Ticker

6/recent/ticker-posts

Wai Kamar Sun Sadu Da Juna Amma Ba Su Sadu Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam, ƙawata ce da saurayinta suna soyayya, to sai ya kasance suna wasanni a tsakaninsu wanda suke gusar da sha’awarsu, ta hanyar kamar sun sadu da juna amma ba su sadu ba, saboda bai taɓa shigarta ba amma yakan yi kamar ya shige ta, ta hanyar tsayawa a tsakanin cinyarta har ya gamsu ita ma haka, amma bai taɓa shigar ta ba. Yanzu dai gobe ne suke so a ɗaura musu aure, to za ta yi istibra’i ne, ko yaya za ta yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Jama’a! Ya wajaba mu ji tsoron Allaah a cikin dukkan maganganunmu da ayyukanmu, mu sani cewa Allaah Maɗaukakin Sarki yana ji, yana gani, kuma yana sauraron dukkan komai, hatta duk wani abin ma da zuciyarmu take raɗa mana. Dole ne mu san cewa: Ƙoƙarin ɓoye hujjojin laifi da yin bayanai a murɗe don neman zurma Malamai har su halatta laifi ya fi asalin laifin zama babban laifi fa!

Tsakani da Allaah! Wace irin magana ce wai: ‘Suna wasanni a tsakaninsu wanda suke gusar da sha’awa?’ Menene ke motsar da sha’awar tun farko in ba wasannin ba? To, yaya kuma za a ce wai wasannin za su gusar da sha’awar?! Sai dai fa idan sun gama kaiwa ƙoƙoluwa ko maƙurar shaawar ce, watau sun gama saduwa da juna! Wannan kuwa shi ne maanar: Gamsuwa da aka faɗa daga baya!

Haka kuma wai: ‘Ta hanyar kamar sun sadu amma ba su sadu ba!’ da kuma wai: ‘bai taɓa shigar ta ba, amma yakan yi kamar ya shige ta!’ Wane irin zaurancen magana ne wannan? Magana dai ɗayar biyu ce, babu tsaka-tsakiya: Ko dai sun sadu ko kuma ba su sadu ba, haka kuma ko dai ya shige ta ko kuma bai shige ta ba. Amma ba wani abu: ‘kamar sun sadu kuma kamar ba su sadu ba!’ Ko kuma wai: ‘bai shige ta ba amma kuma kamar ya shige ta!!’

Sannan kamar yadda maganar ta nuna: Wannan abin ba sau ɗaya ba ne ya auku a tsakaninsu, abu ne da suka sha aikatawa, shi ne ma’anar cewa: ‘bai taɓa….ba’, watau duk da yawan aukuwar ‘wasannin’ a tsakaninsu amma bai taɓa shigarta ba! Abu ne sananne kuwa irin wannan abin a kullum cigaba suke yi: Koda da farko a kan cinya su ke tsayawa, a ƙarshe dai sai sun shige a cikin tsakanin cinyoyin! Idan kuwa haka ne, ta yaya za su tabbatar cewa bai shige ta ba? Alhali, kamar yadda wani ya faɗa: ‘A lokacin sun kai ƙoƙoluwar shaawarsu ta yadda ko da iyayensu ne suka leƙo, suka kira su ba za su iya ji balle amsawa ba?!!

Sannan cewa wai: ‘…ta hanyar tsayawa a tsakanin cinyarta…’ Wannan ma wani surkulle ne kawai, domin duk mai hankali ya san cewa tsayawa a tsakanin cinyoyi ba ya gamsarwa, duk kuwa da cewarsu wai: ‘har ya gamsu…!’ Domin babu yadda shi zai gamsu kawai da tsakanin cinyoyi ba tare da an samu wani abu, kamar ruwan maziyyinsa ko maziyyinta a wurin ba! Wannan kuwa shi yake nuna cewa al’aurorinsu sun haɗu da juna kenan, amma ba wai a tsakanin cinya ba! Wannan kuwa shi ne abin da maganarta: ‘har ya gamsu, ita ma haka…’ take nunawa.

Tsakani da Allaah! Ko da tsayawa a tsakanin cinyoyinta ya gamsar da shi, ta yaya ita za ta gamsu da haka ba tare da ya shige ta ba?! Amma tun da dai, kamar yadda aka ce: Har ita ta gamsu to kuwa wannan babban dalili ne a kan cewa al’aurarsa ta haɗu da al’aurarta kenan! Domin ta yaya mace za ta gamsu ba da hakan ba?! Kuma kamar yadda ya gabata, abu ne mawuyaci su iya tabbatar da cewa wai bai shige ta ba, saboda santsin da wurin ke da shi a lokacin da farko, sannan kuma da kasantuwar sun kai matsayin da ba su tunanin komai, saboda sun kai ƙoƙoluwar shaawa a lokacin! A cikin Sahih Muslim, Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) dai cewa ya yi:

إِذَا جَلَسَ بَيْنَ شُعَبِهَا الأَرْبَعِ وَمَسَّ الْخِتَانُ الْخِتَانَ فَقَدْ وَجَبَ الْغُسْلُ

Idan ya zauna a tsakanin sassanta guda huɗu, kuma kaciya ta haɗu da kaciya, to tabbas! Wanka ya wajaba.

Sannan kuma mun samu sahihan bayanai da suka tabbatar da cewa: Wasu ma’aurata ma sukan yi irin wannan domin gudun samun ciki, amma kuma daga ƙarshe sai ga cikin ya samu, alhali kuma sun tabbatar da cewa ko kusa da al’aurarta mijin bai kai ba! Wannan dalili ne a kan cewa: Ya shige ta amma ita kanta ma ba ta sani ba , balle shi!!

A ƙarƙashin waɗannan bayanan, ina ga abin da ya fi shi ne: Wannan budurwar ta yi istibra’i kawai kafin a ɗaura ma ta aure. Sai dai idan ta tabbatar, kuma tana da yaƙini cewa alaurarsa ba ta taɓa shafar al’aurarta ba a cikin dukkan ‘wasannin’ da suka ɗauki tsawon lokaci suna yi!

Sannan kuma dole ne kafin a ɗaura auren sai sun tuba ga Allaah, kuma su yawaita istigfaari saboda saɓa ma Allaah da suka yi, saboda aikata wannan mummunar alfasha:

وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَآءَ سَبِيل

Kuma kar ku kusanci zina, lallai ne shi alfasha ne kuma mummunar hanya ce.

Sannan kuma a cikin Suratun Nuur, ya ce:

الزَّانِي لَا يَنْكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لَا يَنْكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ وَحُرِّمَ ذَلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِين

Mazinaci kar ya yi aure sai da mazinaciya ko kuma mushirika, ita kuma mazinaciya kar wani ya aure ta sai dai mazinaci ko kuma mushiriki, kuma an haramta wannan ga muminai.

A ƙarshe ina fatar masu karatu, musamman mata za su gafarce ni saboda irin sakin-baki da kuma irin ɓaro-ɓaron da na yi a wurin bayar da wannan amsar. Haka abin yake zama a wani lokaci, sai a yi haƙuri don Allaah. Allaah ya gafarta mana gaba-ɗaya.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments