Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Waƙoƙin Noma Na Alhaji
Mamman Shata
Alhaji Mamman Shata makaɗi ne na Jama’a,
kuma yana amfani da kalangu ne a wajen kiɗinsa tare da makaɗa da‘yan amshinsa.
Yana amfani da wannan nau’in kayan kiɗin ne ko a lokacin da yake yin kiɗin noma, kodayake a
tarihance ya taɓa amfani da ganga
(ta tallabe) tun farko-farkon waƙoƙinsa
musamman na Asawwara, amma bai dogara ga yin amfani da su kaɗai ba wajen kiɗin noman, wasu waƙoƙin
noman sai dai ya sa kalangunsa.
Taƙaitaccen Tarihin Shata
An haifi Shata a shekarar 1923 a lokacin sallah babba, sunan mahaifiyar Shata Lariya kuma ‘yar Fulata Borno ce. Wajajen shekarar dubu ɗaya da ɗari takwas da goma 1810, a lokacin da aka yi jihadin Shehu Ɗanfodiyo iyayenta suka taso suka zauna a Tofar Ɗan’adala ta cikin jihar Kano inda ta zauna tana aiki a gidan sarkin garin. Daga baya sai ta ƙulle kayanta ta koma Ingawa ta ƙasar Katsina wajen Dije matar Sarkin Ingawar, ta auri wani mahauci ta haifi ‘ya’ya biyu maza. Da aurensu ya mutu sai ta koma Musawa wajen matar sarkin, sai soyayya ta haɗa su da Ibrahim yaro Raruma, wato mahaifin Shata. Ibrahim Raruma ɗan asalin garin Sanyinna ne ta jihar Sakkwato wanda shi ma Bafulatanin Sakkwato ne, neman makiyaya ta kawo iyayensa aka haife shi a nan. Shata shi ne ɗan fari ga mahaifinsa amma dai su uku suke ga mahaifiyarsa, na farko shi ne Ali na biyu kuwa muhammadu Lawal wato Shata, ke nan sai autarsu Yelwa (Amina).
Maroƙin Shata kan danganta shi da wani sahabin Manzon Allah mai suna Sasana a cikin kirarinsa. Ana ganin ita waƙa ta samo asali ne daga shi wannan mutum Sasana wanda shi wani mawaƙi ne a zamanin Jahiliyya a Madina wanda ya Musulunta daga baya. To da ya karɓi Musulunci sai ya zama mawaƙin Annabi Muhammadu (SAW). To wai zuriyar wannan sahabi ne suka watsu cikin duniya suna waƙa har Allah ya Kar kato da su a ƙasar Hausa inda aka sami alhaji Mamman Shata.
Shata ya fara waƙar Asauwara tun a wajajen shekarar 1920-1940 kuma ya yi
fice sosai. Ya zama cikakken mawaƙi kuma sananne
kuma karɓaɓɓe a ƙasar Hausa har ma ya sami nasarar yin waƙoƙi da yawa da har shi bai san yawan su
ba. Yana da ‘ya’ya da jikoki maza da mata. Allah ya karɓi ran Shata a
ranar Juma’a 18 ga watan Yuni 1999 da misalin ƙarfe 12:30 na dare, Allah ya jiƙansa da rahamarsa, amin.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.