𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malam, barka da safiya.
Tambayata ita ce: Mace ce mijinta ya kauce hanya (ta kama shi da mace). To, shi
ne take bin hanyar da ta san za a iya bi don ta katange shi daga wancan
mummunan aikin. Shi ne take yi masa dabaru domin karɓar kuɗi a wajensa, wani lokaci ma takan ɗaukar masa kuɗi kamar N500, ta cika ta sai turaruka masu
tsada. Malam to, wannan abin da take aikatawa, shin ko tana da laifi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
Wajibinta ne da ma tun farko ta ɗauki dukkan matakan da suka halatta domin
kare mijinta, da hana shi aikata irin wannan ɓarnar. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ya ce:
مَنْ رَآى مِنْكُمْ مُنْكَراً فَلْيُغَيِّرْهُ بِيَدِهِ ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِلِسَانِهِ ، وَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِقَلْبِهِ ، وَذَلِكَ أَضْعَفُ الْإِيمَانِ
Daga cikinku duk wanda ya ga wani abin ƙyama
to ya gyara shi da hannunsa, idan kuma ba zai iya ba to da bakinsa, idan kuwa
ba zai iya ba to da zuciyarsa, kuma wannan ne mafi raunin imani.
Amma yin dabara, wadda ta haɗa da yin ƙarya, ko yaudara, ko
sata, ko barazana, ko dai wata dabara, domin samu ko karɓar kuɗi daga gare shi, wannan kam bai halatta
ba. Kuma ba shakka, wannan matar tana da laifi a kan haka, har sai ta tuba,
kuma ta nemo amincewarsa da yafewarsa. Wannan ya zama haka ne, matuƙar dai
yana ɗaukar
nauyin biya mata haƙƙoƙinta da suka hau kansa
gwargwadon hali da ikonsa.
Idan kuma ba ya sauke haƙƙinsa ne saboda mummunar
ɗabi’ar rowa ko
makamanciyarta, to a nan ne Malamai suka yarda cewa za ta iya ɗaukar abin da zai yi daidai da buƙatarta
da na ’ya’yanta,
saboda Hadisin Hindu matar Abu-Sufyaan (Radiyal Laahu Anhumaa).
WALLAHU
A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.