Ticker

6/recent/ticker-posts

Awon Baka

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Awon Baka

Awon baka shi ne yadda mawaƙi ya zuba ɗiyan waƙarsa. Gusau (2003:32). Wannan na nufin irin yawan layuka ko tsawon layukan a cikin ɗan waƙa. A waƙar bara ɗiya ba su cika ƙunsar fiye da layi ɗaya ba, kaɗan ne ƙwarai ke zarta haka. Misali:

Ja gora: A tumbulo Inna a tumbulo.

Amshi: To, to.

Ja gora: A tumbulo a kawo ma gajere.

 Amshi: To, to.

 Ja gora: Gajere ba abin reni ne ba.

 Amshi: To, to.

(A Tumbulo)

Waƙar da ta gabata za a ga ba ta da ɗiya da yawa a cikin ɗiyanata. Kowane ɗa layi ɗaya ne yake ƙunshe da shi. Kusan mafi yawan ɗiyan waƙoƙin bara a bisa wannan awo suke.


Post a Comment

0 Comments