Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Bismillah Rabbana

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Ya Bismillah Rabbana

 Jagora: Ya bismilla Rabbana,

 Amshi: To

 Jagora: In yaro bai san ta ba,

 Amshi: To

 Jagora: Ni da na san ta na sha wuya,

 Amshi: To

 Jagora: Matar malam ta bugan,

 Amshi: To

 Jagora: Har shi malam ya bugan,

 Amshi: To

 Jagora: Nit tahi nit tahi nit tahi,

 Amshi: To

 Jagora: To Nit tahi can bisa goɗiya,

 Amshi: To

 Jagora: Sai naga kura can tahe,

 Amshi: To

 Jagora: Sai nacce wa zaki ci,

 Amshi: To

 Jagora: Sa ta ce almajiri,

 Amshi: To

 Jagora: Sai na baɗe ta da magani,

 Amshi: To

 Jagora: Kahin a jima ban gan ta ba,

 Amshi: To

 Jagora: Sai na wuce ban gan ta ba,

 Amshi: To

 Jagora: Na dawo ban gan ta ba.


Post a Comment

0 Comments