Ticker

6/recent/ticker-posts

Almajiri Da Ƙaho:

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Almajiri Da Ƙaho:

 Jagora: Dan Tuɓulle, Tuɓulle,

 Amshi: To

 Jagora: Almajiri da ƙaho,

 Amshi: To

 Jagora: Guda na shukar gero,

 Amshi: To

 Jagora: Guda na shukar dawa,

 Amshi: To

 Jagora: Guda na shukar marar tuwo a sa ta a baki da daɗi,

 Amshi: To

 Jagora: Sai ni na malam Sani,

 Amshi: To

 Jagora: Najje baran alkali,

 Amshi: To

 Jagora: Ciwon ciki yak kamman,

 Amshi: To

 Jagora: Daga mai jiƙa min kanwa,

 Amshi: To

 Jagora: Sai mai jiƙa min manda,

 Amshi: To

 Jagora: Ba magani ke nan ba,

 Amshi: To

 Jagora: A samu farare-farare,

 Amshi: To

 Jagora: A samu fararen mata,

 Amshi: To

 Jagora: Su ɗebo nonon shanu,

 Amshi: To

 Jagora: Su likkiɗa mini damu,

 Amshi: To

 Jagora: In karkace hulata,

 Amshi: To

 Jagora: In rangaɗa ma cikina,

 Amshi: To

 Jagora: Ciwon ciki ya yi sauƙi,

 Amshi: To


Post a Comment

0 Comments