Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Waƙoƙin Noma Da Wasu Mawaƙan Suka Yi Wa Manoma
A wannan babi za a kawo wasu waƙoƙin
noma ne waɗanda wasu mawaƙan
da ba ainahin mawaƙan noma ba ne suka yi su. Abin nufi a nan shi ne su waɗannan nau’in mawaƙa
suna yin wasu waƙoƙin da ba na noma ba, ko ma a ce sun fi yin wasu waƙoƙin
daban ba na noma ba, Misali kamar mawaƙan jama’a waɗanda kowa suna yi
wa waƙoƙinsu da sauran irinsu, kamar yadda masanan adabin Hausa
suka karkasa su. Dubi yadda makaɗa irinsu Alhaji Mamman Shata da Alhaji Musa
Ɗanƙwairo
da Ɗan’anace da sauransu, suka yi suna a wasu nau’o’in waƙoƙin
ba na noma ba, amma duk da haka sun yi wasu waƙoƙin
na noma kamar yadda za a iya gani a wannan babin.
0 Comments
Post your comment or ask a question.