Saɓe:-
Saɓe wata ciyawa ce mai albarka da kwarjini. A cikin fadama take fitowa wajen da babu noma ta kan yi baƙi ta yi kyau sosai amma ba ta daukan lokaci mai tsaho sai ta yi ja, kenan ta fi son wajen da aka yi noma, idan ta fito ta wajen da noma yake za ka ga ciyawan saɓe baƙiƙirin tsanwa shar gwanin sha'awa, ganyenta tana da laushi da daɗin taɓi domin bata da ƙaya bata da kaifi.
Taken bushe a lokacin rani idan iskan yamma ya buga takan yi ƙonshi ta fitar da kai kaman sauran ciyayi 'yan uwanta, haka ma takan yi ƙwaya ƙanana kanana, ƙwayan yakan zube a nan inda ya fito kuma su ne suken zam irin da zai sake fitowa damuna mai zuwa idan Allah ya kai mu.
Shawara ga malaman gona da su kula ga ma su yin feshi ga irin waɗannan ciyayin a lokacin da ba su riga sun zubar da ƙwayoyinsu ba, tabbas wata rana duniya za ta nemi ire-iren waɗannan ciyayin a rasa.
Daga Taskar
Mai Girma Sarkin Rafin Gobir
Mai Girma Isma'il Muhammad Yusuf
Proofread By:
Nafisa Abdullahi
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.