Ticker

6/recent/ticker-posts

Garba Nagodi

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Garba Nagodi

 

  G/Waƙa: Maigida gona,

: Kandare[1] Ali ka ba Garba Nagodi.

 

Jagora: Na gaida wane rannan,

: Yaki taɓa man.

  ‘Y/ Amshi: Halama kai ka  ba ni awaƙai.

 

  Jagora: Mai takama da iko.

  ‘Y/ Amshi: To wane in ba ka  ba ni komi,

: Kar ka matsa man.

 

  Jagora: Sarki adda gari, shi adda mutane.

  ‘Y/ Amshi: Shi ka ajin kuɗɗi a miƙa man.

 

  Jagora: Na ga had da kai an ba ka takarda.

  ‘Y/ Amshi: Dauri ka ce mai ba ka iyawa.

 

  Jagora: Wanda ad da girman kai.

  ‘Y/ Amshi: Hulla bata kyau garai,

: Sai dai ya yi malhwa[2],

: Yau asirin wane ya tonu.

 

  Jagora: Na ‘yan masaƙa Garba na Janu.

  ‘Y/ Amshi: Mai cin hakin gona da haƙora.

  Jagora: Garba ya yi noma ya yi karatu.

  ‘Y/ Amshi: Ya bi ubanai kai da kahwahu[3].

 

  Jagora: Inda karatu na hana kyauta.

  ‘Y/ Amshi: Da ban zuwa garkakku da roƙo.

 

  Jagora: Ko  ba ni gida ko na tafiya ta.

  ‘Y/ Amshi: Kow auri mai goyo a faɗa man.

 

  Jagora: Koh haihi ɗa nai,

: Shi ka kiwo nai.

  ‘Y/ Amshi: Ba a zuwa aure da agola.

 

  Jagora: Koh haihi ɗa nai,

: Shi ka kiwo nai.

  ‘Y/ Amshi: Ba a zuwa aure da agola[4].

 

  Jagora: Wanda duk yay auri matata da agola.

‘Y/ Amshi: Kar ya bari ɗana ya yi rama,

: Maigidan gona,

: Kandare Ali ka ba Garba Nagodi.

 

  Jagora: Ni nawa aure bashi macewa.

  ‘Y/ Amshi: Sai na ga alƙali da idona,

: Mai gida gona,

: Kandare Ali ka ba Garba Nagodi.

 

  Jagora: Armen kiwo armen wahala na.

  ‘Y/ Amshi: In baki kamnata tahiyarki.

 

  Jagora: Ke na gaji day yau  ba ni iyawa.

  ‘Y/ Amshi: In kin ga ɗan gangu tahi aure.

: Mai gida gona,

: Kandare Ali ka ba Garba Nagodi.

 

  Jagora: Ina gani nai Garba Nagodi.

  ‘Y/ Amshi: Ba ni bari rani ya taɓani.

 

  Jagora: Agaza mani Garba Nagodi.

  ‘Y/ Amshi: Yau hwa ruwa sun kai ga wuyana.

: Mai gida gona,

: Kandare Ali ka ba Garba Nagodi.

 

  Jagora: Ka ga uwar raggo ita ka faɗa man,

: Ka ga ɗana ɗan babane na,

: Yaki noma ya tafiya tai,

: In munka kai kaka.

  ‘Y/ Amshi: In ya zaka garinga,

: Ya bar hauda tumu na.

 

  Jagora: A gaida Nagodi.

  ‘Y/ Amshi: Mazan jiran noma na Yahaiya.

 

  Jagora: Agaza[5] mani Garba Nagodi.

  ‘Y/ Amshi: Yau har ruwa sun kai ga wuyana.

 

  Jagora: Ni ka ga nan ina tsoron duniyar ga,

: Amma fa raina dai nika tsoro,

: Ashe mutum ba komi naba,

: Ranar mutuwa so ya lalace.

: Ka so mutum rannan ka rasa shi,

: Kai kira bai amsa kira ba.

  ‘Y/ Amshi: Bai amsa kira ba,

: Sai mutuwa dai ad da hakan ga.

: Maigidan gona,

: Kandare Ali ka ba Garba Nagodi.

 

  Jagora: A gaida Nagodi.

  ‘Y/ Amshi: Mazan jiran noma na Yahaiya.

 

  Jagora: Na yan masaƙa Garba Najanu.

  ‘Y/ Amshi: Mai cin hakin gona da haƙora.

: Mai gida gona,

: Kandare Ali ka ba Garba Nagodi.

 

  Jagora: Na zo ni ƙetare ‘yammata.

  ‘Y/ Amshi: Sun cire lalo dus sun yamutse sure,

: Wanga rani babu iri nai.

 

  Jagora: Wanga ɗankaren rani.

  ‘Y/ Amshi: In dai ana hakanga ni sai na tahiya ta.

 

  Jagora: Hayaƙi hid[6] da na kogo.

  ‘Y/ Amshi: Duk yunwa ta watce mukoda.

 

  Jagora: Yunwa mai watse mutane,

: Jifa mai watse mutane.

  ‘Y/ Amshi: To a ci runƙwui babu na zaɓe.

: Maigida gona,

: Kandare Ali ka ba Garba Nagodi.

 

  Jagora: Zo gaba kama.

  ‘Y/ Amshi: Mazan jiran noma na Yahaiya.



[1]  Sunan wata bishiya ne wanda ake magani da shi ana sha a sami ƙarfin jiki don noma.

[2]  Wata hula ce mai faɗi wadda ake saƙawa da kaba domin kare rana.

[3]  Ƙafafu “legs”

[4]  Ɗan matar mutum, wanda ba tare da shi ta haife shi ba.

[5]  Taimaka.

[6]  Fitar da abu daga wurin da yake.

Post a Comment

0 Comments