Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Wallahi – Wallahi: Ta Usmanu Ɗanfodiyo
1. Mun
samu babban tafarki da’iyallahi,
Mun samu hukuncin shari’a minallahi,
Mun samu jihadi da kau nasarin minallahi,
Ya ku Musulmi ku ce Alhamdulillahi,
An bamu babban rabo Wallahi Wallahi.
2. Waɗansu na nan cikin duniya suna ta ƙwafa,
Zama sukai fada don samu su kai ga kwaɗai,
Sun ya da addin suna retse suna ta kwaɗai,
Kowa fa yaz zam musulmi yab biye ma kwaɗai,
Na duniya kaito ya ƙanƙanta Wallahi.
3. Kowa
ka bad a sarauta don a bashi dubu,
Domin shi matso talakkawa su ba shi dubu,
Ana jira nai shi zo can inda babu duhu,
Na ba ku shadad dubu da abinda yaf fi dubu,
Ba Ban karɓi yankin kurum Wallahi
Wallahi.
4. Tsaron
tallaka marayu niy alhaƙumi,
Cin dukiyassu jini irinsu alƙuƙumi,
Amri da nahayi na Allah niy yi alƙuƙumi,
Ban karɓi komi ga yanki ban da alƙuƙumi,
Huƙumin shari’ah kaɗai Wallahi Wallahi.
5. Mai
sai da gonat tallaka shi ƙwace
wansu ƙasa,
Tara da gumki da fiski ɗai
sukai ga ƙasa,
Ƙwace
da zulmi sukai domin su amshi ƙasa,
Kowa fa yak karɓi yanki don shi noma ƙasa,
Ta duniya ya ci massai assha Wallahi.
6. Su
sa su noma, su yo kuɗɗin ƙasa ga hali,
Ginak Katanga sukai, yin ɗakuna
ga hali,
Rago na safka, da layya sukai ga wanga hali,
Kowa fa yak karɓi yanki ai ga wanga hali,
Yuƙa ta Iblisu ta yanko shi Wallahi.
7. Ni
ban ƙayya haƙƙu
in yi gari,
Ni ban da busa da ganguma in yi gari,
Ni ban da bayi liffidda haƙƙu
in yi gari,
Don tadda kowa ba ni amma fa masu gari,
Su sunka tasshe ku don shalinsu Wallahi.
8. Kui
hattara da batun yankinsu don ku sani,
Kui hattara fa ga gonakkinsu don sani,
Kui hattara da batun kuyyansa don ku sani,
Akwai guba fa ga gonakkinsu don ku sani,
Kowa fa yab bar su ya bi ta tamu Wallahi.
9. Shaida
da anka yi nan fa don ku sani,
Shaida da anka yin saran nan fa don ku sani,
Kasa da anka ci kafirrai kaɗai
ku sani,
Kowa fa yab bar su ya bi ta tamu Wallahi.
10. Runfa da shingi shikai shi fake a canye mai,
Wani ko shi noma a sa shanu su canye mai,
Wani baku iko shi roƙi
zumai su nomo mai,
Kowa ka ɓata mutane cimakassu da mai,
Kururuwa fada sun ƙi
ta tamu Wallahi.
11. Ƙwaj
ja adawa da sarki walla ba ni ciki,
Ƙwaj
ja sarauta da sarki walla ba ni ciki,
Ni ban zuwa fada ba ko zan shiga ba ciki,
Alhamdu Lillahi kowa ya ji ba ni ciki,
Ga batun sarauta duka Wallahi Wallahi.
12. Mai son Ta’ala shi ilmi shi san shi ƙwarai,
Mai son Ta’ala shi yo sallah shi san ta ƙwarai,
Kwas so Fiyayye shina so nai mu so shi ƙwarai,
Sunna ta Annabi hanya ta ka san ta ƙwarai,
Kowa fa yab bi ta ya unfana wallahi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.