Ticker

6/recent/ticker-posts

Alhaji Sani Mai Burodi Na Dakitakwas

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Alhaji Sani Mai Burodi Na Ɗakitakwas

 

 G/ Waƙa: Mu dinga yin aiki,

: Namijin jiya.

 

 Jagora : A gaida Mamman ɗan Mamman,

: A gaida rani mai tare haki,

: Ai don haka ni zamna ɗaki takwas,

: In ban da Mamman da tahiya ni kai,

: Ni ban zama Kulu,

: Don zan raɓe – raɓe,

: Ai da gidanmu na gado zani na,

: An ka zanna inda gimmu za ni,

: Abin ga na gado wajjen kulu,

: Yau hadda ni Kulu kowa ya sani.

 

Jagora: Alkura’a nai yab bar ma ni,

: Banda abokin jayayya gidan nan,

: Saboda Mamman ɗan Mamman

: Na Mamman,

: A gaida rani mai ƙare haki,

: Na roƙi Allah sarki mai sama,

: Na roƙi tutal mulki maji kira,

: Roƙon da niy yi Ta’ala ka riƙa man,

: Haji Bello,

: Malam Bello,

: Na gode maka,

: Wahabu Allah dai ya riƙa maka,

 

Jagora : Na gode Sani,

: Mai borodi na Ɗaki takwas,

: Wahabu Allah dai ya riƙa maka,

: Abin da ba ka da Jallah ya ‘yamma,

: Ai ga damana ta faɗi maƙigudu,

: Sabon gari ban gona na tsare,

: Sai na zuba ku ga gona na tsare,

: A kai a kama,

: Haba Mamman a kai a kama,

: Hat a yi azzahar,

: Ga da raggo suma za ya yi,

: Sai na gane raggo kumya za ya yi,

 

Jagora : Na gode Sani mai burodi,

: Na Ɗaki takwas,

: Ashe akwi mazaizai ɓoye Asa gudu,

: Ni ban Sani ba da roƙo niz zaka,

: Na zaka ni Kulu bai nuna mani,

: Wahabu Allah dai ya riƙa maku,

: Abin da babu Jallah ya ‘yammaku.

Post a Comment

0 Comments