Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakokin Noma Na Audu Dangunduwa

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Waƙoƙin Noma Na Audu Ɗangunduwa

Waƙoƙin Noma Na Audu Ɗangunduwa 

Taƙaitaccen Tarihin Audu Ɗangunduwa

Sunansa zananne shi ne Abdullahi, an haife shi ne a garin Tungar Ɗangudo wani ƙauye a ƙaramar hukumar Talatar Mafara  a shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da ashirin daidai (1920). Audu ya gaji kiɗa ne ga mahaifinsa Alhaji Abdullahi Ɗangunduwa Kagarar Morai domin shi ma makaɗi ne sananne a yankin bakiɗaya.

Magidanci ne matarsa ɗaya mai suna Amina, ‘ya’yansa tara maza shida mata uku. Akwai daga cikin ‘ya’yan nasa Muhammadu Sani da Ya’u da Shehu da Nasiru da Mustafa da Kuma Yunusa, su kuma matan su ne Aisha (babba) da Rabi da kuma Aisha (ƙarama). Yana yin kiɗe-kiɗen noma da na sarakuna. Kayan kiɗansa kalangu ne da wanim lokaci kotso na kiɗin sarakuna. ‘yan amshinsa su bakwai ne, akwai Ya’u da Hussanida Sa’idu daAbubakar da Muhtari da Muhammadu Nagido da kuma Ummaru Guga, sai kuma Muhammadu Sani wanda shi ne ya jagoranci ƙungiyar bayan rasuwar tsohon nasa.

Post a Comment

0 Comments