Ticker

6/recent/ticker-posts

Kambamawa

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Kambamawa

Ita wannan wani lafazi ne ko furuci da mawaƙa kan yi wanda sai a ga abu ne mai wuya haka ta auku, sukan faɗi abin da ba zai yiwu ba, su nuna ya auku ko zai auku; ko kuma su ce in ma ya auku ba zai hana haddasa wani abu ba. Ɗangambo, (2007:43).

Wato ke nan kambamawa shi ne faɗin aukuwar wani abu wanda hankali bai iya kamawa kuma a ce haƙiƙa ya auku. Mawaƙa na amfani da wannan salo domin nuna ƙololuwar wani abu da suke son nunawa. Misali:

 “Mara goma ta yaro ce,

 Ni saba’in nika canyewa,

Ga sittin bisa leɓona,

Ko ƙoshi ban fara ba.

 (Iya Siriri)

A wannan waƙar mabaracin yana son ya nuna shi ma’abucin cin abinci ne har yadda ba a zato. Domin tabbatar da haka sai ya ɗan bayar da labari irin abin da yake iya canyewa. Mai bara na yin haka domin kada masu ba shi sadaka su yi ba shi abinci komai yawansa. Sai ya gaya masu ga abin da yake ci kuma duk da haka ba don ya ishe shi ba. Wannan ci da almajirin da ke rera wannan waƙa yake da’awar yana da shi kambamawa ce, cin nasa ko alama bai kai haka ba ko kusa.

Post a Comment

0 Comments