Ticker

6/recent/ticker-posts

Isah Na Zurmi

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Isah Na Zurmi

 G/ Waƙa: Karyar  mazan noma isah,

: Jikan Ɗanmakau,

: Ka fi ‘yan maza noma isah,

: Jikan Ɗanmakau.

 

 Jagora: Karyar mazan ruwa.

‘Y/ Amshi: Karyar  mazan noma isah,

: Jikan Ɗan Makau ,

: Katu yan maza noma isah,

: Jikan Ɗan Makau.

 

Jagora: Kai ka yi masu noma x2.

‘Y/ Amshi: Ga bajimi barkan ka da aiki,

: Kai kwazo.

 

 Jagora : Dangin sake ni nai uzurun.

‘Y/ Amshi: Ka yi noma ka noma dawa.

: Ad daidai ai ka yi hatsi,

: Jikan Ɗanmakau.

 

 Jagora: Danji  sakeni dan gutsure.

 ‘Y/ Amshi: Ka yi noma ka shikka dawa,

: Ad dai dai.

 

Jagora: Karyar maza ka yi noma magaji,

: Jikan Ɗan Makau.

‘Y/ Amshi: Ga ba jinin shehu,

: Ku ka muka zo da ji kai gero.

 

Jagora: Ranar  da muka zo gayya sarkin,

: Kiɗi muka zo daji kai gero.

‘Y/ Amshi: Noma kware mu ja mai.

 

Jagora: Rai maza sannu da aiki.

‘Y/ Amshi: Karyar maza wane na,

: Jikan Ɗanmakau.

 

Jagora: Sai  kun zo ga noma.

 ‘Y/ Amshi: Kai dan shehu ku ka aiki,

 

Jagora: Mani na manga ya gode.

‘Y/ Amshi: Ga isah ya riga kalme,

: Nai walkam.

 

Jagora: Sani  na mai kano.

: Wane  ga wani ya yi ma,

: Tuka.

 

‘Y/ Amshi: Ga  wani minahiki,

: Na kwance kahi ƙarhin maza,

: Isah na zurmi aiki dai dai.

 

Jagora: Wane ba ka  son mata jeka,

: A daura ma jakkai.

 ‘Y/ Amshi: Ka hi  yan maza noma,

: Isah na zurmi jikan Ɗan Makau.

 

Jagora: Kai maza na noma.

: Ga kila na kware.

‘Y/ Amshi: Noma shi  ad dai dai.

 

Jagora: Kai sannunku da aiki.

‘Y/ Amshi: Ga Bajinin shehu kuka aiki,

: Zak kwaza.

 

Jagora: Kai  wane ba’a ce  maka raggo.

‘Y/ Amshi: Karyar mazan noma,

: Isah na zurmi jikan Ɗan  Makau,

 

Jagora: Sannu  na baba ƙaryar,

‘Y/ Amshi: Sannu  na baba ƙaryar ,

: Maza yunƙura namiji.

 

Jagora: Tunbin aiki,

: ‘Yan aiki.

‘Y/ Amshi: Karyar maza yan aiki,

: Ga na ku haka.

 

Jagora: Yunƙura jikan Ibrahim,

: Mamman na audu.

 ‘Y/ Amshi: Yunƙura jikan Ibrahim,

: Mamman na audu.

 

Jagora: In kagga Ɗan Bala na tonon,

: Falke.

‘Y/ Amshi: Na yi godiya  ga Muhammad,

: Zaki ba ka tsoron rana.

 Jagora: Kowa ya yi ma ɗan gutsture ,

: Kana yi mai abu mai kuraru[1].



[1]  Abu mai muhimmanci.

Post a Comment

0 Comments