Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
WAƘOƘIN NOMA NA BAWA DAN ANACE GANDI
Taƙaitaccen Tarihin Rayuwar Ɗan’anace
An haifi Muhammadu Bawa Ɗan’anace a garin ‘Yar tsakkuwa ta ƙasar Gandi a ƙaramar hukumar Raɓa ta jihar Sakkwato. Ɗan’anace bai gaji waƙa ba daga mahaifinsa, saboda shi mahaifin nasa ba makiɗi ba ne manomi ne. Bawa Ɗan’anace ya koyi kiɗi ne daga ƙanen mahaifiyarsa wanda ake ce wa Anace kuma shi ya riƙi Muhammadu Bawa tun yana ƙaraminsa. Anace wani shahararren mawaƙin ‘yan dambe ne kuma shi ne sarkin makaɗan ‘Yar tsakkuwa.a lokacin rayuwarsa.
Bawa
Ɗan’anace
ya fara kiɗi ne saboda tashin
da ya yi a hannun kawun nasa, da farko shi ma ya ɗauki kiɗan dambe ne, sai ya
watsar ya koma ma kiɗan noma. A cikin kiɗan noman ne Bawa Ɗan’anace
ya fara yin fice, kodayake ya koma ma kiɗin dambe daga baya inda ya haɗu da su Shago da Ɗandunawa
dasauran ‘yan damben da ya yi wa waƙarsa ta damben. An
ce da farko Ɗan’anace ya tsani Shago kuma ya ƙi
yi masa waƙa! Sai da Shago ya sha wahala ƙwarai
wajen shawo kansa sannan ya amince ya yi masa waƙar, har kuma suka
riƙa yawon dambe tare da shi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.