Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
WAƘOƘIN NOMA NA MAKAƊA SAIDU MAIDAJI
SABONBIRNI
Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Saidu Maidaji Sabonbirni
An haifi Alhaji Sa’idu Maidaji Sabonbirni a shekarar 1938 a garin Tara ne ta sarki Ƙwanni wadda take ƙarƙashin Sabonbirni ta sarkin Gobir a jihar Sakkwato. Sunan mahaifinsa shi ne Mainasara. A lokacin rayuwar mahaifinsa suna zaune a garin Tara sai wata rigima ta kaure ana ta faɗace-faɗace sai mutane suka riƙa tashi suna barin garin, shi kau sai ya ce ba zai tashi ya bar shukarsa ta lalace ga banza ba, sai ya koma a gonar inda ya gyara wurin zama suka zauna tare da sauran ‘yan’uwansa wato irin zaman da ake ce wa zaman gona, basa zuwa gari watakila sai ran kasuwa ko ranar juma’a. to bayan da aka koma a gidan gonar ne aka haifi sa’idu, sai ake kiransa Maidaji, wannan shi ne dalilin wannan laƙabin nasa na Maidaji wato ɗan gidan gona. Suna nan zaune har Maidaji ya girma sai wata shekarar ruwa ya yi musu ambaliya ya rusa masu ‘yan gine-ginen da suka yi! Sai mahaifinsa da shi da sauran iyalinsa suka bar gidan gonar na Tara[1] suka koma Rambaɗawa. Rambaɗawa a ƙarƙashin sarkin Ƙwannin Tara, ita kuma Tara tana ƙarƙashin sarkin Gobir.
Ba sai an ce Maidaji ya yi noma ba, saboda ganin irin tashinsa na gidan gona, tun yana yaro noma ya tashi cikinsa kuma da ya girma ya shahara sosai ga noma. Bayan noma ya taɓa karatun allo, ya yi tafiye-tafiye don yawon makaranta, ya je kamar Mailalle da tsamaye. Yawanci Maidaji da abokansa sukan sauka a wajen wani sarki ne ko hakimi wanda suka tabbatar yana da abinci, sukan yi yarjejeniya da sarkin cewa ya dinga ciyar da su, su kuwa su riƙa yi masa noma idan sun dawo daga aikin gona sai su yi karatunsu na allo da ya kawo su, don haka duk inda suka tafi ba su yin yawon bara, ya yi karatu har ya sauke alkur’ani. Ya yi karatun yaƙi da jahilci kafa shi a ƙauyensu, amma bai daɗe a ciki ba.
Alhaji Sa’idu Maidaji ya yi gadon kiɗa da waƙa ne domin mahaifinsa ya yi, kuma wansa Nadada ya yi, hasali ma shi ne makaɗan garin, sannan kuma wani wansa wanda ake kira alhaji Maigari ya yi kiɗan. Ba a wajen maifinsa ya koyi waƙar ba, a wajen wansa ne Nadada ya koya, sannan yana da hikima da basira wajen waƙa.
Bayan ya zama maigidan kansa wato
bayan rasuwar wansa Nadada Maidaji ya haye khalifar ya shahara a waƙoƙin
noma ne da na sarauta har ya zama shi ne makaɗan Rambaɗawa, ya yi
tafiye-tafiye a garuruwa da dama don waƙa.
Kamar
yadda bayani ya gabata Maidaji ya tashi a gidan kiɗa ne, mafi yawan
yaransa waɗanda ke yi masa
amshi danginsa ne, daga ƙannensa sai ƙanen tsohonsa sai
wansa sai kuma ‘ya’yansa. Ga sunayen yaran nasa kamar haka:
1.
Tanko
Ibrahim – (ƙanen mahaifinsa ne)
2.
Alhaji
Maigari – (Wansa ne)
3.
Hana
– (ɗansa ne)
4.
Baciri
– (ɗansa ne)
5.
Abara
- (ɗansa ne)
6.
Sallau
- (ɗansa ne)
7.
Garba
na Mai ƙosai - (ɗansa ne)
8.
Dogo
- (ɗansa ne)
9.
Ɗan Malam - (ɗansa ne)
10. Ibrahim - (maroƙinsa ne kuma baransa ne)
Malamai
da ɗalibai daga
jami’o’i da dama suna zuwa wajensa don yin bincike a kan waƙoƙinsa,
ya yi waƙoƙi masu yawa fiye da dubu na noma da na sarauta da na
sauran jama’a. Ya rasu a wajajen shekara ta dubu biyu, Allah ya gafarta masa da
rahamarsa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.