Ticker

6/recent/ticker-posts

Zubi Da Tsarin Waƙoƙin Bara

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Zubi Da Tsarin Waƙoƙin Bara

Zubi da tsari shi ne yadda mawaƙi ke saƙa tare da tsara zaren tunaninsa a cikin waƙa. Dumfawa (2002:63).

Wannan na nufin irin tsarin da mai waƙa ya yi amfani da ga isar da saƙonsa da ya sa cikin waƙarsa. Wannan zai haɗa da yadda ya tsara ɗiya ko baitocin waƙarasa da yadda ya tsara saƙon waƙar daki-daki yadda mai saurare ke iya karɓar saƙon ba tare da wata rikitarwa ba.

Zubi da tsari shi ne yadda mawaƙi ya tsara waƙarsa, a nan za a duba tsarin waƙa dangane da yadda aka shirya ta. Wato za a duba carbin tunanin mawaƙi. Ɗangambo (2007:17).

Wannan bayani ya yi kama da wanda ya gabace shi, sai dai akwai ƙarin bayanin cewa ‘zuba carbin tunani’ wanda ke nuna tunanin a cikin tsari aka zuba shi, wato baitoci ko ɗiya. Wannan zubi akwai shi a waƙoƙin bara kamar yadda sauran waƙoƙi da ba na bara ba suke da shi. An dubi wannan zubi na waƙoƙin bara aka yi bayaninsa tare da misalai.


Post a Comment

0 Comments