Ticker

6/recent/ticker-posts

Garkuwan Bauchi Amadun kari

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Garkuwan Bauchi Amadun kari

 G/Waƙa: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

. ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 Jagora: Wannan kiɗa, duk kiɗan manoma ne,

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Na Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

Jagora: Wannan kiɗan duk kiɗan manoma ne,

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Na Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Ku gyara gona, ku share gonarku,

: In damina ta iso ruwa ya zo

: Ku shuka komai, amma a gonakku,

: Ya zamanto komai duk mai amfani.

: Mai shuka komai ba zai rasa komai ba.

  ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Idan mutun ya ga bai da gona yau,

: Ya shiga a zucci ya shuka alheri,

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Mai shuka wannan ba zai rasa komai ba,

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Mu tama ‘yan Bauchi godiyar Allah,

: Nan aka yo baba Amadun kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.x2

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.x2

 

Jagora: Ma’aikata, kun a yi ma horon[1] nan,

: Idan mutun ya shige cikin ofis,

: Idan ya taso a nan cikin ofis

: In la’asar ta yi ta riga ta yi,

: Ya ɗauki mota ya doshi gonassa.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

Jagora: Ya ɗauki mota ya doshi gonassa,

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Ya ɗauki doka ta Amadun kari.x2

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.x2

 

Jagora: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

  ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Ka ga gida,

: Sai ka ce gidan Rasdan[2]

: Sai suka ce,

: Man gidan na gona ne.

  ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Wace gona ta Amadun Kari,

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Amadu ne,

: Yay yi garkuwan Bauchi,

: Kana ya zo,

: Yay yi garkuwan aiki.x2

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.x2

 

Jagora: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Wo garkuwan Bauchi Amadun kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Wannan kiɗa, duk kiɗan manoma ne.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Don masu koyi da Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Na ɗauki doka, ta Amadun kari,

: Kula da gona yana da alfanu.

  ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Kula da gona yana da alfanu.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Wo Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Mu tama ‘yan Bauchi godiyar Allah.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Nan aka yo[3] baba Amadun kari.

‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Wannan kiɗan duk kiɗan manoma ne.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Amadu ne yay yi garkuwan Bauchi,

: Kana ya zo yay yi garkuwan aiki.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Amadu in yac ci garkuwan Bauchi,

: Sannan ya zo yay yi garkuwar aiki[4].

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Ce wa manoma ku gyara gonakku.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Ka duba Shata na Yelwa mai waƙa,

: In na yi yawo, na gama waƙata,

: Na zo gida na ga damina ta yi,

: In tahi gona in gyara gonata,

: Ina ta koyi da Amadun Kari.

  ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: In tafi gona, da ni da yarana,

: Muna ta koyi da Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Muna ta koyi da Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.x2

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.x2

Jagora: Mu tama[5] ‘yan Bauchi godiyar Allah.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Nan aka wo baba Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Wo Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.

 

Jagora: Wanga kiɗan duk kiɗan manoma ne.

 ‘Y/ Amshi: Garkuwan Bauchi Amadun Kari.



[1]  Bayar da shawara irin ta gyara kayanka.

[2]  Sugaban lardi.

[3]  Halitta, Allah ya halicci abin halitta.

[4]  Aikin gona, wato noma.

[5]  Taya/tanyo.

Post a Comment

0 Comments