Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijin Da Ya Ke Fasiƙanci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mace ce ta ke da miji, yana son yin sallar dare, da azumin nafila, kuma mutane suna mutunta shi, amma matsalarshi dai: Idan ya samu ’yar walwala yana shan giya kuma yana kallon fina-finan batsa. Ta sha yi masa magana a kan haka, wani lokaci ma har kuka yake yi, amma duk da haka ya kasa dainawa, musamman in ya shiga ban-ɗaki. Matar har addu’a take yi kar Allaah ya ba shi arziƙi don ba ta san abin da zai yi ba a gaba. Wace shawara malam zai bai wa wannan matar da kuma mazaje masu ƙuntata wa matansu a kan irin wannan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Idan dai haka maganar ta ke, cewa: Mijin yana sallar dare kuma yana azumin nafila, amma kuma yana shan giya da kallon fina-finan batsa idan ya samu hali, to a nan abin da zan ce shi ne: A cigaba da yi masa addu’a da roƙon Allaah Taaala ya shirye shi, ya sa ya fi ƙarfin zuciyarsa da shaiɗaninsa.

Matar ta cigaba da yi masa bayani cikin hikima da kyakkyawar wa’azi, kar ta gaji. Ta jawo hankalinsa ga ya daina barin irin waɗanan fina-finan a cikin wayarsa, kuma ya daina abota da mashaya giyar, ya daina bi ta layi ko wurin da ake sayar da giyar, kuma ya daina ajiye duk wani abin da zai tuna masa al’amarinta, kamar kwalabenta da hotunata da fina-finan da ke nuna yadda ake shan giyar da sauransu. Yanzu zai ji daɗi ’ya’yansa su tashi su gan shi yana aikata irin wannan aikin, kuma zai so a ce sun yi koyi da shi a kan haka? Sannan kuma yaya zai ji idan aka fara yi musu gori cewa: Ubansu mashayi ne, ko mazinaci ko dai wani abu irin wannan?

Ta yi haƙuri ta cigaba da zama da shi tana yi masa waazi. Na lura: Akwai alamar alkhairi a tare da shi, tun har kuka yakan yi in tana yi masa faɗa.

Addu’ar: Kar Allaah ya ba shi arziƙi ba, ba daidai ba ne. Maimakon haka ta yi addu’ar: Allaah ya ba shi arziƙi mai amfani a duniya da lahira. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana yawaita yin wannan adduar:

رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً ، وَفِي ألْآخِرَةِ حَسَنَةً ، وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ

Ya Ubangijinmu! Ka ba mu kyakkyawa a duniya, kuma kyakkyawa a lahira, kuma ka tsare mu daga azabar wuta.

Allaah ya taimake mu.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments