Ticker

6/recent/ticker-posts

Zayyana

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Zayyana

Wannan salo shi ne wanda mawaƙi kan tsaro bayanin faruwar wani ko yadda zai faru a cikin waƙa ta har yadda mai saurare zai ji kamar ga abin nan a gabansa yana faruwa. Wato bayanin da mawaƙin ya yi ya sa idanun zuciyar mai saurare na ganin yadda abin ke gudana. Misali:

 Almajiri tsuntsu ne,

 Da ya ji motsin tsaba,

 Sai ya yi hiringi da kunne,

 Kama da mataccen kusu,

 (Almajiri Tsuntsu ne)

Duk lokacin da mai sauraro ya ji wannan ɗa , a daidai waɗannan layuka na uku da na huɗu sai ya ji kamar yana ganin yadda almajirin ya sifantu da wannan sifa sakamakon motsin tsaba da ya ji. Zayyana masa hiringi da kunne da dubin yadda kunnen mataccen kusu yake zama ƙyam ba motsaawa shi ke sa ya ji kamar yana ganin abin da ke faruwa ga almajirin. Sai ya gani a ransa kamar ga wani tsuntsu nan an watsa tsaba shi kuma ya kashe kunnensa ko dai don nufinsa na ya samu abincin da ya daɗe yana nema ko kuma don ya fake ne kar a gane shi yana cin tsabar a kore shi, sai wannan kashe kunne da ya yi ta mayar da shi kama da mataccen kusu (ɓera).

A wani misalin ana cewa:

Jagora : Annabi ya hito da haske da kyawo,

 Amshi : To

 Jagora : Kowa ya gane shi ya ɗora murna,

 Amshi : To

 Jagora : Ke ko kin gane shi kin ɗora kuka,

 Amshi : To

 Jagora : Ba kukan rashin ɗiya niy da shi ba,

 Amshi : To

 Jagora : Don ƙamnar Rasulu Manzo fiyayye,

 Amshi : To

(Yabon Annabi)

A cikin waɗannan ɗiyan waƙar da na kawo a sama, akwai hoto a cikin bayani wanda shi ake kira zayyana, domin mai saurare waƙar kan iya riya yadda Annabi kuma ya gani a zuciyarsa irin hasken da aka ce ya siffantu da shi. Zai iya ganin sa a zuci a matsayin mai cikakken kyau wadda kowa da komai ke murnar gani a lokacin da ya fito. Sai aka kawo wata kaza tana kuka ga kuma wani mutum yana tambayar ta dalilin ɓacin ranta bayan kowa na cikin murnar ganin Annabi. Daga ƙarshe sai ta nuna cewa son Annabin ne ya sa ta kuka ba wai don ‘ya’yanta da shaho ya cinye ba.


Post a Comment

0 Comments