Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Ɗanladi Ƙanen Buzu
G/Waƙa: Ya kwan da shirin
aiki,
: Ɗanladi ƙanen
Buzu.
Jagora: Sarkin yaƙi
ƙanen
Buzu.
‘Y/ Amshi: Ɗanladi
miyas sallah,
: Ai
bata iri daɗi[1].
Jagora: Haba Ɗanladi
tsare aiki.
‘Y/
Amshi:
Mu kau mu tsare turu[2].
Jagora: Dogo barka da yini daji.
‘Y/ Amshi: Barka da zuwa gona.
.: Ya
kwan da shirin aiki,
: Ɗanladi ƙanen
Buzu.
Jagora: Ƙwazon
makaɗa ya gode.x2
‘Y/ Amshi: Bakin da ya ci ya gode,
: Mu
bamu butulce[3]
ba.
: Ya
kwan da shirin aiki,
: Ɗanladi ƙanen
Buzu.x2
Jagora: Kwanakki ana shirin yawo,
‘Y/ Amshi: Ya ba ni sule goma,
:
Kuma da munka zo kura,
:
Ya ba ni sule goma,
:
Kuma da munka dawo nan,
:
Ya ba ni sule goma,
:
Komi aka yi, ya yi.
: Ya
kwan da shirin aiki,
: Ɗanladi ƙanen
Buzu.
Jagora: Haba Arne tsare kai taki.x2
‘Y/ Amshi: Don Allah bari sa rani.x2
: Ya
kwan da shirin aiki,
: Ɗanladi ƙanen
Buzu.
Jagora: Ƙwazon
makaɗa ya gode.x2
‘Y/ Amshi: Bakin da ya ci ya gode,
: Mu
bamu butulce[4]
ba.
: Ya
kwan da shirin aiki,
: Ɗanladi ƙanen
Buzu.x2
Jagora: Sarkin yaƙi
ƙanen
Buzu.
‘Y/ Amshi: Ɗanladi
miyas sallah,
: Ai
bata iri daɗi.
Jagora: Dogo barka da yini[5]
daji.x2
‘Y/ Amshi: Barka da zuwa gona.
.: Ya
kwan da shirin aiki,
: Ɗanladi ƙanen
Buzu.x2
0 Comments
Post your comment or ask a question.