𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Mallam musulunci ya haramta
asadu da mace tana cikin al'ada. tambaya anan shin ya halatta mace tayi wasa da
mijinta har maniyyi ya futa? Cikin al'ada Ko kuma shi zaice mata tayi wasa da
gabansa har maniyyi yafuta, meye hukuncin yin Hakan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wabarakatuhu.
Dukkan Maluman Musulunci suna ganin halaccin Mutum
ya kwanta shimfida guda da Matarsa alokacin da take cikin jinin haila, har ma
ya halatta su aikata komai irin nasu na Ma'aurata amma banda Jima'i.
Suna kafa hujjah ne da hadisin Sayyiduna Anas bn
Malik (ra) wanda yake cewa : "Yahudawa sun kasance idan Mace tana haila basu
cin abinci tare da ita, kuma basu zaunawa waje guda da ita. Da Sahabban Manzon
Allah ﷺ suka
tambayeshi game da haka sai Allah Mai girma da daukaka ya saukar da ayar nan ta
cikin Suratul Baƙarah :
وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ ۖ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ ۖ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ ۖ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ
Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi
cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance
su (wato kar kuyi jima'i dasu) sai sun yi tsarki (wato bayan daukewar jininsu
kenan). To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku.
Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakewa. (Suratul
Bakara 222)
Sai Manzon Allah ﷺ yace ma Sahabbansa "KU AIKATA KOMAI
DASU IN BANDA JIMA'I". (Imamu Ahmad da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Masrouƙ bn Al-Ajda' yace "Na tambayi Nana A'ishah
menene ya halatta ga Namiji alokacin da Matarsa take cikin haila? Sai tace
"KOMAI DA KOMAI, IN BANDA FARJI". (Wato zai ita Mu'amala da dukkan
Jikinta amma banda al'aurarta). (Imamul Bukhariy ne ya ruwaitoshi acikin
Tareekh).
Wato zata sanya Wani zani tayi Ƙunzugu dashi, ko kuma ta sanya Gajeren
wando wanda zai rufe tun daga Ƙasan
cibiyarta har zuwa gwiwarta, Sannan ta kwanta Shimfida guda da Mijinta.
Akwai Hadithi daga Nana Maimunatu bintul Harith
(ra) tace "Manzon Allah ﷺ ya
kasance idan yana nufin yin Mubashara da wata Mata daga cikin Matansa wacce
take cikin Haila, yakan umurceta da tayi Ƙunzugu" (Bukhariy da Muslim ne suka
ruwaitoshi).
Don Ƙarin
bayani aduba wadannan hadithan :
Sahihul Bukhariy hadisi na 300-303.
Sahihu Muslim hadisi na 293-294.
Abu Dawud hadisi na 211, 269.
Sannan aduba RISALATUL ƘAIRAWANIY babin dake magana akan haila.
Sai kuma AL-FIƘHUL
WADHIHU juzu'i na 1, shafi na 104-105.
Sannan dangane da hukuncin fidda maniyyi ba tare
da Jima'i ba, Malamai sun ce ya halatta Mace ta shafi al'aurar Mijinta har ya
fitar da Maniyyi, ko kuma shi ya shafi al'aurarta har ta biya bukatarta. Amma
idan mutum ya shafi tasa al'aurar da kansa har Maniyyi ya fita, to Wannan shi
ne Istimna'i wanda mafiya yawan Maluman Musulunci suka ce Haramun ne.
Amma idan mace tana cikin haila bai halatta
mijinta ya shafi Farjinta ba, sai dai sauran sassan jikinta. (Kamar yadda aka
faɗa cikin hadisan dake
sama).
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.