Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Bismillahi Farkon Zance: Ta Malam Zainu Zubairu Bunguɗu
1. Bismillahi farkon zance,
Na da nake nufin shiryawa.
2. Mun gode wa sarkin baiwa,
Allah wanda ba shi gushewa.
3. Muna shukura muna ƙarawa,
Baiwa rabbu na sabkowa.
4. Tsira sallama da aminci,
Gun mahmudu mai shiryawa.
5. Bayan godiya da salati,
Ga shakwa da zan bayarwa.
6. Nai kuka ina ta hawaye,
Laifuka na nake ta tunowa.
7. Ga kaya muna Tarawa,
Ga karfi shina ƙarewa.
8. Ga kaya kwarai sun nauyaya,
Ba gammo da zamu azawa.
9. Ga mu cikin
duhu ba haske,
Babu abin da zan
ya dawa.
10. Ga mu cikin
ruwa ga kaya,
Ga gulbi shina
kawo wa.
11. Kowa ga mu kai
yai zafi,
Kana ba wurin
hutawa.
12. Gulbi ya cike
yai baye,
Amma ba ruwan kurɓawa.
13. Kowa sai shina
masha’a,
Babu hani bare
horawa.
14. Don ga zamani
ya canza,
Ga ƙarfinmu bai ƙarawa.
15. Ɓanna ta yawaita ga fili,
Sai ‘yan ƙalla ke ɓoyewa.
16. Kunya ta ƙaranta ga kowa,
Manya yara ba
runtsewa.
17. Kowa duniya ya
zaɓa,
Sai ‘yan kalla ke
waigawa.
18. Ga gyaransa ga
ɓarnassu,
Kuwa ne basu san
dainawa.
19. Ga bami da
burkutu fili,
Sai in ba kason
kurɓawa.
20. Ga duma ga
giya barasa,
Ga kabso suna
watsawa.
21. Sauran
shaye-shaye gaba ɗai,
Ko fili ana
saidawa.
22. Ba tsoro bare
jin kunya,
Sai ‘yan ƙalla ke ɓoyewa.
23. Caca da shan
giya ba dama,
Sai daɗuwa suke ƙarawa.
24. Sata ci da
ceto rashuwa,
Ga bori suna ƙagawa.
25. Ga zina ta yawaita
a fili,
Talla suke suna
saidawa.
26. Karuwa da su
da karame,
Har kullum suna
tarawa.
27. Manya yara ba
mai kunya,
Ɓanna ɗai suke
kwaɓawa.
28. Ba mai
tattalin ayi gyara,
Sai mai tattalin ɓatawa.
29. Sun mance da ɗakin turɗa,
Mai tsanani wajen
kwantawa.
30. Kabri ga duhu
ga kewa,
Sai halinka zaka
ishewa.
31. In khairinka
ya rijaya,
Shi ne ɗan’ uwan kwantawa.
32. In mugun hali
ka aika,
Ka ɓata ba wurin hutawa.
33. Ga duka Nakiri
da Munkar,
Bayan tambayar ruɗarwa.
34. Ga shi wuta
tana ɓullo mashi,
Ga shi a kwance ba
motsawa.
35. Dangogin azaba
tari,
Sun riske shi bai
tserewa.
36. Ga shi cikin
duhu ga kewa,
Shina ƙarar da ba karɓawa.
37. Hali nai dashi
zai zauna,
Dan nan ma har
zuwa tayarwa.
38. Allah ya tada
shi ba fashi,
In mun tuba zai
yafewa.
39. Komi ke yawan
zunubanka,
In yaso shina
yafewa.
40. Sai bawa baƙi mummuna,
Mai shirka ba a
yafewa.
41. Sai ya tuba ya
bar tsafi,
Ya bi rasulu mai
shiryawa.
42. Sannan za shi
sadu da jinƙai,
Domin daha mai
shiryawa.
43. Ya bar
godabensa da haske,
Haske wanda baya
dushewa.
44. Har abada da
bashi katsewa,
Zance ne da bai
canzawa.
45. Islamu ne
addini,
Har abada da bai
yankewa.
46. Sa shirya
garemu cikakka,
Har ko yaushe ba
saɓawa.
47. Ya Allah kai
ka ishemu,
Samammu kaza da
rasawa.
48. Mai roƙo ka roƙi ta’ala,
Shi ke baka shi ka
hanawa.
49. In ya baka to
ka samu,
Ba wani wanda za
shi hanawa.
50. In ya hana ka
wa zai baka,
Ba wani wanda za
shi iyawa.
51. Rayayye
wadatacce ne,
Komi na shi bai ƙarewa.
52. Kai ɗai ke garan tun fari,
Ban ƙara ba, ban ƙarawa.
53. Komi nawa kai
kab bani,
Ba wani wanda zai
amshewa.
54. Ya Allah ban
imani,
Sabitu wanda bai
katsewa.
55. Ban ikon da na
bauta ma,
Bauta wadda ba
tsaidawa.
56. Ƙanana da manya,
Har ko yaushe ba ƙetawa.
57. Komi ka hana
in barshi,
Ban kamnarshi ban
dubawa.
58. Komi nawa kai
kayyoshi,
Sai ka yarda zan
sheɗawa.
59. Don haka kai
roƙon kowa,
Sai kai mai abin
bayarwa.
60. Ya razzaku
arzittani,
Ko yaushe ina
walawa.
61. Allah bani
ilmi rasikhu,
Har ko yaushe ban
mantawa.
62. Na roƙa ka ban ilhami,
Koyaushe ina
ganewa.
63. Na yi
tawassuli da Muhammad,
Khairul kalki mai
shiryawa.
64. Ya Allah ka bani bayani,
Komi na shi zan
kyawawa.
65. Don kakan Hassan da Hussaini,
Mai baiwa shina ƙarawa.
66. In ka zo garai ya baka,
Ko baka zo ba zai
aikawa.
67. Ya mai tsamo masu nutsewa,
Zaɓaɓɓe abin zaɓowa.
68. Ga mu cikin ruwa mun noce,
Ba motsi bare
tasowa.
69. Ya jirgin fito fishshe mu,
Tun sheɗanmu da dawowa.
70. Cetanmu macecin bayi,
Tun kukanmu na juyawa.
71. Don Allah ya zaɓeka,
Shi ya raya ka ba
togewa.
72. Gun darajjakka ba jayayya.
Gun tsimma bare
tserewa.
73. Tun farko fa ba tamkarka,
Har ƙarshe ba’a samowa.
74. Kai ne mai daraja tamma,
Zaɓaɓɓe wanda zashi musama.
75. Kai ne Swadiƙul
masduƙu,
Kwar roƙa ka bashi rasawa.
76. Mai baiwa da bashi kwarri,
Ko ya baka zashi
daɗawa.
77. Baya son ka
don samunka,
Ba ya ƙin ka don jemewa.
78. Komi zo garai ya bayar,
Mai baiwa shina ƙarawa.
79. Bai gajiya da bai wa manzo,
Komi na shi bai ɓoyewa.
80. Shi zai baka har shi isheka,
Ahmadu Ɗaha bai ƙosawa.
81. Mai so nai kaza mai ƙin shi,
In zai baka bai ƙoshewa.
82. In ya baka sai ya ba shi,
Har kullum ba zai
fasawa.
83. Shi ne kamilul ihsani,
Mai natsuwa mafi
yafewa.
84. Ko ka cuci Annabi Ɗaha,
Bai gurin shirin
ramawa.
85. Ramko nai gareshi Nasiha,
Ga khaira shi na
ta daɗawa.
86. In ya baka sai ka gode,
Har abada baka
mantawa.
87. Kowas so shi
Ahmadu Ɗaha,
Ya huta ba ya ƙonewa.
88. Don haka na
garai muka raɓa,
Don ranarmu mai
tarawa.
89. Allah bamu
yarda taka,
In ga rasulu mai
tserarwa.
90. Bada wuya ba
ya Allah,
Don zati ba zamu
rasuwa.
91. Don zatinka
shiryasshemu,
Har mu ga Ɗaha ba ƙonawa.
92. Don zatinka
karɓi du’aina,
In tsira ba
Konawa.
93. Laifina da nai
yafe mani,
Domin Ɗaha mai cetowa.
94. Ga zunubai
muna Tarawa,
Ga kuka muna
rabkawa.
95. Yafe man
zunubaina duk,
Don rahamakka mai
shafewa.
96. Mata na dani
da uwaye,
Na da ɗiyanmu ba keɓewa.
97. Dangina da
almajiraina,
Da ɗiyansu ban zaɓewa.
98. Malamanmu su
da masoya,
Kakanninmu ba keɓewa.
99. Sa jama’a
musulmai su duka,
Rayayyu da masu
macewa.
100. Kai muna
arziki mu ga Annabi,
Ko ciwon mu na
warkewa.
101. Kowa yagganai
ya warke,
Saura nai gidan
hutawa.
102. Can darus
salami mu huta,
Hutawa da ba ƙosawa.
103. Baiti ne dari
na tsara,
Ga ishirin suna raɓewa.
104. Fi hadi
sashin na yi ta,
Gun hijra mafi
shiryawa.
105. Salli alaihi
ya Allahu,
Alaye da masa
biyawa.
106. Aiki nai kaza
zance nai,
Ba su rage shi
basu daɗawa.
107. Bunguɗu ce garin mai waƙa,
Zainu Zubairu ban ɓoyewa.
108. Ga aiki gare
ni daɗaɗɗe,
Ɗan ilmin mu bai warkarwa.
109. Datti gare
shi ga shi kaɗanne,
Na nutsa ko ina
tasowa.
110. Nan na dakata
nai aya,
Allah sa muna ƙarawa.
111. Amin rabbu
domin zafi,
Sa gurin mu bai
takewa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.