Ticker

6/recent/ticker-posts

Inna Uwarmu Ce

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

 Inna Uwarmu Ce

 Jagora: Ɗan almajirin bara Inna uwarmu ce,

 Amshi: To

 Jagora: Da farko za mu sa Jalla Jalaluhu,

 Amshi: To

 Jagora: Allah wanda bai da farko balle ƙarshe,

 Amshi: To

 Jagora: Inna na taho da ƙoƙo ina bara

 Amshi: To

 Jagora: Ɗan almajirinki ne Inna uwar gida,

 Amshi: To

 Jagora: Ko da karkaren tuwu ne ina bara,

 Amshi: To

 Jagora: Ɗan almajirin bara ƙanzo nashi ne,

 Amshi: To

 Jagora: A ba shi na Allah da na Anmnabi,

 Amshi: To

 Jagora: Wanda ya ba shi don Allah kuma don Annabi,

 Amshi: To

 Jagora: Ba shi talauci a duniya har can lahira,

 Amshi: To


Post a Comment

0 Comments