Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakokin Noma na Hauwa Kulu Mukkunu

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

 Waƙoƙin Noma na Hauwa Kulu Mukkunu 

Waƙoƙin Noma na Hauwa Kulu Mukkunu

Taƙaitaccen Tarihin Hauwa Kulu Mukkunu

An haifi Hauwa Kulu Mukkunu a shekarar 1942 a garin Abare ta ƙaramar hukumar Gummi a jihar Zamfara. Mahaifinta wani makaɗi ne kuma ɗankasuwa, mai suna Abdullahi. Mawaƙiyar sunansu ɗaya da mahaifiyarta wato Hauwa, amma an fi sanin ta da suna Ladi. Kakanta na ɓangaren uwa wato mahaifin Ladi sunansa Alu Maitandu[1] wani sanannen makaɗin sarakuna da manoma a nasa lokacin, don haka Hauwa ta gaji kiɗa ne gaba da baya (wato ta uwa ta uba). Sunan mijinta malam Aliyu wani mutumin Wasagu. Mijin nata ya ba ta ƙarfin guiwar yin waƙa don bai hana ta ba, ko nuna damuwarsa ga yin waƙar tata. Ta fara yin waƙa ne a shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da biyu (1982) a lokacin da ta yi wa wani fitaccen manomi kuma hakimin gundumar Wasagu Alhaji Haruna waƙa. Tun daga nan ne ta cigaba da yi wa manoma waƙoƙinta iri-iri.

Kayan kiɗinta su ne kalangu waɗanda wasu maza suke kiɗa mata a lokacin da take waƙarta. Ita kaɗai take yin waƙarta ba tare da yi mata amshi ba.

Rasuwarta

Hauwa Kulu Mukkunu ta rasu a ranar ashirin da takwas ga watan shida shekarar dubu biyu da goma (28/6/2010) a sandiyyar rashin lafiyar da ta yi. Ta rasu ta bar ‘ya’ya bakwai, maza biyar mata biyu. Allah ya jiƙanta da rahamarsa, amin.



[1]  Ya sami wannan suna ne saboda kayan kiɗansa su ake kira tandu.

Post a Comment

0 Comments